Da sauri ya sauka daga gadon ya nufi frigde ɗinshi na ɗaki ya buɗe cike da son shan ruwa sede babu, haka ya juya ya nufi parlor da sauri..

Daidai lokacin ta fito don daukowa junior ruwan da ta manta bata dauko ba, karo suka ci da hanzari ta koma baya tana ambaton Allah, hannunta dake rawa ta laluba ta kunna switch..

Hard broad chest ɗinshi da ba riga ta ci karo da kan ta kai idanunta kan fuskarsa, wani irin zufa yake Haɗawa kaman ma a firgice yake, zata yi magana ta ga ya sulale ya zauna tare da haɗe kanshi da gwiwa kaman me tsoron mutane kaman kuma me tsoron ta ganshi a halin da yake ciki, da sauri itama ta durkusa tace

"Sir! Me kake bukata? Jikin ne?"

Cikin rawar murya yace
"waaa...ter"

Da gudu taje fridge ta ɗauko ruwan ta dawo ta buɗe murfin ta mika mishi ya karɓa ya kurbi kaɗan ya watsa sauran a fuskanshi zuwa kanshi yana karkada gashin shi wadda feshin ruwan har fuskanta lumshe idanunta tayi, Seda ruwan ya kare tsab kan ya jefar da goran ya sake maida kanshi cikin kafafunshi yana sauke numfashi..

"Mugun mafarki kayi?"

Kaman yaro ya tsinci kanshi da gyaɗa mata kai..

Tace cikin sassanyar muryarta
"ka ja numfashi a hankali sir, mafarki ne ba zahiri ba. Ana so idan mutum yayi mummunan mafarki a duk sadda ya farka ze ce 'Auzu bi kalimatillahi tammat min qablihi wa iqabihi wa sharri ibadihi wa min hamazaatis shayadini wa an yahduruun' Adu'ar na nan cikin hisnul Muslim"

Gajiyayyun idanunshi ya ɗago ya zuba mata yana so ya ce ta sake don be sani ba se yanzu kuma ba ze iya maimaitawa ba, kanta ta mayar kasa ta sake farawa yana bi har suka kai karshe..

Seda ya ɗan natsu kan ya miƙe cikin kasalalliyar murya yace
"thank you"

Jurewa kallon idanunshi dake gigitata tayi cikin natsuwar murya tace
"u welcome, kayi Adu'a karka sake yin irin mafarkin kuma"

Har ya juya ya sake juyowa yace
"ban iya ba"

Runtse idanunta tayi sbd hawayen dake son zubo mata, shi kuwa wani irin rayuwa ne wannan da yayi!

Tace
"baka yin ko wani irin Adu'a?"

Kallonta kawai yake, se taji kaman maganan yayi mishi rashin daaɗi zata ce yayi hakuri se taji ya ce
"me zan roka?"

A tsorace ta kalleshi tace
"Subhanallah! Sir ai Adu'a dole ce ga dukkanin musulmi ko ka samu duniya ba shine ze sa ka kasa neman lahirarka ba, mahaifiyarka dake kwance cikin kabari itama tana bukatar Adu'ar ka don Adu'an ƴaƴa na daga cikin manyan sadakatul jariya  zaka nemi tsari da azabar kabari da na wuta, kuma ka nemi gamawa da duniya lafiya.."

Bakinta dake ta motsi kawai yake kallo idanunshi sun sake rinewa don ambatar sunan mahaifiyar shi kaɗai ya Tono mishi wani miki da ya jima da binnewa, me ke faruwa ne? Meyasa bayan ya manta komai nightmere ɗin Mahaifinshi ke dawo mishi kaman yanzu?

Muryarshi na ɗan rawa yace
"ban san hakan ba..!"

Hawayen tausayin shi ne ya zubo mata ta sa hannu ta share tare da Kallonshi tace
"ai ka iya ayatul kursiyu, qulhuwa, Falaq da nasi?"

Kai ya gyaɗa mata tace
"ka karantasu kafa uku uku se ka shafa in Shaa Allah bazaka sake mafarkin ba"

Kaman ze yi magana se kuma ya fasa ya juya ya wuce, da kallo ta bishi har ya shige room ɗinshi se ta samu kujera ta zauna hawaye na sake silalo mata, Matukar tausayin rayuwarshi na lulluɓe ta.

Ta jima a wurin kan ta ɗauki ruwan ta koma ɗaki zuciyarta fal sake sake..

Washegari Seda likita ya sake dawowa ya sa mishi drip sbd jikin dae ba daaɗi, ba jikin kaɗai ba har zuciyarshi likitan ya tsorata ganin ciwon da suka samu suka raba shi dashi karfi da yaji ne ke shirin sake dawowa, idan kuwa hakan ta kasance har career ɗinshi se yayi affecting..

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now