"Daga gida nake!"
Ta faɗa kanta kasa..

"Eh na san daga gida kike tunda gidan Yusuf ɗin ba daji bane, shine kika kamo hanya kika zo mana da magariban nan?"
Cewar umma.

"Ya sakeni"

Wani irin dariya umma da Surayya suka yi kan Surayya tace
"to mu ina ruwan mu don ya sakeki, shine zaki zo mana nan? Kinga ki je chan ki san yadda zaki yi"

Umma tace
"nan gidanku ne? Ko kina da gado a gidan nan ne? Me gidan nan kin kashe shi kuma a iya sanina bakya daga cikin ƴaƴansa"

Kanta kasa tace
"Don Allah kuyi hakuri bani da kowa a duniyan nan se ku, in kuka gujeni ban san inda zan yi ba"

Umma na mikewa tsaye tace
"au kin san da hakan kika kaso aurenki kika zo mana? Bama ki da kunya wallahi..."

Surayya tace
"kinga babu abunda ya hadamu dake, babu abunda ya Haɗa ƴar tsintuwa da ƴaƴan halak ki je chan ki san nayi"

Hawaye masu zafi ne suka zubo mata, laifin iyayenta ne ba nata ba, kowa ana haifanshi cikin gata da kauna amma sun tauye mata wannan farin cikin, a hankali tace
"don Allah karku min haka, ku taimakeni bani da wani gida a duniyan nan se nan"

Umma tace
"ke kinga tsinto ki aka yi, kuma wadda ya tsinto kin nan ya mutu don haka baki da wani alaka da gidan nan don gida namu ne in har mu ke da iko dashi kuwa baki da matsuguni ko na kwayar zarra a cikin gidan nan"

Hawayenta gudu suka kara, a Tunaninta umma zasu karɓeta ko da bauta zata ke musu bazata rasa na baiwa Aisha ba, cikin zub da hawaye tace
"don Allah umma kiyi hakuri, ni amana ce a hannun ku bani da wani gata a duniyan nan se naku, ku kaɗai ne gata na"

Surayya tace
"mu ba gatan ki bane! Mu Ba gatan ki bane kije chan ki nemi gatan ki, ah to"

Umma tace
"se yanzu kika san mu gatan ki ne? Shafaffiya da mai, ina har korata kika sa aka yi a cikin gidan nan? Ko kin manta ne In tuna miki, ina ce wata biyu baya kika sa aka yi mana tsakani dake bayan kin sa an fitar mana da jini? Tun da wuri ki san Inda dare ya miki da inda gari zata waye miki"

Dole ta sake jarrabawa saboda yaranta tana tsoron su faɗa mummunan hali idan har ta bar gidan Abba, da ita kaɗai ce zata iya ficewa sede Su Junior..

Cikin rawar murya tace
"Umma kuyi hakuri bani da Inda zan je, ku rufamin asiri ko saboda Aisha da Junior ku barni in zauna Anan in muka tafi a wannan lokacin komai ze iya faruwa damu"

"babu ruwan mu da abunda ze sameku, duk abunda ze sameku sede ya sameku kinga tashi ki fitar min daga gida.."
Umma tayi maganan tana nuna kofa..

Mikewa hidayat tayi daga ita har Aisha hawaye kawai suke yi, zuciyarta yayi nauyi matuka, a hankali wani irin tsanar ahalin da ta taso a ciki na mamayeta, ficewa suka yi daga gidan suka kama tafiya ba tare da sun san inda zasu ba.

Har magrib yayi suna yawo, gida ta gani ta shiga da sallama sede sallamar duniyan nan sun ƙi amsa mata Dukda suna zazzaune ne suna kallonta tana Kallonsu, bata ga laifin su ba sanin yadda duniya ta zama se ta fice, a haka ta jera Gidaje kusan biyar don ta samu tayi sallah sede sun ƙi amsa mata sallama ma bare ta roke su.

Masallaci ta samu lokacin ana kiran isha anan sukayi magrib da isha, suna nan zaune cikin wani irin hali junior na bayanta Aisha na cikin jikinta har wurin karfe goma me gadin masallacin ya zo yace
"baiwar Allah ku kara gaba lokacin rufe masallacin yayi"

Rokon shi ta fara akan ya bari su kwana na yau kaɗai Sam ya ƙi haka suka mike suka fito.

Tafiya suke tayi ba tare da sanin inda zasu ba, ko kula da inda suke zuwan bata yi tunani ya ci karfinta, damuwa yayi mata yawa, garin yayi shiru banda hasken farin wata babu abunda yake sararin na duniya kowa na cikin gidanshi a killace banda ita da yaranta.

"Kai baba..! Wanchan yarinyar tayi Sak yadda honor ya tsara mana wacce yake bukata"

Maganan da ya shiga kunnenta kenan ya sakata tsayuwa Chakk ta kalli hagu da damanta ko ɗan tsuntsu babu.. Wadda aka kira da baban ne yace

"wai wannan gansamemiya taya tayi kama da kiyasin shi? Ka manta yarinya yace wacce bata kai goma ba?"

Na farkon yace
"kai dallah chan kalli hannun matar"

"kai kai kai wallahi da gaskiyarka wannan ma ai har ta wuce yadda ya kiyasta mana, kaga mu je mu kwaceta mu kaita kila a yau ma zasu yi abunda zasu yi da ita don zaɓe ya riga ya gama karatowa"

Basu gama maganan ba Hidayat ta damke hannun Aisha tace
"Aisha zamu fara gudu, kiyi gudu da iyakar karfin ki in ba haka ba zamu rasa juna..."

A take suka runtuma da gudu mutanen suka biyo bayansu suma da mugun gudu.....

#like
#share
#comment

                     🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now