"Wannan ba komai bane ba Sadiya na fara maganin yarinyar shi ba wani abin damuwa bane in nace bana so zance ya k'are; ita yarinyar ita nake so na jawa kunne ko dan tasan wutsiyar rak'umi tayi nesa da k'asa. Ina so tasan ruwa fa ba sa'an kwando bane, ta banbance tsakanin zare da abawa." ta girgiza kai cikin gamsuwa tace, "Haka ne, yana da kyau mu tauna tsakuwa dan aya taji tsoro. Amma wanne mataki kika d'auka a zuciyar ki wanda kike gani zamu aiwatar dashi?."

Mama ta kalle ta tace, "Shiyasa na kira ki domin inaso ko meye a aiwatar dashi yau bana son b'ata lokaci." Mum tayi jim tana tunani kafin tace, "Mu saka a d'auko ta a sace ta mu bata wahala sosai a sake b'alla k'afar ta ta kinga in aka mata haka zata shiga hankalin ta." Mama ta girgiza kai tace, "Shawara ce mai kyau wannan amma bazata yu ba, in labarin ya bayyana daga baya sunan mai martaba zai b'aci a garin nan za'a dinga yawo dashi ace nice na aikata hakan. Canja wata."
Mum tace, "Haka ne. Mu tura mutane su je gidan ayi mata dukan tsiya ita da iyayen ta inda dama a b'alla ta a b'alla iyayen ta a kuma yi musu kyakykyawan warning wanda zai shiga jikin su, kin ga zasu ji tsoro dukkan su bama ita kad'ai ba har da iyayen ta."

Mama tayi murmushi cikin jin dad'in maganar tace, "Wannan shawarar tayi d'ari bisa dari da kuma ita zamuyi amfani; amma fa bana son aje da wani dogari daga gidan nan dan tonuwar wannan maganar ma b'ata suna ne a idanun mutanen gidan nan balle mutanen gari, k'askanci ne a wajena ace yaron dana fi so cikin y'ay'ana yana bibiyar wata y'ar talakawa. Inaso aje dake domin kiyi musu kyakykyawan warning wanda zasu shiga hankalin su." Mum tace, "Wannan ki d'auka an gama ranki ya dad'e, zan samu mutane a waje muje muyi duk abinda kika ce ai abu ne mai sauk'i."

Mama ta girgiza kai tace, "kuje a fara aiwatar da komai yanzu bana son b'ata lokaci Sadiya ke kin sani." Ba musu Mum ta mik'e tace, "An gama ranki ya dad'e" tana gama fad'ar hakan ta fita daga gidan da sauri.

         Mum na fita gida ta koma Jidda bata nan gidan babu kowa jikin ta har rawa yake dan tama fi Mama son d'aukar mataki a kan Rauda ta d'auki abinda zata d'auka ta fita daga gidan da sauri. Mata da maza ta had'a duka ta biya su aka tafi gidan su Rauda lokacin rana ta bud'e sosai.

            Rauda na zaune akan kujerar da ta saba zama ita da Umma da Inna bata nan sauran sun tafi makaranta, Baba ne ya fito daga d'aki bai fita da wuri ba Umma tace, "Malam kaji ashe duk abinda aka kawo gidan nan ba Anas ne ya bayar ba?." Baba ya kalle su yace, "kamar yaya kenan?."
"Jiya take yiwa Anas mganar magani yake cewa shi duk abinda aka kawo bashi ya bayar ba, hankalina duk ya tashi ban san abin wanda muke ci ba wallahi, da alhairi yake neman mu ko akasin sa duk bamu sani ba." Baba yace, "Bashi bane ba? Kuma Rauda ba wasa yake miki ba kuwa?."

Rauda tace, "Ya rantse min da Allah akan bashi bane ba." Baba cikin mamaki yace, "To amma dashi muka yi maganar ta kawai, da shi muka yi maganar keke napep d'in nan ya akayi wani daban yasan da ita?." Umma tace, "abinda ya d'aure min kai nima kenan." Shiru Baba yayi sai shiru can kuma yace, "Koma dai waye tunda ba sata nayi ba ai shikenan, ban kuma rok'i mutum ba Allah ne ya kawo min tsuntsu daga sama a gashe akan me zan ki ci ni kuwa?."

Umma tace, "Amma malam ya kamata a bincika." Baba yace, "Na bincika ina? Nida ke da kowa bamu sanshi ba ina zanje na bincika nace ga wanda nake nema nida ban sanshi ba?; kar ki d'aga min hankali ina zaune lafiya dan Allah."
"Assalamu Alaikum!" Aka fad'a daga soron gidan aka wuce Baba suka shigo cikin gidan mata uku maza biyu sai Mum ta hud'u. Baba da yake kallon ikon Allah ganin maza garada sun shige shi sun shiga tsakar gidan sa kai tsaye babu izinin sa ya k'araso yana kallon su yace, "Malamai lafiya kuka shigo min gida kai tsaye haka?."

Mum ta k'are masa kallo ta kalle gidan tace, "Au wai wannan gida ne?, ni na d'auka wani kango wanda y'an zaman banza suke zama suna shaye-shaye da yiwa yara fyad'e muka shigo, wai ashe gida" ta fad'a tana kallon wanda suka shigo sai suka fashe da dariya har da tafawa. Rauda ta kalle su tace, "Malamai lafiya zaku shigowa mutane gida kai tsaye?." Jin yadda tayi maganar cikin tsiwa ya saka Mum kallon ta tace, "Oh kece gurguwar kenan, astagafirullah" ta fad'a tana dariya kafin tace, "Yadda aka kwatanta min munin ki ma ashe kin wuce wajan, wannan sai kace ragowar y'an wuta; wanne bak'in zunubi kuka aikata kuka haifo wannan?" Mum ta fad'a tana kallon Baba tana nuna Rauda.

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now