Malamin ya kalle su yace, "Kamar yadda na fad'a muku babu batun asiri a tare da lamarin nan soyayya ce daga Allah wacce ya dasa masa ita a zuciyar sa."  Mama tace, "To meyesa yake sonta?."
"Ranki ya dad'e soyayya ce da kuma had'uwar jini ce."
"Ban amince da wani had'uwar jini ba dole akwai wani abun a k'asa. Kai kanka da zaka ga yarinyar na tabbatar zaka bada shaidar akwai abinda aka kulla." Mum ta kalle shi tace, "to yanzu ya za'ayi kenan?." Malam d'in ya sake duba farantin sa sannan yace, "Asad yana son yarinyar sosai lokaci guda Allah ya saka masa ita a ransa, yana sonta kamar ya had'd'iye ta. ita kuma yarinyar kamar har yanzu babu wani tsayayyen abu a ranta amma dai......" Mama ta katse shi ta hanyar fad'in, "Amma me..? A datse soyayyar kawai."

Malam yace, "ranki ya dad'e kenan hakan yana nufin a yiwa Asad aiki ko?." Mama tace, "A'a ba tun yau ba kasan bana san a yiwa Asad wani abu a yiwa ita yarinyar amma bashi ba." Malam ya murmusa yace, "Ranki ya dad'e banda abin ki ita da babu abu tsayayye a ranta shine akwai soyayya a ransa sai dai in shi za'a yiwa aikin a cire ta daga zuciyar sa. "Mama ta girgiza kai tace, "A'a ko kad'an bana son hakan, a nemo wata hanyar." Malam ya sake bincikawa ya kalle su yace, "Kun sani bana fad'ar k'arya dan na samu wani abun a wajan kowa, haka zalika bana fad'awa mutum abinda zaiji dad'i koda bana jin dad'in na gani ba, ina fad'ar abinda Allah ya bani ikon gani ne komai d'acin sa. Maganar gaskiya auren yarinyar nan da Asad bazai lalatu ta sauk'i ba akwai wani abu mai k'arfi da yake rik'e dashi."

      A firgice Mama ta kalle shi tace, "A lalata shi ta k'arfi, a saka k'arfin da yafi nasu k'arfin a tarwatsa shibana son hakan ta kasance ne ko a mafarki." Malam ya jinjina kai kafin Mum tace, "A yiwa yarinyar asirin da zata ji ta tsane shi gabad'aya taji bata son ganin sa ko kad'an, kaga koda tayi niyar amincewa dashi zata fasa." Malam ya sake dubawa kana yace, "Yiwa yarinyar aiki ba abu bane mai sauk'i, tana da rik'o da ibada fiye da tunanin ki Hajiya Sadiya." Mama ta dafe kai cikin takaici tana cizan yatsa zuciyar ta na tafasa sabida b'acin rai jikin ta har zafi ya d'auka kamar mai zazzaɓi, bata k'aunar talaka ya rage ta balle kuma y'ay'an ta.

     Mum tace, "A kashe ta ko a haukata ta!." Malam ya yi murmushi yace, "Kar ayi gaggawa ranki ya dad'e, shawara a nan aje a same ta a tsoratar da ita har a cusa mata tsanar auren tak'i amsawa zata aure shi, a fitar mata da sha'awar auren jinin sarauta a zuciyar ta. A ganina wannan itace kawai hanya mai sauk'i in tak'i sai a dauki mataki." Mum tace, "Kenan mune zamu same ta?."
"Kwarai ku da kanku zaku same ta in akayi sa'a hakan zaiyi aiki, domin indai ba ita tace bata so ba Asad bazai fasa auren ta ba haka mai martaba bazai fasa bashi ita ba."

Mama ta sauke numfashi tace, "ya batun sarautar sa?." Malam ya bincika kana yace, "Tana nan, kamar yadda na sha fad'a miki shine zai mulki katagum har gobe maganar haka take; amma kamar koda yaushe akwai qalubale manya ma wanda suka fi na baya yawa. Na farko maganar auren nan zata sake dagula komai, na biyu wad'annan wanda nake fad'a miki suna aiki a kansa sun sake zage dantse sun k'aro makaman yak'in yak'ar ku, na uku suna gab da yin nasara a kanki da kuma kan Asad d'in." Mama ta sauke ajiyar kana ta sassauta murya tace, "ya batun tsarin jikin sa?."

"Ranki ya dad'e komai lafiya yana k'ok'ari wajan ibada da rok'on Allah shiyasa suka kasa nasara akan sa har yanzu." Kai ta girgiza kafin ta mik'e tsaye tace, "Zamuyi waya, muje" ta fad'a tana yin gaba tare da sakin niqab d'in fuskar ta. Mum ta kalle shi bayan ta tashi tace, "Akwai maganar da zamuyi ma tattauna a waya" ta fad'a tana fita daga d'akin tabi bayan Mama da sauri. Suna shiga motar Mama ta kalle Mum tace, "muje gidan su yarinyar."

Zaro idanu Mum tayi tace, "muje muyi me? Kin manta rashin kunyar ta dana baki labari?; marina fa tayi."
"Zamu je mu gyara komai ne yanzu."
"Kamar ya mu gyara Fulani? Kema in ta maren ki fa?."
"Ko uban uban ubanta bai isa ya tab'ani ba balle ita; dalilin da Malam ya fad'a shine zai kai mu wajan ta."
"Amma fulani......?" Dakatar da ita Mama tayi ta hanyar cewa, "Muje kawai. Zan nuna miki gidan da suka koma."

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now