Murmushi tayi me kyau tace
"Thank you..."
Se ta rasa sunan da zata kirashi shima murmushi yayi mata for the first time yace
"call me Daddy"
Tace
"thank you Daddy, idan mama ta tashi Allah yasa kar tayi faɗa na kula stranger"

Yana murmushin wayon yarinyar a ranshi yana kwaɗaita mata samun Ingantacciyar ilimi yace
"bazata yi ba idan kika ce mata Daddy Muhammad ne tell her masu sunan basa cuta bare cutarwa"

Godiya tayi mishi, ya ɗaga Farah dake ta fushi ya saka a mota kan ya shiga, Seda yaga shigar Aisha cikin ward ɗin kan yayiwa drivern umarni da su wuce.

Dayawa suna ganinshi Miskilin gaske marar fara'a da sakewa sede yana wasa da yaranshi sossai a ganinshi idan be musu ba wa ze musu? Shi kaɗai suke da a duniya matsayin uwa da uba da dangi, be taɓa Tunanin za'a samu worst uba irin nashi uban ba seda yanzu yaga Aisha ya tabbatar uban ta ma irin nashi ne, hakan yasa ta tsaya mishi a rai.

Daidai last flyover da zasu ɗauka zuwa hanyar Airport idanunshi ya faɗa kanshi, ko ba'a faɗa ba wannan shine Yayan Aisha, da sauri yacewa drivern
"wait!"

Parking suka yi, ya sauke glass yana kallon Usman dake bin mutane yana roko kaman almajiri, wani irin tausayin su ne ya sake mishi dabaibayi, ɗaya daga cikin masu tsaron shi da ya sauko don jin Abunda ogan nasu ke bukata ya kalla yace
"call that boy"

Da sauri yaje ya kira Usman Dukda a tsorace yake sede haka ya biyo shi yana share hawaye akai akai, ganin Raed yasa ya karasa yace
"Dan Allah ka taimaka min mamana bata da lafiya tana asibiti karta mutu ko ta haukace"

Dauke kai Raed yayi yana shafa hancinshi da bayan hannunshi, da kyar ya iya controlling kanshi kan ya juyo ga Usman dake ta kallonshi yace
"a ina ne asibitin? Ina babanku?"

Usman yace
"nima ban sani ba duka, na kasa gane hanyar gida kuma nima ban san sunan asibitin da mamana take ba"

Yanzu da be ga yaron nan ba da wannan uwar ta rasa shi kenan har Abada, eh har Abada mana baze gane gida ba ba kuma ze gane asibiti ba, idan uwar ta mutu ba taimako shikenan Aisha ma zata gantale, idan kuwa ta warke ta ina zata fara neman yaronta a birnin Kano?

"What a worthless father nd a heartless husband!"
Yayi exclaiming kan ya sake kallon Usman yace

"ur mom zata samu lafiya ok? just follow him he will get u back to her"

Yace
"ka san mamana?"
Raed ya ɗan yi murmushi yace
"yeah harda Aisha also"

Washe baki Usman yayi yace
"ka biya ma mamana kuɗin?"

Kai kawai Raed ya gyaɗa don be cika dogon surutu ba ko da yaran Nashi ma, wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskan Usman yace
"Allah ya biya ka da gidan Aljanna ya sa a mizani haka mama tace a gayawa duk mutumin kirkin da yayi mana abun alkhairi"

Murmushi kawai Raed yayi, Usman ya bi wadda aka Haɗa shi dashi zuwa motan karshe suka juya dashi zuwa asibiti yayinda Moh Raed yayi Airport.

A asibiti kuwa gaban ɗakin da Hidayat take Aisha ta tsuguna rungume da jakan maman, lokaci lokaci take murmushin jin daaɗin mamanta zata Samu lafiya, taɓata taji an yi da sauri ta ɗago se taga senior nurse na jiyan nan ce, ta mike tana kallonta se kuma tace
"Ina yini?"

Matar tayi murmushi tace
"Maman ki zata samu lafiya ko"

Tace
"haka Daddy yace in shaa Allah"

Matar tace
"masha Allah" a zaton ta ma daddyn baban su take nufi don ita bata ga Raed ba.

Tace
"mu je in miki wanka ki sauya kayan nan, na kawo miki na ƴata ina yayanki?"

Murna Aisha ta fara kan tace
"Na gode, yayana kuma ya tafi wurin Abba"

KOWA YA GA ZABUWA...Όπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα