Page 38- Kai Amarya

En başından başla
                                    

Daren biki Umma ta hada duk kayan kitchen din da ta tara min, su Mama suka je kai kaya. Ko da suka dawo dukkansu santin gida kawai suke. Cewa suke ba karamin kokari Haidar ya yi ba, parlor biyu da bedroom uku. Kuma duk an cika su taf da sababbin kayan kasar waje. Sannan ga kitchen da dining area su ma din duk ciccike suke. Suka dinga shi masa albarka don ba kowanne namiji ne zai iya kokarin da ya yi ba, duk da ya san cewa ba a budurwa zai same ni ba.

Da yamma aka gabatar da walima, na sha tsadadduyar doguwar rigar Egyptian abaya na yafa dan karamin mayafinta. An sha wa'azi sai daf da maghriba aka gama kowa ya watse.
A daren kuma mai lalle ta zo ta zana min dan ubansu ja da baki, ba karamin haska fatata ya yi ba kuwa.

Washegari da safe su Nusaiba da su Anti Salima suka zo kawo lefe. Akwatuna dozin daya cif, saiti biyu kenan kowanne saiti tsadadde ne. Kayan ciki kuwa na ji kowa na yabawa babu kanana.
Ni da Nusaiba mun yi farincikin ganin juna da aka raka ta gidan Mama inda muke tare da tsirarun kawayena da wasu daga cikin 'yan'uwanmu daidai kaina.

Tare da su aka sha yinin biki. Da yamma bakin lace mai adon golden brown na sanya, dinkin riga da skirt da ya bi jikina tamkar fitted gown, sannan aka bi da makeup da daurin head golden brown mai hawan-hawa. Babu wanda bai yi santin kyan da na yi ba.

Sai dai a lokaci guda da tunanin Ummu ya fado min, bakidaya na lalata kwalliyar. Kuka nake sosai, ina tunanin da tana raye da yanzu da ita ake komai na bikina, da ita ce kan gaba. Amma da babu ita a duniyar, kanwata Safra ita ce ke dawainiya da kawayena da bakin da suke zuwa.

Kowa ya ga kukan da nake yi zai yi tunanin na kewar gida da zan yi ne, har sai da na bude baki na ce
"Allah Ya ji kanki Ummu, ya toni asirin azzaluman da suka kashe min ke."
A sannan ne kowa ya gane dalilin kukan. Wasu daga cikin kawayenmu da suka san mu tare suka taya ni kukan, yayin da wasu ke rarrashina.

Karfe bakwai daidai motocin daukar amarya suka iso. Mama da kanta ta zo ta kama hannuna muka karasa gida. A gaban Umma ta dirar da ni, ta ce
"To Fatima, Allah Ya kawo ranar da UmmulKhairi za ta tafi ta bar ki, za ta tafi dakin mijinta kamar yadda ake yi wa duk wata budurwa fata. A matsayinki na mahaifiyarta, ki yi mata addu'a, don na san tuni dai kin mata duk nasihohin da suka dace."

Umma na kuka ina kuka, da kyar ta iya bude baki ta ce
"Allah Ya ba ku zaman lafiya Khairi..."
Daga haka ba ta iya kara fadin komai ba sai kukan da take yi. Masu raunin da ke wurin taya mu kukan suka yi. Anti Talatu kanwar mahaifinmu, da Anti Marwa suka kama hannuwana, Mama ke gaba suka kai ni har inda dankareriyar bakar prado ke bude ana jiran isowar mu.

Nannade nake cikin bakar lapaya har fuskata rufe ruf. Daga nan muka kama hanya zuwa unguwar Modoji da can ne gidana yake.

Da kafar dama, bakina dauke da sunan Allah na shiga gidan. Wani irin ni'imtaccen kamshi ne ya doki hancina wanda ke garwaye da sanyin air conditioner. Hannuna na rike da Anti Marwa ta kai ni daya daga cikin bedroom ta zaunar. Sannan ta yaye min lapayar ta ga yadda har a lokacin kuka nake yi.
Cikin tausayi da sanyin murya ta ce,
"Ki daina kukan haka nan mana UmmulKhairi. Kowacce mace da kike gani sai da ta taka wannan matakin. Na sani rabuwa da iyaye babu dadi, barinma ke da kuka yi kyakkyawar shakuwa ke da Yaya Fatima. To amma ya za ki yi? Aure dole ne, kuka ba mafita ba ce ba sai ma wani ciwon da zai iya janyo miki."
Ta zauna da kyau, sannan ta janyo ni cikin jikinta.
"Ina so ki zama mai kyakkyawar dabi'a Khairi, irin dabi'ar da mazajen kwarai suke alfaharin matansu na da ita. Ki kyautata wa mijinki, don wallahi, kin ji na rantse, irin su Aliyu kadan ne a duniyar nan. Ya yi duk abin da ya kamata dan halak ya aikata. Babu hanyar biyan sa face ki kyautata masa, ki yi masa biyayya, sannan ki kaunaci ahalinsa tamkar yadda za ki kaunaci naki. Ki kiyaye harshenki, ki san irin maganar da za ki dinga jifan mijinki da ita, don idan har kika kasance daya daga cikin matan nan da ba su iya magana ba, kina yab'a masa kowacce magana da ta zo bakinki, to sannu a hankali shi ma zai koya, zai dinga mayarwa idan kin yi masa.
Duk yadda kike ganin mijinki na son ki idan ba ki kyautata masa yau da gobe soyayyar nan za ta ragu, domin kuwa shi dai hakuri hatsin tukunya ne, ana dibarsa yau da gobe dole wata rana zai kare.
Ke ma kuma ki kasance mai hakurin, yau da gobe ta wuce komai Khairi, zaman aure dukkaninsa dan hakuri ne don ba kullum ake samun yadda ake so ba.
Akwai kuma halin rayuwa, ba a dawwama cikin akwai; saboda halin akwai da babu.
Ki ji tsoron Allah ki tsarkake zuciyarki, yanzu wani zamani muke wanda da yawan matan aure sun mayar da bin mazan waje ba komai ba, da aurensu suna sharholiyarsu a waje.
Ki dinga dora shi bisa hanyar kyautata wa danginsa, ba wai iyakacin danginki kadai za ki sanya ya yi wa hidima ba, danginsan ma naki ne ko kina so ko ba kya so.
A karshe sai in kara jaddada miki da ki ji tsoron Allah, ki rike ibadarki, ki tsayar da sallah, sannan ki tsayu wajen ganin mijinki ya kiyaye ibadarsa shi ma. Akwai hadisin da aka ce mata tagari rabin addini. Idan ka same ta sai ka yi kokarin cikashe sauran."

Kuka nake sosai har zuwa lokacin da ta kai aya, ta sanya bakin gyalenta ta dinga share min hawaye amma wasu ne ke sauka.
Gidan a cike yake da 'yan kawo amarya, wasu tsakaninsu da Allah ganin gida suke, yayin da na tabbatar da wasu kam gulma da kwarmato suka zo yi.




Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin