Da dare a haukace Yusuf ya shigo gidan yana me hargowan ina ta kai su umma? Ummi ce ta amsa mishi da
"inda ya dace a kaisu mana tun farko"

Ze yi kanta ta shata mai layi tare da zaro numbern DPO tace
"Wallahi kana taɓa ni tare zaka kwana da ƴan uwanka a cell, karka ji da wai ba iya nan abun ze tsaya ba wallahi se mun je kotu, kotun ma na addinin musulunci se ka gayamin wani addini ne ya baka lasisin zina, wani kuma addinin ne ya baka lasisin musgunawa matar aurenka da yaran ka"

Baya ya koma yana kallonta, tabbas daga kallon idanunta zata aikata kwafa yayi yace
"Zaku gani!"

Ummi tayi Charab tace
"Alkhairi ba! Se Alkhairi in shaa Allah"

Juyawa yayi ya fice, hidiyat dae haka ta kwana cikin zullumi da sanyin jiki ummi kam ko a jikinta se hira suke tayi da su Aisha tana basu labarai kala kala suna dariya.

Washegari bayan la'asar suka yiwa police station tsinke, a nan suka tarar da Yusuf da ba yadda be yi ba a bada belinsu sede DPO ko bari ya ganshi be yi ba se da time ɗin da ya dibar musu yayi yasa aka fiddo su zuwa office nashi hidayat dae banda faɗuwa babu abunda gabanta yake musamman da ta ga yadda su umma suka firgice sukayi zuru zuru da alamu sun ci duka duk a kwana ɗaya.

Gyaran murya yayi kan yace
"kun riga kun amsa laifin ku so Bama bukatar wani sake maida magana, yanzu doka zan kafa muku wadda duk kuka tsallake da human rights zan Haɗa ku tunda ita ba dabba bace kai ko ita dabba ce akwai animal right so ku buɗe kunnuwanku da kyau ku jini"

Yayi maganan yana Kallonsu ɗaya bayan ɗaya kan ya cigaba
"Wallahi ko me kama daku aka ce min an sake ganin gilamawarta a unguwan nan wlh ba zamu yi ta daaɗi ba, ba zan hana danku zuwa gare ku ba sede ita na haramta muku zuwa kusanta, please idan kuna Tunanin wasa nake just try me and see fileing ɗin ku zanyi as attempt murderer, ke kuma uwa ce kaman yadda aka haifeta haka kika haihu babu wadda ya san inda Rana zata faɗa in banda jalihci da ƙarancin addini taya zaki fara fitowa kawai don tashin hankali da takabar mijinki? Allah yayi gaskiya da yace mafi koluluwar jin daaɗin namiji a duniya shine mata ta gari, hakanan annabi ya horemu da samawa ƴaƴayenmu iyaye nagartattu amma ke kam baki daga cikin ko guda Allah ya shirye ki in na shiriya ne"

Kuɗin beli ya fadawa Yusuf, jiki na rawa ya cire ya biya yace ya sallame su, shi kuma kar ya bari su haɗu.

Godiya ummi tayi ta mishi shi kuwa hidiyat yayi consoling yace karta damu babu abunda ze sake faruwa she's safe.

Ko da suka dawo shawarwari ummi ta bata ganin har lokacin hankalinta be kwanta ba yasa Ummi sake kwana, anan suka yanke shawarar sana'ar da zatayi da dubu ashirin din nan.

Kaman da wasa aka saukewa Hidayat Gawayin dubu goma da kuma icce na dubu goma nan take ta fara sana'arta ba kama hannu yaro tana kula da yaranta cikin rufin asirin Allah da ikonsa, babu abunda ya gagaresu na daidai talaka Yusuf ya kan shigo sede kallo kawai yake hadasu baya ce mata ci kanki in ta gaishe shi ba amsawa yake ba.

Raed junior na wata biyu ta sayi freezer ƙarami ta kara sana'ar Kankarar zobo da na nono da su kankarar tsamiya at dsame time tana icce da gawayin ta.

A lokacin kuma ta fara lura da Yusuf da ya kan shigo kullum a birkice, sannan yanzu da kafa take ganinshi ƴan matan ma ya dena kawowa, bata dae dena gaishe shi ba Dukda baya amsawa haka yaran ta kan yi musu dole su gaida uban nasu Dukda tsoron shi da ya riga ya rikide zuwa tsanar shi da suke suma don tun tana iya kare shi har ta dawo shiru, yaran yanzu ne da ake haifar su da wayaun su.

Yau tana zaune tana lissafin kuɗin da zata ware uwar kudin ta sake sayan kayan sana'a sannan ribar kuwa ta je kasuwa ta sayo musu abun bukata zuwa Abinci kaman an jefo shi haka ya faɗo ɗakin, idanunshi kan hannunta kuwa yayi saurin zuwa ya fusge a razane ta mike sede ko sake kallonta be yi ba ya juya ya fice.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now