Chan ɗakin shi ya bar hidayat a time ɗin karfe wurin tara na dare ya tura kofan ɗakin umma ya shiga, tana tsaye jikin wardrobe tana duba abu ganin yanayin fuskanshi yasa ta rufe wardrobe ɗin ta bashi hankalinta yace

"Amina ashe ba kya tsoron haɗuwar ki da ubangiji? Amina ina abun cuta a jikin Hidayat? Me ta sani nan duniya? Me ta yi miki da zaki dinga zaluntarta? Mahaifiyarta ranta ba'a hannunta yake ba da a hannunta yake na tabbatar bazata taɓa zaɓan tafiya ta bar yarinyar ba, kema kuma haka naki ran ba'a hannun ki yake ba ko yanzu Allah ze iya ɗaukewa idan aka yiwa naki abunda kike yiwa ɗan wani zaki ji daaɗi? Kiji tsoron Allah ki Sani Allah baya zalunci kuma baya barin me yi..."

Dakatar dashi tayi tace
"yanzu ita hidayat ɗin ce ta ce maka ina zaluntarta da har zaka zo ka cika ni da wa'azi? Allah na tuba ai idan zan mutu in bar yarana ma ba zan bar su a titi da kokonton ko ƴaƴan sunnah suke ba ko ƴaƴan zina, dangi gaba da baya Alhamdulillah, ita fa? Wa ya san daga inda uwarta ta yayumo ciki ta kawo kai kuma me tausayi da imani ba dangin iya ba na Baba ka ɗauka ka rike ta mutu ta barmu babu wani hujja ko haske, yarinya kyau kaman ita tayi kanta, wa ma ya sani ko kai ne ka yayumo mata cikin aka korota daga garin su ta zo ka saka ni riƙeta har ta mutu ta bar ƴar Zi...."

Marin da ya sauke mata ne ya hanata karasawa, a zafafe yake kallonta yace
"dama abunda ke zuciyarki kenan shine se yau kika amayar? Ina me baƙin cikin Haɗa zuri'a dake Amina baki da zuciyar imani da tausayi, wa ma ya sani irin wahalar da baiwar Allahn nan ta sha hannunki? Ki tattara kayan ki ki koma gidanku idan aka karanta miki karatun da ya kamata se ki dawo ki gyara rayuwarki karki ɓata min rayuwar yara da wannan halin kafurcin"

Yana kai nan ya juya ze fita da gudu ta sha gabanshi tace
"ni ka mara akan wanchan ƴar shegiya..?"

Kara zabga mata mari yayi yace
"idan har zaki cigaba da kiran hidayat da irin sunayen nan hannuna ba ze gaji da hukunta ki ba"

Ihu ta kurma tace
"Wallahi ba zan tafi ba se da hujjah, ba zan bar gidan nan ba har se ka ban hujjar tafiya"

Yace
"hujja kike so? OK ki je na sake ki saki ɗaya"

Hannu ta sa a kai ta kurma ihu
"akan ts...." Fasa faɗar tsinanniyar tayi ganin ya sake ɗaga hannu tayi saurin cewa
"yanzu akan hidayat ka sakeni Abubakar? Akan wannan yarinyar?"

Yace
"ba saki kaɗai ba, zan auro wacce zata kula da ita tunda ina da damar hakan"

Me umma zata yi! kuka wiwi kaman yarinya Alhj ya ce ze yi aure, a haka ya fita ya barta, a kofar ɗakin ya samu sauran yaran be kula su ba ya fice abun shi, suna ji suna gani umma ta Haɗa akwati ta fice.

A ranan a sashen Abba hidayat ta kwana bayan tafiyan umma ma fita yayi ya sayo musu gasashen kaji da su ice cream ya biya super market ya sayi sabon lunch box hadadde, Washegari a sashenshi ta ci abincinta suka fito mota a tare, yaran basu ɗauko mata lunch box ba ya kalli khausar bayan sun gaishe shi yace
"koma ki ɗauko wa hidayat basket ɗinta"

Juyawa tayi bakin ciki kaman ya kashe ta, haka ta je ta ɗauko ta kawo musab dake zaune a gaba ya kalla yace
"mus'ab koma baya"

Fita yayi ya koma baya da kanshi ya saka hidayat a gaba yace
"as from today wurin zamanta kenan Habibu driver duk ranar da ka kuskura muka haɗu ko daga nesa ne ban hange ta ɗaga gaba ba a bakin aikin ka, sannan duk ranar da ta sake fita ba lunch box baka gayamin ba shima a bakin aikin ka"

Yana kai nan yayi musu waving bayan ya ba kowa kuɗin break ɗinshi suka fice.

A mota sun yi shiru ne sbd sun san ko an koma habu ya faɗawa Abba in ya tashi dukansu babu umma me karɓansu, a school ne suka Taran mata suka mata kacha kacha Aunty khausi har niyyar dukanta tayi aka raba su.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now