Umma tayi Jimm sai tace, "mun gode bawan Allah kayi magana godiya dan Allah. bamu da bakin gode masa sai dai muce Allah ya biya masa dukkan buk'atun sa na alkhairi."
Ya amsa da amin Umma tace, "Tsaya bawan Allah a baka tukwici." Yayi dariya yace, "Haba hajiya ki bar shi na gode sosai. Sannan Baba yace a fad'a maka dan Allah kar kace zaka ja keken da kanka ka bayar a dinga yi maka ana kawo maka kud'i har gida."

Baba yace, "In sha Allah hakan ce zata kasance, Allah ya biya buk'atar duniya da lahira."
"Amin ya Allah. sai an jiman ku" ya fad'a yana fita Baba yabi bayan sa.

Rauda dai ta kasa cewa komai bakin ta a bud'e tana kallon abincin da kuma kud'in dake kusa da Umma zuciyar ta na mugun bugawa da sauri-sauri bakin ta ya mutu murus ta rasa wacce irin kalma zata furta. Umma ta kalle ta tace, "Rauda baki ce komai ba bayan duk abinda ya faru ta silar ki ne." Kamar kuma an mata allura a lokacin ta sauke ajiyar zuciya tace, "Umma na kasa magana ne gabad'aya ban san me zance ba."
"Haka zaki ce kuwa Rauda domin duk abinda aka bamu ta dalilin kine."
Kafin tayi magana Baba ya shigo fuska washe yana kallon kayan abincin yana fad'in, "yau ko fita kasuwar ma bazan ba a dafa mana kajin nan muci mu karya k'asusuwa."

Umma ta kalle shi bata ce komai ba ya kalli Rauda yace, "Allah ya yi miki albarka Rauda, ke farar haihuwa ce wallahi ko cikin y'ay'ana ke ta daban ce." Inna da take tsaye tace, "Su kuma bak'ak'en haihuwar sai a zubar dasu ace ba'a so" tana fad'a ta shiga d'aki ya bita da kallo baice komai ba ya cigaba da santin kayan abinci.

Umma tayi dariya tana girgiza kai jin yau Rauda ake cewa ko a cikin y'ay'an sa ita ta dabance, ita yake yiwa wannan fara'ar har yana ce mata farar haihuwa. "Allah yayi mana arzuk'i" Umma ta furta a bayyane tana sauke numfashi.

Umma ya kalla yace, "Nawa ne kud'in da aka baki?." Yana fad'ar hakan ta d'auke takardun kud'in da nata dana Rauda ta rik'e bata ce komai ba ganin hakan ya saka yace, "Ga b'arawo zan sace miki kud'i shine kika d'auke ko?." Ita dai bata furta ba ya girgiza kai.

Ranar Umma ke da girki abinda baya faruwa a gidan ranar shine ya faru, lafiyayar shinkafa da miyar kaji aka yi a gidan kowa y'an makaranta suka dawo cikin ikon Allah akayi bak'i a yayyen su mata duk suka zo aka ci aka sha kowa da farin ciki a zuciyar sa ana ta santin auren Anas da Rauda. Rauda sai taji alfahari a zuciyar ta ganin ana ta santin abinda ta dalilin ta ya samu lokaci d'aya taji Anas yana samu kyakykyawan gurbi a zuciyar ta.

*☆☆*

       A jingine yake da fuskar gado idanun sa a lumshe kana kallon yanayin sa kasan bashi da cikakkiyar lafiya haka zalika baya jin k'wari a jikin sa dan fuskar sa da yanayin sa ya gwada hakan. kamar wanda aka yiwa magana ya bud'e idanun sa yana kallon d'akin kafin ya sauke numfashi ya kalli k'ofar da za'a shigo d'aki jin motsi.
Mama ya gani ta shigo ya tashi zaune sosai yana kallon ta ta k'araso da sauri ta zauna kusa dashi ta tab'a fatar kansa tana kallon sa tace, "Asad ya jikin? Tun d'azu nake zuwa kana bacci."

"Naji sauk'i, Barka da safiya."
"Ka tabbata lafiya lau ka ke?" Ta furta ba tare da ta amsa gaisuwar ba. "Naji sauk'i" ya sake fad'a yana kallon ta. Fuskar sa ta rik'e tana kallon sa tace, "ka rame Asad yanayin fuskar ka ya nuna min akwai abinda yake damun ka bayan ciwon da kake fama dashi, meye?."
"Mama kwana biyu ta daina zuwar min cikin mafarkina, ina so na ganta ban san inda take ba, ina kewar ta sosai" ya furta yana kulle idanun sa yana nuni da tsantsar abinda yake zuciyar sa kenan.

Da mamaki mai had'e da fad'uwar gaba Mama tace,  "Wacece take zuwa mafarkin ka har kake so ka ganta?." Bud'e ido yayi yaga ta kafe shi da idanuwa sai kuma ya dawo hankalin sa tunawa da wacece a zaune kusa dashi ya sauke kai k'asa baice komai ba.

"Magana nake maka wacece?."
"Margayiya Hajiya mai babban d'aki" ya furta a hankali ba tare da ya kalle ta ba. Nannauyar ajiyar zuciya tayi jin abinda yace sai ta murmusa tace, "Ka dinga mata addu'a itace zata amfane ta a yanzu. Ni har ka bani tsoro na d'auka wata ce take kutse cikin mafarkin ka." Shiru yayi bai amsa ba gaban sa mugun fad'uwa haka kawai ba tare da ya san dalilin hakan ba.

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now