A falon Hajiya iyalan ta zagaye suke da ita maza da mata y'ay'an ta kowa ka kalla zaka hango zallar farin ciki a tare dashi barin ma ita da take ta murmushi ita kad'ai alamun hak'ar ta ta cimma ruwa. Wayar ta da taji tana k'ara ya sakata ta mik'e ta shiga d'aki ta barsu a wajan ta amsa wayar tace, "Abu kamar wasa yana ta zama gaske, sai ga mai martaba da kansa ya janye batun nan."
Waziri yace, "Na sha fad'a miki ki kwantar da hankalin ki komai fa a hannun mu yake amma duk sai ki bi damu kan ki."

Murmushi tayi mai sauti tace, "yanzu meye abu na gaba?."
"Master planer tace mu had'u dake waje d'aya zamu tattauna."
"Yaushe zaka shigo to?."
"Zan shigo zuwa dare." Murmushi tayi tace, "Allah ya kai mu" tana fad'ar hakan ta yanke wayar zuciyar ta cike da farin ciki a bayyane.

*◇*
            Amaryar Sarki Hajiya Rukayya wacce ake kira da Ammi a gidan itama tana zaune da nata iyalan babban d'an ta namiji mai suna Nazif a shekaru bazai wuce shekara sha hud'u ba ya kalle ta yace, "Ammi ni na rasa ganewa kamar kina goyan bayan sarautar Asad?." Murmushi tayi ta kalle su dukkan su tace, "To meye nawa da zanki goyan baya Nazif? Kai dai a musulunce baka kai minzalin jan ragamar al'umma ba to meye abin tayar da jijiyoyin wuya akan hakan?."

        Babbar y'ar ta mace mai suna Zainab wacce ake kira Yaya Zainab tace, "kin huta Ammi, koma waye zai mulki garin nan mudai burin mu ya kasance alkahiri a gare mu da kuma garin." Wacce take bin ta tace, "Shine kawai fatan mu amma ni banga abin tayar da hankali a lamarin nan ba. Asad kuma kaf gidan nan babu mai kirkin sa kawai shi rashin maganar sa ce illa amma kowa yasan halin sa ga san y'an uwan sa baya lakari da yanayin gidan namu kowa na sa ne. Duk da Mama bata son yana sauraren mu amma shi ko a jikin sa, ga ilimi da kud'i a hannun sa."
Ammi tace, "Allah ya kyauta" duk suka amsa da amin suka cigaba da hirar su gabad'aya maganar mulkin katagum bata gaban su su kam.

           Hydar da Aliyu da kuma Asad ne a zaune a b'angaren su babu wanda yake yiwa d'an uwan sa magana dukkan su waya ce a hannun su suna dannawa hankalin su a kwance, waya Hydar ya d'auka ya kira Dr ya sake tambayar sa jikin Rauda ya tabbatar masa da komai daidai. Asad ya dafe kansa da yake mugun ciwo yana yatsine fuskar sa. Hydar ya kalle shi yace, "Deaf ya dai?." Yatsine fuska yayi yace, "nothing" yana fad'a kawai ya tashi ya shiga d'akin sa ya kulle k'ofar ya zaga baya ya bud'e varanda yana kallon harabar gidan ana ta hidima da shige da fice.

Allah ya sani baya k'aunar mulkin da ake son k'ak'aba masa ga jifa da yake sha tun daga fara maganar sarautar nan yake ganin mutane da yawa wanda baiyi tunani ba a mafarkin sa ina ga an bashi sarautar?. Burin sa kasancewa a madina ba'a Nigeria ba a can yake burin yin aiki kuma burin sa ya cika amma Mama ta hana.

Lumshe idanun sa yayi mafarkin da yayi a jiya ya dawo masa kansa ya wara idanun sa yana k'ok'arin tuno fuskar yarinyar da ya gani ta taimake sa a mafarkin amma ya kasa, furzar da iska yake yi jikin sa na kyarma hankalin sa ya tashi ji yake gidan gabad'aya yana juya masa sam baya son zama a cikin sa, duk yadda yaso daurewa kasawa yayi ya fito ya d'auki makullin mota ya fita har lokacin Hydar da Ali suna zaune.

        Hydar ma fita yayi aka bar Aliyu a zaune yana ganin fitar su ya mik'e ya shiga d'akin Asad yana k'arewa d'akin kallo kamar yana neman wani abun a ciki. Babba ne d'akin sosai komai fari ne a d'akin hatta tiles d'in d'akin fari ne labulaye carpet komai fari ne a d'akin, fari kuma tass babu alamun daud'a a tare da ko ina sai khamshi da yake yi. tab'e baki yake yana girgiza kai yana hasahen abinda ya kamata yayi a d'akin kafin ya fita daga d'akin.

         Hydar yana fita asibitin ya koma a lokacin Umma ce kawai a ciki ya shiga da sallama ta amsa tana kallon sa yace, "Sannu Mama, ya mai jikin?."
"Da sauk'i gata bata farka ba har yanzu." Kallon ta yake yi ya runtse idanu ya rasa dalilin da ya saka gaban sa yake fad'uwa in ya kalli fuskar ta sai yaji wani abun yana shigar sa ya rasa meye.

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now