Kiran wayar Suhail ya gani ya jawo wayar ya d'auka ya saka a kunnen sa yayi shiru alamun ana yi masa magana kafin yace, "Alright" daga haka ya yanke wayar ya tashi ya shiga band'aki. Sai bayan ya gama komai sannan ya kwanta da burin Allah ya sa yau yayi mafarki da yarinyar da yake gani ko zai gane ta.

Washe gari da ya farka yaso yaje ofishin fasko amma sabida juma'a ce dole ya tsaya yayi hud'uba ya saka babu inda yaje har aka shiga masallacin cikin gari, kamar ko yaushe yayi hud'uba ya kuma yi sallah bayan an idar ya hau mota ya wuce office d'in. Da kansa ya karb'o faskunan nasu guda uku da hotuna yana shiga mota ya zauna yana kiran agent d'in su a waya, ana d'auka yace, "Egyptian visa nake so guda uku" Shiru ya kuma yi kafin yace, "Okay better" yana fad'a ya yanke wayar ya ja motar sa ya bar wajan.
Gida ya wuce ya ajjiye faskunan ya fito zuwa wajan Mama kamar yadda ya saba. A hakimce ya same ta tana danna waya kamar koda yaushe ya zauna a gefen ta kana yace, "Barka da juma'a."

"Barka Asad" ta furta kawai ba tare da ta kalle shi ba. Shiru ya biyo baya babu wanda ya kuma yin magana kafin yace, "Mama anyi inviting d'ina wani event a Cairo"
"Kwana nawa zakayi?."
"I think one week."
"I'm not allow u to go."
Kallon ya yayi itama ta kalle shi yace, "but Mah...." D'aga masa hannu tafi tace, "Na gama magana Asad, tafiya indai ba ta kwana biyu bace ban amince ka jeta a yanzu ba maybe kaje wani lokacin."

Numfashi ya sauke ya tashi ya fita daga falon nata zuwa falon Hajiya kamar yadda ya saba duk juma'a, tana zaune ita da hidiman ta ya shiga da sallama, "Barka da zuwa Yarima, barka da zuwa fari mai farar wutsiya, fari mai farar aniya, indaroro sai kan soro, kaga tufa mad'aukar d'aki, sikari bakayi farin banza ba, walikiya kake duk inda kabi sai ka haska......" zasu kuma magana ya d'aga hannu sama sukayi shiru cikin girmawawa.
Murmushin yake take tana kallon sa ya zauna a k'asa yana kallon yace, "Barka da Juma'a Hajiya"
"Barka dai Asad, ya jama'a ya kuma k'ok'ari?."
"Alhamdulillah, ina suke?" Ya fad'a yana kallon falon alamun yana neman kannen sa.

"Sunje gidan Yayar ku sai zuwa anjima zasu dawo." Tunda tace Yayar ku ya gano wacce take nufi dan babar yar ta wacce ta kasance babba a gida gabad'aya bata fad'ar sunan ta daman. "Na barki lafiya" ya fad'a yana mik'ewa tsaye tace, "Na gode Asad." Bai amsa ba ya fita ya tafi b'angaren Umma, kamar ita tana zaune itama a zagaye da hadimai suka gaisa kamar waccan ya tafi.
Kasancewar rana ce bai samu mai martaba ya bada kud'in da ake rabawa dan bazai samu damar yi da kansa ba ya koma apartment d'in sa.

Sai yamma sannan wanda zai karb'i faskunan yazo ya bashi ya wuce Abuja dasu domin a buga musu visa.  Bayan wanda karb'a ya tashi yana zaune Suhail ya kira shi, bai d'auka ba har ta katse bayan ta katse ya d'auki wayar ya kira hidiman k'ofar ya bada umarnin a bar shi ya shigo ya ajjiye wayar.
Da sallama ya shigo ya zauna kusa dashi Asad yace, "Suna bin umarnin Mama ne."
Suhail ya murmusa yace, "Hakan yana da kyau sosai tsoron lafiyar kace, sai naga kamar ka rame." Tab'e baki yayi baice komai ba kafin Suhail ya kuma cewa, "me yake faruwa?."

Iska ya furzar a hankali yana sauke numfashi amma bai ce masa komai ba, jin hakan sai shima yayi shiru ya saka hannu a aljihun gaban rigar sa kamar mai neman wani abu, "me kake saka min?" Yaji muryar Asad a kansa  yayi saurin janye hannun sa daga kusa dashi.

Had'a idanu sukayi Asad ya d'aga gira alamun ya bashi amsa, nutsuwa ya aro ya saka a fuskar sakana yace, "me kuwa zan shafa maka Asad? Kalli hannu na mana" ya fad'a yana nuna masa tafikan hannun sa. Murmushin gefen baki Asad yayi kafin ya d'auke kansa daga kallon sa yace, "lafiya ka ke nema na?."
"Normal ina so mu had'u ne kawai."
"Really?" Asad ya fad'a yana wara idanun sa waje.
"Sure, naga duk ka canja Asad kamar baka yadda dani ba, ko da Aliyu nake tare ne ban sani ba?."

Baice masa komai ba ya shafa kai kawai kafin yace, "u can go." Suhail ya kalle shi yace, "Okay bye" ya fad'a yana mik'ewa ya fita  yana mamakin canjawar Asad.  Waya aka kuma yi masa ya kalla yaga masu tsaron k'ofar sane ya share kiran ya katse aka kuma kira ya ja k'aramin tsaki ya d'auka baice komai ba, daga can b'angaren suka ce, "Ranka ya dad'e Allah ya wuci zuciyar ka na dame ka, wata yarinya ce take so tayi magana da kai, tana ta magiya mu barta ta ganka."

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now