"Kina da Yaya?." A sama taji maganar tasa ta juyo ta kalle shi sai taga kamar ba shine yayi maganar ba dan bama ita yake kallo ba. Idanu ta goge ta girgiza kai alamun a'a kafin tace, "Bani dashi."
"Mahaifi?" Ya sake fad'a bai kalle ta ba har lokacin.
"Ina dashi" ta bashi amsa muryar ta na rawa sosai.

Sai da ya kusa kwashe sakan hamsin sannan yace, "kice ana sallama dashi" ya fad'a yana danna lock d'in motar ta bada sautin k'ut alamun ta bud'e. "Na gode. kayi hak'uri da abinda na fad'a maka a baya ban san kai bane ba, ka bawa d'an uwan ka hak'uri ya fita a rayuwata nasan nayi kuskure duk da laifin sane amma na karb'i laifin." ta fad'a murya na rawa sosai.
Yadda maganar take rawa shine ya jawo hankalin sa ya kalle ta yaga yadda hawaye suke ambaliya daga idanun sa sai yaji rauni ya sake mamaye ko ina na jikin sa zuciyar sa na harbawa da sauri-sauri wani abu nayi masa yawo tun daga yatsan sa har cikin kansa.

"Allah ya saka maka da alkhairi ya biya maka dukkan buk'atun ka na duniya, na gode ka taimake ni Allah ya taimake ka kai ma" ta sake fad'a tana bud'e motar ta saka sandar ta sannan ta sauka ta d'auki d'ayar ta kulle motar ta nufi cikin gidan su. Da kallo ya bita yana kallo ta cikin wani abu mai kama da kewa a zuciyar sa da shauki wanda bai tab'a jin makamancin sa ba a kan kowa sai ita kawai, duk takun da zatayi sai zuciyar sa ta buga hakan ya saka shi dafe zuciyar sa yaji tana harbawa a guje kamar zata faso k'irjin sa ta fito.
Gidan yaga ta shiga ya sauke numfashi yana k'arewa gidan kallo tausayin ta na sake ninka na baya a zuciyar sa.

        A can gidan kuwa ana ganin shigar ta Umma ta mik'e tana fad'in, "Alhamdulillah! Malam gata ta dawo" ta fad'a tana nufo Rauda da idanun ta suke cike da kwallah har lokacin. Rik'e ta tayi tana kallon fuskar ta tace, "Rauda ina kika tsaya? Meya faru kike kuka?." Tare suke tafiya har suka k'arasa kan kujerar da take zama ta zauna Umma ta kalli Khairi tace, "Kawo mata ruwa."
Da sauri ta tashi ta kawo ruwa a kofi Umma ta bata tasha ta sauke numfashi hannun ta dafe da kanta da yake mata ciwo.

Baba yace, "Sannu Rauda, daga ina kike Shamsiyya ta sanar dani tun la'asar kika baro gidan ta gashi har anyi i'sha yanzu?." Numfashi take yi kafin tace, "Baba ana sallama da kai a waje." Baba yace, "Waye yake sallamar?."
"Wanda ya taimake ni" ta fad'a tana haki jin hakan ya saka Baba fita bai kuma cewa komai ba.

       "Ummulkhairi kawo mata abinci taci" Umma ta fad'a tana kallon Khairi. Mik'ewa Khairi tayi ta d'auko mata abinci ta kawo mata ta karb'a ta bud'e dan taga meye a ciki, shinkafa ce da miya ta sauke numfashi tunda Anas ya aiko musu da abinci suke ci suke sha a gidan shiyasa take bashi babban matsayi a zuciyar ta.
Kad'an ta fara cin abincin duk jikin ta babu dad'i haka ta fara ci gaban ta sai fad'uwa yake ba tare da tasan dalilin faruwar hakan ba.

        Shigowar Baba da sallama ya saka suka amsa har ya k'araso ya zauna ya kalle su dukkan su har da Inna da Rahma yace, "Yayan wanda ya kad'e Rauda ne. abin mamakin y'ay'an sarkin katagum ne." A tare k'irjin su ya buga har da ita Rauda d'in dan bata san waye ya buge ta ba daman. Umma tace, "ko da naji, yadda yaron da ya buge ta yake da izza kana kallon sa kasan jinin sarauta ne."
Baba yace, "tunda ya buge ta ranar da ya dawo da safe ya kwanta ciwo har yanzu bai farfad'o ba yana kwance, shi wannan d'in yayan sane duk da kamar ana masa dole in yana magana har wani yatsine fuska yake yi yace min yana so a madadin k'anin sa zai saka ayi mata aikin k'afar ta a waccan k'asar ta larabawa meye ma sunan ta...." ya fad'a yana yin shiru alamun tunani.

"Yauwa Misra, gobe zai aiko a d'auke ta a kai ta can ofishin da ake yin fasko na tafiya ayi mata cikin satin nan yake so ayi mata aikin. Yace kuma na baku hak'uri bai san da mara lafiyar da wuri ba da tuni anyi mata magani." Umma da take sauraren sa ta sauke numfashi tace, "Shi ya akayi yanzu ya san da ita?." Baba ya kalle ta yace, "Ai bazai miki k'arya ba."
"nidai Malam ina jin tsoro aikin baza'a yi a k'asar nan ba har sai anje Misra? Kuma haka zamu bada ita daga shi sai ita aje ayi mata aiki muna nan baki sake?."

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now