Gaban Asad ya fad'i haka kawai ya tsaya yana kallon fuskar ta kamar dai yana so ya san mai irin ta amma bai a ina ba, ya motsa bakin sa ya kalli wanda yake masa magana yace, "ku bata komai." Jiki na rawa yace, "an gama alhaji" ya fad'a yana komawa ya fara had'a mata kaya da yawa. Murmushi tayi tace, "na gode sosai Yaya Allah ya saka da alkhairi, Yayata ce aka kwantar da ita a nan bata iya cin komai akace nazo na siyo mata kuma d'ari biyun kenan damu itama dak'yar Baba ya bayar" ta fad'a tana kallon sa.

        Kallon ta shima yake jin tana magana kamar ta had'd'iye radio ba commer babu full stop zuba kawai take yi, kallon asibitin yayi ya dawo da kallon sa gare ta ganin asibitin da suke zuwa ne kuma wanda yake k'ark'ashin kulawar Mama to meya kawo yarinya kamar wannan cikin sa bayan yasan hundred percent na kud'i ne kud'i ma kuma ba kad'an ba..?. A lokacin aka kawo mata manyan ledodoji guda uku an cika su da kayan marmari da murna ta kalli ledar lokacin da yake karb'ar tasa ta apple tace, "na gode Yaya, dan Allah ya sunan ka?."

Sai ya samu kansa da yin murmushi a hankali yace, "Aliyu."
"Na gode Yaya Aliyu, kuma wallahi kana da kyau kamar mutanen nan na tv da nake gani a gidan Yaya Ummi, kuma gashi kana jin hausa, dan Allah d'an garin nan ne kai?." Shi dai Asad kallon ikon Allah kawai yake ganin yarinya mai shegen surutu kamar wata y'ar tsana.
Sai kuma tace, "Umma zata min fad'a tace ina na samo kud'i na siyo wannan zata kuma ce rok'ar ka nayi."

         Shi kam ya gaji da surutun ta ya d'aga glass sama bai ce komai ba yaja motar sa ya tafi ta bishi da kallo ta kinkimi ledojin dak'yar ta shiga asibitin. Tana tafiya tana hutawa har ta shiga d'akin ganin ta da leda har uku Umma tace, "Ke bashi kika karb'o ne?."
Tana haki ta ajjiye tace, "Wani ne ya siya min ganin suna tayi min wulaƙanci sunce baza su bani duka a d'ari biyu ba wai sai dai lemo guda biyu d'ari biyu, shine ya siya min duka. Umma baki ganshi ba mai kyau kamar baya jin hausa ya kuma cemin sunan sa Aliyu."

"Ummulkhairi yaushe zakiyi hankali ne wai ke? Baki da girma sam ke sai na jikin ki? Akan me zaki karb'i abin hannun wanda baki sani ba?, rok'on sa kika yi ko?."
"Wallahi Umma ban rok'e sa ba shine fa ya bani, kuma ban tambaya ba muje a tambayi masu siyarwar." Baba da yake sauraren su ya bud'e leda d'aya ya d'auki apple ya ci yana lumshe ido yace, "ni nasan halin ki baza ki tambaya ba, d'auki ki sha kema ki dandali arzuk'i." Umma ta kalle shi kafin ta girgiza kai ta tashi ta d'auki wuk'a ta yankawa Rauda kankana da gwanda da tufa d'in ta k'arasa kusa da ita tana bata tana ci a hankali.

         Sai da Baba ya cika cikin sa dam da kayan marmari ya goge baki yace, "oh yarinyar nan dai ana ta samun alkhairi tunda kika kwanta a asibitin nan, a haka ma fa wai dan Anas baya nan ai da nasan kullum sai munci kaji wallahi. Kai Allah ya dawo dashi kafin a sallame mu." Babu wanda ya tanka ya mik'e yace, "to zan koma Rahma zata kawo muku abinci inda wani abun sai amin waya."
"Basai an kawo komai bama wannan zai isa muci."
"To Khalil, Ummulkhairi muje, sai da safen ku."
"Allah ya tashe mu lafiya."

Bayan fitar su Umma tace, "tsabar san kud'i ya dinga fatan wai kar a sallame ki har sai wani ya dawo kawai dan a basa kud'i, Allah ya kyauta ni ban san irin zuciyar baban ku ba nikam ba haka nake ba wallahi." Rauda tana ji bata ce komai ba idanun ta a rufe tana tauna kankana.

*☆☆☆*
         Asad haka ya gama zagayen sa a gari bai koma gida ba sai bayan sallar i'sha sai da ya shiga wajan Mama yaga Hydar sannan ya wuce d'aki yana shiga d'akin Ummulkhairi ta fad'o masa a rai ya murmusa tuno surutun ta baice komai ba ya shiga band'aki yayi wanka tare da alwala ya fito yayi shafa'i da wutur ya jima yana addu'a sannan ya kwanta.

Abu yaji kamar yana shiga jikin sa ya tashi ya yaye zanin gadon da yake shinfid'e a kan gadon ya dawo zallar katifa yana kallon tsurar katifar amma baiga komai ba, mayarwa yayi ya yafa zanin gadon ya koma ya kwanta ya rasa meyasa yake jin hakan duk sanda ya kwanta a kan gadon sa. Ya jima kafin bacci ya d'auke shi yana juyi yana jin abu na shiga jinin sa kamar tiriri ne yake fitowa daga katifar yana shiga jinin sa.

KWANTAN ƁAUNAOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz