Ranar da aka sallamesu napep suka samo ya kwashe musu kayansu har gida bayan tayi ta yiwa Aunty jamila godiya ta kuma rubuta lambar wayanta a paper..

Ko da suka isa gidan sun samu kwaɗon gidan a ɓalle, ta san aikin yusuf ne suka fiffatar da ƴan kayansu suka shiga gida, a kan shimfiɗarta ta kwantar da yaron ta hau tattare gidan Dukda yadda take jin kiɗa na tashi daga sashen Yusuf alamun yana gidan, Usman ta ba kuɗi yaje ya sayo icce ta zo ta hura wuta ta ɗaura ruwa.

Tana tsaka da sharar tsakar gidan kenan taji sallamar Asabe, ɗagowa tayi fuskanta a washe tana mata sannu da zuwa Asabe tace

"Hidayat kin tsoratamu, ina kika shiga sama da sati biyu kullum se na leko tunda naji dawowan baban su Aisha sede shiru ba ki ba yara? A'ah haihuwa kika yi ne?"

Murmushi hidayat tayi tace
"eh wallahi ranar da abun ze faru na tura su Aisha su kiramin ke sede bakya nan"

Tace
"la shakka ranar na dawo su habiba ke cewa kina ta aikowa na saɓa hijabi na zo na samu gidan a garkame"

Hidayat tace
"ranar ne aka yi min aiki, kuma a ranar Abbana ya rasu"

Salati Asabe ta saki tana mata gaisuwa, ita ta karbi Sharan ta karasa, a varender ɗinsu ta shimfiɗa taburma Nan Asabe ta fita chan se gata da daidaikun matan unguwan masu yi mata ta'aziyya na yi masu yi mata murnar karuwa na yi.

Zulai da ta shigo tace
"yanzu kenan kun yi suna a asibitin kenan?"

Hidayat na murmushi tace
"eh sunanshi Muhammad Raed"

Habiba tace
"Raed..! Me kuma hakan?"

Hidayat na murmushi tace
"Sunan larabci ne kuma yana cikin ma'anonin sunan Muhammad wato Shugaba ko jagora"

Baki Zulai ta taɓe, sauran matan na masha Allah.

Wata A'i daga gefe tace
"to yanzu baza'a mishi yanka ba kenan?"

Hidayat a zuciyarta tace dole kuwa in mishi yanka in shaa Allah, a fili tayi murmushi tace

"Ina gayyatarku duka in shaa Allah jibi za'a yi sunanshi"

Aah masha Allah! Kawai suke ta cewa.

Bayan dayawa sun watse ta ari wayan Asabe ta tura Usman ya saya mata credit ta zo ta saka ta kira Ummi.

Ummi na ɗagawa Hidayat ta fashe da kuka, ummi ta rikice duk yadda ta lallashi hidayat kasa shiru tayi tace tana zuwa yanzu yanzu.

Ba'a yi awa guda ba se ga ummi har lokacin kuka hidayat take, tana ganin ummi ta tashi ta rungume ta, she really needs a shoulder to cry abubuwan sun mata yawa da shekaruntan nan, kwarai ba don Muhammad ba da rayuwarta ta gama nakasa, baabinta maybe da an jima da rufewa, ummi tace

"Hidayat kina ruɗa ni, menene? Me ya faru kike kuka haka?"

"Na Rasa Abba ummi, Abba ya tafi ya barni"

Salati ummi ta saki ta sallame, zama suka yi tayi ta rarrashin hidayat har tayi shiru ta yi mata ta'aziyyan Abban, nan hidayat ta ɗauko yaron ta mika mata, cikin sanyinta ta mata bayanin duk abunda ya faru, Albarka tayi ta sawa wannan Muhammad ɗin da duk basu san shi ba in ka cire Aisha da Usman.

Asabe ce tayi mishi wanka, yayinda hidayat ta zare dubu hamsin cikin dubu saba'in da ya saura a hannun su tace ta je tayi duk abunda ya kamata, ummi na fita gidansu tayi ta sanar wa mamanta tare da diban kaya akan bazata dawo ba se bayan suna, suma ƴan gidansu sun yi alkawarin zuwa mata sunan da gaisuwan Abba don duk wadda ya san ummi se ya san ƙawarta hidayat.

Kasuwa ummi taje ta samo tunkiya ƴar dubu ashirin da biyar, tayi sayayyan kayan abinci har na dubu goma, akan zata ɗibi wadda zata yi abincin suna sauran ta ajiyewa hidayat ɗin su dinga amfani dashi kan suyi Tunanin sana'ar da zata fara kuma.

KOWA YA GA ZABUWA...Όπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα