Yaya ta girgiza kai tace, "Allah ya kyauta, lamarin Baba sai addu'a."
"Amin, kin san me Yaya."
"Sai kin fad'a."
"Mafarki nayi ina makaranta ina karantar aikin jarida." Yaya Ummi ta dara kad'an tace, "Wannan mafarki naki na aikin jarida Allah yasa ya tabbata Rauda."
"Badai a gidan Baba ba."
"Ha! Ha! Daman sai dai in kin auri Anas" Yaya Ummi ta fad'a tana dariya.

Rauda tace, "Kin san kuma kwana biyun nan sai na dinga mafarkin mutane masu fuska iri d'aya ko wanne da rawani a kansa, d'aya yana b'angaren dama d'aya hana haggu, a tsakiya kuma nice in na tafi wajan d'aya sai na kasa k'arasawa in na koma wajan d'aya ma sai na kasa zuwa. Ina yawan wannan mafarkin amma har yanzu na kasa rik'e fuskokin mazan guda biyu."

Yaya tace, "tofa, Allah mai hikima shi kad'ai yasan meya b'oye a cikin mafarkin naki, koma dai meye Allah yasa alkhairi ne shine fatan mu."
"Amin Yaya." Daga nan suka cigaba da hirar su.

*☆☆☆*

           Tunda garin Allah ya waye ya samu labarin mai martaba da Asad sun fita hankalin sa yayi mugun tashi, safa da marwa yake a d'akin ransa a b'ace zuciyar sa yske so ta bashi mafita akan Asad amma har lokacin ya kasa samun matsaya.

Tashin hankalin sa da damuwar sa bai san me zasu tattauna da mai martaba ba abinda yake sake d'aga masa hankali kenan ya kasa zaune ya kasa tsaye, Suhail ne ya shigo ganin halin da mahaifin sa yake ciki ya saka yace, "Ranka ya dad'e lafiya?."
"Asad ya fad'a maka dalilin fitar su da mai martaba?."
"A'a bai fad'a min ban ma san zasuyi tafiyar ba."
"Oh god! Laifin kane Suhail da ka bashi madarar nan jiya duk da ba haka ba, yanzu gashi sun tafi taro Kaduna ko ni ba'a nema ba matsayina na waziri a masarauta daga shi sai ni amma ya tafi daga shi sai Asad, me suke so su mayar dani ne a masarautar nan?."

Yadda yake fad'a tashin hankali ya bayyana k'arara a tare dashi Suhail ya kwantar da murya yace, "Kayi hak'uri Abba ka bani lokaci matuk'ar ina raye babu wanda zai mulki garin nan sai kai."
"Kana shirme a haka zan mulki garin?! Ka manta kane ka b'arar da damar da ya k'i shan madarar nan jiya?, kasan mahimmacin maganin da na baka kuwa Suhail?. Na baka sabida na yadda dakai amma sai ka bani kunya" Ya fad'a da fad'a sosai yana kallon sa.

"Abba indai kaine ka haife ni nayi maka alqawarin zan yi duk abinda zanyi wajan ganin bayan Asad bama shi kad'ai ba dukka su ukun a hankali kowa zai k'are, ka bar komai a hannuna barewa baza tayi gudu d'an ta yayi rarrafe ba, zan baka mamaki Abba zan tabbatar maka da Jarumi ka haifa" yana fad'a ya fita daga falon ya ya bar mahaifin nasa a tsaye yana kallon sa.

Murmushin jin dad'i yayi jin abinda Suhail yace ko babu kowa hankalin sa ya kwanta kad'an. Sai a lokacin ya samu dama da kwanciyar hankalin fita daga gidan.

            A cikin gidan sarki kuwa Mama tana zaune a falon ta ita da k'awar ta kuma aminiyar ta mai suna Sadiya suna tattaunawa Mama tace, "Sadiya bana son wani tsaiko ko katanga da zata shiga tsakanin Asad da mulkin garin nan, in wani daga cikin yaran nan baiyi mulki a garin nan ba na shiga uku Sadiya."
"Baza ki shiga uku ba ranki ya dad'e, ai mulki ma kamar Asad yayi ya gama ne, in kika cire rashin son magana irin na Asad bashi da wani aibun da za'a hana shi mulki, to a tak'aice ma waye yake da qualities d'in da yake dasu kaf gidan nan da dangin mai martaban?."

Mama tace, "Babu, amma kin san akwai y'an taka haye, tsaf waziri da Sa'adatu zasu shiga su fita wajan ganin buri na bai cika ba, zasu iya ni na sani hatsabibai ne sune suka mayar min da Aliyu na haka, sune suka mayar da Hydar haka, Asad ma ya gagare su ne shiyasa suka kasa yi masa komai. In kika duba su galadima da sauran y'an uwan mai martaba basu damu da sarautar nan ba harkar gaban su kawai suke banda shi. Sadiya idan Asad baiyi mulkin nan ba zan iya mutuwa."

        "Baza ki mutu ba ranki ya dad'e sai kin d'auki jikan ki d'an sarki kuma jikan sarki shima kuma sarki, Muma ai ba zuba idanu zamuyi muna kallon su muna da namu hanyoyin da zamu bi wajan ganin mun b'arar da duk wani hatsabiban cin su." Numfashi ta sauke tace, "ni bana jin wannan Sadiya, duk wani jifa da zasu yo mana su sun san nima ba kanwar lasa bace, abinda yake gabana a yanzu bai wuce Asad, baya son mulkin nan ko kad'an balle ya mayar da hankali a kai, ki duba inda yana da hankali yana kuma son abin yadda ake maganar nan da yanzu bai nemi matar aure an yi biki an gama ba?."

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now