A sanyaye tace, "haka Allah ya k'addara, babu komai a hakan ma na gode sosai, mun ga abubuwan alkhairi Allah ya saka da alkhairi ya biya buk'ata. Umma tace nayi maka godiya sosai." Murmushi yayi yace, "Babu komai Rauda kar ki damu."

Shiru ya sake biyo baya kafin yace, "Munyi magana da Baba akan aikin k'afar ki in sha Allah tafiyar ki zata dawo kamar dah indai ina da rai tunda aikin ba wani mai wahala bane indai aka bar nigeria, cikin satin nan in Allah ya amince za'a yi aikin." D'ago ido tayi suka had'a idanu yayi murmushi sai tace, "Na gode."
"Haba Rauda ni dake babu godiya wallahi, fatana ki amince da soyayya ta ki yadda dani har ta kai mu ga aure."
Murmushi tayi kad'an bata ce komai ba domin ita kam bata d'auka zai sake dawowa inda take ba sabida lalurar da ta same ta.

"Naga kin gaji sosai ga sallah ana yi, zan koma amma in sha Allah gobe zan yiwa Baba bayanin aiki da za'ayi in sha Allah." Kai ta girgiza kafin tace, "Allah ya saka da alkhairi."
"Amin. Amma kin san wacce irin addu'a nake so kiyi min?."
Kai ta girgiza alamun a'a yace, "Ki min addu'a Allah ya mallaka min ke a matsayin matata." Murmushi tayi sai tace, "Ban d'auka zaka yi wannan fatan ba duba da irin iftila'in da ya same ni."  Murmushi yayi yace, "Wai da sai na guje ki kenan?."

Ya sake yin murmushi yace, "Ni Rauda nake so ba abinda yake tare da Rauda ba, zuciyar Rauda nake so ba gangar jikin Rauda ba. Ilimi, halayya, tarbiyya, nutsuwa, iya magana, girmama na gaba, su nake so a tare da Rauda ba k'afar ta ko hannun ta ba. Rauda a yadda nake jin ki a zuciyata ba fata nake ba ko ido da k'afa da hannu kika rasa wallahil azim ni mai iya auren ki ne, soyayyar gaskiya nake miki ba soyayya dan wani abun ba. Ina fatan ki fahimta?."

Murmushi tayi mai d'auke da jin dad'in kalaman sa ko babu komai ta tabbatar da soyayyar ta ta gaskiya ce a zuciyar sa tace, "Na amince da duk abinda ka fad'a, ina kuma alfahari da hakan." shima yayi murmushi yana kallon ta yace, "A karo na farko da nake ganin murmushi a kan fuskar ki har kike min doguwar magana haka lallai addu'ar da nake ba dare ba rana Allah ya karb'a ya kuma fara biya min." Murmushi ta kuma yi ya kalli agogo yace, "Ana ta sallar i'sha zan tafi."
"Ka gaida gida da mutanen gidan."
"Zasu ji in sha Allah. A gaida Umma da kowa da kowa." Ta amsa da to kafin suyi sallama ta koma cikin gida.

       Sallah Umma ta samu tana Khalil ya d'auko mata kujerar ta ta zauna dan ita ba sallar zatayi ba, bayan Umma ta idar da sallah Inna ma na zaune ita da Rahma Umma tace, "Har ya tafi?." Kai ta d'aga alamun eh.
Baba ne ya shigo da sallama suka amsa ya nemi waje ya zauna yana fad'in, "Ke Rauda Anas yace zai biya ko nawa ne ayi miki aikin k'afar ki, zuwa gobe zan nemi likitan da ya amince da aikin sa ayi komai a gama."
Umma ta kalli shi tace, "Amma malam hidimar yaron nan bata yi yawa ba? Ka duna irin abubuwan da aka kawo mana fa yanzu kuma ya kuma biyan kud'in aiki...? Bafa ayi auren nan ba kar a fara zagin mu a gari."
"Bafa rok'on sa mukayi ba shi yayi niya ya bayar."
"Allah ya saka masa da alkhairi ya biya shi" Umma ta fad'a kawai dan babu yadda zatayi.

Baba yace, "Abinda ya kamata kice daman kenan." Yana fad'a ya juya zai fita Inna tace, "motar kwadayi in ka hau zata sauke ka a tashar wulaqanci." Juyowa yayi ya kalle ta yace, "kinga munafurcin ki da bak'in cikin ki shine ya saka ga y'ar ki nan a zaune kusa dake babu wanda yake tayawa, kuma wallahi in baki kiyaye ni ba sai na bayar da ita sadaka a masallaci."

Bata ce komai ba ta mik'e ta shiga d'aki Rahma ma ta bi bayan ta yaja tsaki ya fita. Umma ta kalli Rauda bayan sun bar wajan tace, "Rauda kin masa godiya yadda ya kamata kuwa?."
"Nayi Umma."
"To ya kike jin sa a ranki yanzu? Nidai ina miki sha'awar auren sa badan yana da abin hannu ba sai dan yana son ki, duk da abinda ya faru dake bai guje ki ba sai ma sake bibiyar ki da yake yi wannan alamu ne na masoyin gaskiya."

Shiru Rauda tayi bata ce komai ba Umma tace, "kiyi tunani ki kuma yi addu'a in shine alkhairi Allah ya tabbatar, in ba alkhairi bane Allah ya watsar da maganar ya kawo miki mai alkhairi." Shiru nan ma tayi bata amsa ba ta lumshe idanun ta nan take fuskar Asad ta ziyarci fuskar ta sai ta bud'e idanun ta tana tsaki.
Umma ta kalle ta ganin bata ce komai ya saka ta ja bakin ta itama tayi shiru.

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now