"she hit me"
Tana maganan tana nuna hidayat.

A razane hidayat take kallon yar yarinyar kaman yadda shima yake kallonta cikin ɓacin ran da be san ya bijiro mishi ba, cikin wata kalar murya yace
"how dare you hit my dota?"

A ruɗe tace
"Wallahi wallahi ban taɓa ta ba, taya zan fara dukanta? She came here tace tana son custard na ce mata ina zuwa bara nayi sallar asr da lokacin ke shirin fita se in je in Haɗa mata se kawai gani nayi ta saki ihu tana rike kumatunta but ban taɓa ta..."

"Enough please..!" Ya faɗa har lokacin da ɓacin rai sossai a fuskanshi.

Hannun Farrah ya sauke daga fuskanta wurin kuwa yayi ja, Junior dake bacci ya ajiye bisa kan gadonta ya ɗauki Farrah zasu fita Hidayat ta sake kokarin kare kanta sbd bata taɓa jin zafin a jingina ta da abunda bata yi ba irin yau, sossai abun ya mata zafi wadda ta rasa dalili haka kawai take jin kaman zata yi hauka idan har ya fita da wannan fushin da kuma Tunanin ta taɓa mishi yarinya..

"Sir..! Please believe me wlh ban taɓa ta ba.."

A tsawace yace
"then why her chin shows that? Kalli kumatunta.. I can take anything but not hitting my child ni karan kaina ban taɓa saka musu hannu ba so ba zan yarda common nanny like you ta dakesu ba, If you can't do the job then you should please silently leave tun baki Harzukani ba"

Yana kai nan ya juya ya fice, kuka hidayat ta fashe dashi tana jin ba daaɗi har kasan ranta, idan kuwa bata faranta mishi sbd taimakon da ya mata ba ba zata ɓata ranshi ba, Norah da Aisha ne suka zo wurinta suna share mata hawaye.

Norah tace
"I belive you miss hidayat you can't hit Farrah she's probably lying bcs she doesn't like you"

Zama tayi kawai tana rufe fuskanta da tafukan hannunta tana cigaba da kuka, this is a minor thing a rayuwarta sede ya fi kona mata zuciya fiye da abubuwan Yusuf menene hakan?

Aisha ficewa tayi ta je ta same shi yana ta rarrashin Farrah, a hankali tace
"Daddy mama will never hit Farrah bcs ko mu bata taɓa dukanmu ba, she always says hitting someone is never a solution and will not ever be, gashi yanzu tana ta kuka har Ya Norah ma started to"

Se yaji wani iri, dukda be san Hidayat ba sede Aisha bazata mishi karya ba, idan har bata taɓa dukansu su yaranta ba taya zata fara dukan Farrah, ya san irin yadda ta tashi sbd ya fuskanci abu makamacin hakan shiyasa shima be taɓa dukan yaranshi ba, idan har ze daga hannu da nufin dukan wani se Tunanin mugun mahaifin shi ya darsu a ranshi hakan yasa kwata kwata baya so yaji ko maganan duka ne..

Farrah ya kalla yace
"Baby u knew na faɗa muku lying is a very bad habit right?"

Kai ta gyaɗa, yace
"then tell Me the truth did miss hidayat Hurt you?"

Shiru tayi yace
"I won't be mad ok? Tell me.."

Se tace
"bata dukeni ba, I just don't like her shine friends ɗina gave me idea yadda suka gani a wani film da yarinyar bata son stepmom ɗinta da tayi hakan her dad divorce the stepmom shine nima nayi"

He's so shock da abun, taya yarinya kaman Farrah zata yi acting so fine kaman da gaske hidayat ɗin ta Mareta? Se yaji be ji daaɗi ba sede sbd yarinyar tayi kuka kuma baya so ya sake sakata wani kukan se kawai yace mata
"don't repeat that again is a bad habit kin ji?"

Kai ta gyaɗa ya juya ya kalli Aisha yace
"tell miss hidayat am sorry"

Daga haka ya miƙe ya shige toilet ɗinshi..

Fita Aisha tayi ta koma wurin hidayat da ta samu tana sallah, Norah na zaune daga gefen gadonta, alwala Aisha ma taje tayi ta dawo suka yi sallar tare, bayan sun sallame Aisha tace

KOWA YA GA ZABUWA...Onde histórias criam vida. Descubra agora