Dubu goma ta sake fitarwa ta sayi atmpha kala biyu da yadi me saukin kuɗi kala biyu, ta bada ɗinkin turamen za'a yiwa hidayat da Aisha tunda duk ba jiki ne dasu ba zasu iya shearing turmi, yadukan ta bayar aka dinkawa Usman se ta sayi kayan jariri da showel na karamin kudi wadda ze saka a sunan.

Haka ta dawo da kaya niki niki, aka daure rago kayan abincin suka shigar ciki, ta samu Asabe har tayi musu tuwo miya ne Seda ta dawo suka yi anfani da ƴar naman da ta sayo aka yi romon daddawa me jego aka zubawa sossai ta ci, Su Aisha se daaɗi suke ji, da wayon su dae ba'a taɓa ɗaura irin wannan sanwar don su a gidan ba sede baban su ya bayar kuma naman shi a kirge yake sede su sude bojuwa.

Se Dare Yusuf ya fito ya gansu, a kanta ya tsaya da yaron ya gama kare musu kallo kan yace
"Ashe kina da liver da kuma guts ɗin sake dawowa min gida bayan kin kashe mana uba?"

Kanta ta duƙar ƙasa tace cikin rawar murya
"A'a! Taya zan fara kashe Abba?"

Hannu ya sa ya buge mata baki ko damuwa da Ummi dake zaune a wurin be yi ba yace
"Umma zata miki karya kenan, ban yi tunanin kina da idon da zaki sake kallonmu ba bare har ki dawo garemu, Toh bari kiji ni na gaji da ɗawainiya dake da yaranki gaki kullum ke a haihuwa kaman Akuya, tunda har zaki iya mana ajalin uba muma kenan ɗaya bayan ɗaya zaki yi namu to baze saɓu ba, bari na turo miki Umman duk yadda kuwa tace ayi dake haka za'a yi Gayyar tsiya."

Ummi tace
"Haba Yusuf, kai kam wani irin miji ne? Wani irin uba ne kai? A gaban yaranta kake mata irin wannan cin zarafin? Sati har biyu baka ga matarka ba ta dawo bazaka iya tambayar lafiyar ta da na yaranta ba se ma ka sakata kuka? Baka ganin jarirink...."

"Ke dakata rufe min baki! Me ya kawo ki gidana? Sa ido da shiga sharo ba shanu? To ki kiyaye ni wacce ta kawo ki ma tayi kaɗan bare ke ina ruwanki da rayuwar gidana?"

Harara ta zabga mishi tace
"gida! Gida fa kace ai ni anan ban ga gida ba kurkuku na gani me cike da baƙin duhu da azaba! Wallahi ka guji duniya don tafi bagaruwa iya jima ni de na gayamaka"

Hidayat da ta mike ta kama ummi tace
"Ki rufamin asiri ummi kiyi shiru don Allah"

"ke dakata dallah! Wallahi a gabana wannan azzalumi matsiyacin ba ze ci mutuncinki in kyale ba, da me yake taƙama?"

Kuka ta fara hakan yasa Ummi yin shiru ta zabga mishi harara ta wuce ciki, shi kuwa Hidayat ya kalla kan yayi kwafa irin da ni kike zancen ya fice daga gidan yana ball da tukunya har Seda ya buge tunkiyar dake ɗaure.

"Ummi kin san irin bala'in da kika ja mini?"

Ummi tace cikin zafi
"se kiyi shiru ai kina Kallonsu suna cin zarafinki tun yaranki basu san zafin hakan ba har su zo su sani, har se yaushe zaki cigaba da haƙurin nan! Karshe zuciyarki ya fashe da hakuri ki mutu a banza? Toh wlh idan kika mutu duk a cikinsu babu me asara, yaranki sune da asara kuma suma ba tsira zasu yi a hannun su ba gwara tun wuri ki fara shirin kwatarwa kanki ƴanci"

Ummi bazata gane bane, hakan yasa bata kara magana ba se Raed junior da ta zubawa idanu, kan Aisha ummi ta cigaba da shafawa har tayi bacci.

Ranar suna tun asuba Ummi ta hau aiki ita da Asabe se wata makociyarsu maman Abba, kan karfe goma sun gama duk wani aiki na sunan daidai talaka mutane kuwa sun fara cika gidan, an yanka rago har ana suya, me jego tayi wanka ta saka kayan da ummi ta dinko musu haka ma Aisha da Usman se daaɗi suke ji.

Taron suna yayi kyau daidai gwargwado kuma an ci an sha albarkacin Muhammad, masu kawo kaya sun kawo wasu sun kawo sabulu da omo wasu pampams, ummi Atampha ƴar dubu biyar da Kayan jariri tayiwa Hidayat, mamanta ma Atampha da kayan jariri, har Aunty jamila da Hidayat ta kira da layin ummi itama ta zo showel me kyau da kayan sanyi ta kawowa jaririn.

Se yamma Lis gidan ya fara raguwa da mutane ana ta mamaki don duk taron sunanta batayi goshi irin na wannan yaro ba, kowa se cewa yake yaro ya zo da albarka.

Wuraren biyar Umma da yaranta suka diro gidan, matukar tashi hankalin Hidayat yayi ta zo ta zube kasa tana gaida umman ba tare da ta amsa ba ta hambareta da kafa tace
"da ban yini ba zaki ganni! Salon munafunci da tsugudidi... wallahi hidayat yau se kin bar gidan nan, bazaki kashe uban me gida kuma ki cigaba da cin moriyar gida ba"

Khausar tace
"Umma kiga wai harda taron suna"

Fahariyya tace
"Ai dole tunda ta gama yashe mana uba ta tara ba dole tayi taron suna ba, in ba ta yashe mana uba ba a ina zata samu kudin taron suna harda yanka rago"

Surayya tace
"a dadironta mana kin manta Ya Yusuf yace shi be yarda ma ɗan da aka haifan nashi ne ba.."

A matukar gigice Hidayat ta ɗago daidai lokacin da ummi ta karaso ta sauke ma Surraya wani bahagon mari... Ihu ta kurma ƴan uwanta suka yi kan Ummi itama nata ƴan uwan da ta gayyata suka yi kansu a take gida ya kachame.

#like
#share
#comment

🖤Gureenjoh🖤

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now