"Kai kad'ai ka cancanta Deaf, in ba kai ba duk wanda aka bawa mulkin nan komai sai ya lalace, kayi hak'uri domin ya zamar maka dole." Bai bashi amsa ba daman shima yasan iyakacin maganar da zai samu kenan hakan ya saka shi jan bakin sa yayi shiru kawai yana kallon sa.

       Yana son Asad sosai baya son ganin abinda zai cutar dashi kamar yadda shima yake son sa, yayi alqawarin taya shi yak'i da duk wani mak'iya da suka sako shi a gaba, zai taya shi nemawa kansa kariya a duk inda kariyar take. A haka suka k'arasa babban b'angaren su suka shiga daman sun san baza su samu Aliyu ba kowa ya wuce d'akin sa Hydar yana murmushi ya shiga nasa d'akin.
*☆☆☆*
         "Rauda! Zo ki bani kud'in ciniki na, rainin hankali ne ma irin naki kin san ban karb'i kud'ina ba ina ke ina bacci?" Baba ya fad'a da k'arfi a k'ofar d'akin su.

Rauda da bacci ya d'auke ta ta jiyo amon muryar sa ba jimawa ta mik'e tana laluben k'aramar touch light d'in Umma ta d'auko ta kunna tana haska inda zata ga kud'in. Muryar Umma taji tace, "Suna cikin kayan ki kinyi bacci kin barsu shiyasa na b'oye miki."
"Wai baza ki kawo min bane?!" Ya sake fad'a cikin d'aga murya yana d'aga laluben d'akin.

"D'auko maka nake Baba" ta fad'a cikin muryar bacci tana dube ghana must go na kayan ta ta d'auko kud'in a bak'ar leda ta mik'e ta kawo masa ya karb'a ya kwance yana lissfawa, kallon ta yayi yace, "babu naira hamsin tana ina?."
"Fad'uwa tayi Baba."
"Kinci uwar ki keda fad'uwar, kaji min yarinya ni zaki kalla kice kin naira hamsin ta fad'i? Ina laifin ma biyar ta fad'i sai ki yarda har hamsin?."

"Kayi hak'uri Baba wallahi ban sani ba sai bayan na dawo dana irga naga babu."
"Daman ai kin saba, rik'e min canji ba wannan ya zama sabon ki dan kinga ina k'yale ki. Y'ar uwar ki cif ta kawo min kud'ina amma ke da yake bakya son tallah uwar ki ma bata so shine ake rik'e min canji dan nace na daina d'ora miki, to baki isa ba talla yanzu kika fara kuma wallahi sai kin biya ni hamsin d'ina."

Yana fad'a ya saki labulen ya tafi nasa d'akin yana mita. Umma ta kalle ta tace, "ya akayi kika yar masa da kud'i?." Idanun Rauda suke ciko da hawaye tace, "Banyi da niya ba Umma ban san ta fad'i ba wallahi."
"Da safe cikin cinikin alawar madarar da kike yi ki d'auki hamsin ki bashi in b haka ba kin shiga uku."
"To Umma."
"Kwanta sai da safe" komawa tayi ta kwanta tana share hawayen ta. Ko kad'an bata son wannan dabi'ar ta Baba baya d'aga k'afa akan kud'i ko waye kai.

Kamar kullum da asuba duk ya tashe su kowa ya fito sallah bayan an idar aka jira ya shigo kowa ya gaishe shi sannan aka koma aka kwanta. K'arfe bakwai Rauda ta tashi ta tashi Khairi da Khalil suka fara shirin tafiya makaranta ita kuma ta fara gyare-gyaren gidan.
Bata gama aikin ba ta shiga ciki wajan Umman su tace, "Umma gasarar Koko ta k'are gashi su Khalil zasu tafi makaranta."

Umma ta mik'e zaune tace, "bai baku kud'in awarar bane?."
"Bai bayar ba." Umma ta mik'e tace, "to bara naje naji yadda zamuyi dashi." Ta fad'a tana fitowa shima a lokacin Baba ya fito daga d'aki.

Ganin tana nufo shi ya saka yace, "ban kwana da ko sisi ba kar kizo min da maganar kud'i." Umma ta karyar da wuya tace, "ba batun kud'i bane gasara ta k'are ne gashi baka bada kud'in awara ba ga y'an makaranta suna shiri basu ci komai ba."
"Ki tafasa musu ruwa hamsin d'in da nake bin Rauda ku siyo ganyen shayi da sikari su sha su tafi."
"Bak'in shayi Malam? Kar ka manta fa in suka tafi sai azahar ta yaya zasu gane karatu basu k'oshi ba?."
"Kar su gane mana wani ma ai bai sha bak'in shayin ba, tun yaushe nake cewa ki dinga tura su gidan sarki suna karb'o sadakar taliya baki tab'a ba. Ita y'ar uwar ki ai gashi yanzu sun dafa sun ci har sun tafi sun bar naki suna kale."

Umma tace, "yanzu malam kana da kud'in da zaka bamu muci baza ka bayar ba har sai munje karb'o sadaka har gidan sarki? Ka duba nisan dake tsakanin mu mana."
"Ita wacce taje bata san ciwon kanta ba kenan? Da asuba Rahma take tafiya amma ke y'ar ki y'ar gwal ce baza taje ba sai ku zauna haka ni kinga tafiya ta" ya fad'a yana ficewa ya bar Umma a tsaye.

Ummulkhairi ta taso tace, "Umma barshi ba sai munci komai ba ni zan iya dawowa haka in kina da wani abun ki bawa Khalil kawai." Girgiza kai tayi tace, "A'a Ummulkhairi muje ina da naira d'ari biyu ku siyo awara kuci ku tafi." D'aki ta shiga ta d'auko musu Khalil ya siyo musu awara suka ci suka tafi makaranta.

        Rauda bayan ta gama aikin gidan tayi wanka shiga wajan mahaifiyar tata ta same ta a zaune tayi tagumi tace, "Umma ki daina saka damuwa a ranki, indai batun abinci ne zan dinga zuwa ina karb'owa sai muje tare da Rahman mu dawo."
"A'a Rauda ban amince da fitar asuba d'in nan ba, ban kuma amince da ki nemo abinda zaki ci da kanki ba Allah bazai hanani abinda zan baku ba in ya hana mu. Kin san bana son rok'o ne ko yawan cewa a bani da y'an uwana duk wanda na tambaya sai ya bani, yanzu ma ina da shinkafa kwano guda da aka aiko min dashi har gida wanke ki dafa canjin awarar da suka kawo ki siyo mai na hamsin yaji na hamsin muci har dare." Da to ta amsa ta mik'e ta tayi abinda mahaifiyarta ta ta saka ta.

        Gab da azahar Baba ya dawo ya kwab'e babbar riga ya shiga aikin dafa d'an wake ya gama nan da nan ya kwashe ya lissafa na nawa ne ya zuba masu ya fara kwala musu kira, ita da Rahma suka fito ya kalle su yace, "to gashi nan na naira dubu biyu ne ko waccen ku, wallahi Allah biyar d'ina baza tayi ciwon kai ba." Komawa Rauda tayi ta d'auko hijjabin da tayi sallah ta d'auki abincin ta fita itama Rahma ta fita ba wacce tace kanzil.

Daga can inuwa ta hango motar Anas ta ja tsaki a zuciyar ta ta sake d'aure fuskar ta dan ma kar yaga fuskar da zai kulata, hango ta yayi ta tawo ya fito daga motar yana murmushi tazo zata gifta shi kenan ta jiyo amon sautin muryar Baba yana fad'in, "ki tabbatar sai kin biya ni hamsin d'ina ta jiya dan ba bar miki na yi ba!."

Runtse idanun ta tayi cikin takaicin dizgi irin na Baba ganin wanda yake tsaye ya saka Baba k'arasowa yana fad'in, "Anas yau kaine da rana haka?." Murmushi Anas yayi ya duk'a har k'asa ya gaida Baba ya amsa da fara'a yana fad'in, "Gashi mutuniyar zata tafi wajan sana'ar ta, kana jina da ita ko? Jiya ta yar min da hamsin shine nace sai ta biya ni shine duka ranta a b'ace."

Rauda kamar ta matse bakin Baba haka take ji amma babu dama ta d'aga k'afa zata bar wajan taji Anas yana cewa, "Baba har yanzu Rauda bata daina yawon siyar da abincin nan ba?."
"To ya za'ayi Anas dashi muka dogara ai."
"Bana son yawon Allah ya sani Baba, inda dama a siyar a gida in ya zama dole, in kuma akwai sana'ar da za'a canja a canja basai sun dinga fitowa ba."

Baba ya gyara tsayuwa yace, "Daman sana'ar keke napep d'in nake so to ance kud'i ne dashi tsububu shiyasa muka ganewa abincin."
"Babu damuwa Indai za'a daina bata abincin nan ta fita zan siya maka napep Baba."
"Kai amma nagode d'an albarka, wannan abu mai shegen kud'i za'a siya min? Wallahi na rasa ma me zance maka dan murna." Anas yace, "Babu komai ai Baba."
Baba yace, "talla ai daga yau ta daina zuwa yau d'in ma dan kar ayi asara ne" ya fad'a yana murmushi yana kallon sa.

Kallon Rauda yayi yace, "Rauda na nawa ne abincin?." Kafin ta bada amsa Baba yace, "Na dubu uku ne." Da sauri ta kalle shi shima ya kalle ta ya d'auke kai Anas ya zaro dubu biyar ya bawa Baba yace, "na siye na yau, dan Allah Baba a daina bata tallan nan bana so wallahi."

Hannun Baba har rawa yake ya karb'a yana zuba godiya Anas yace, "Babu komai Baba, zanyi tafiya yau bazan jima ba zan dawo dana dawo za'a kawo maka napep d'in in sha Allah, amma dan Allah a hak'ura da tallan nan dan Allah badan ni ba."
"Ai an gama Anas baza a kuma ba in Allah ya yadda."
"Na gode Baba."

Baba ya kalle ta yace, "bani kular na shiga ciki ku gaisa" ya fad'a yana karb'a ya wuce ya tafi gida ita kuwa ji take takaici kamar ya shek'e ta. Kallon ta Anas yayi yace, "kiyi hak'uri nasan na takura miki Rauda, Ina son ki ne da zuciya d'aya kuma auren ki zanyi." Bata ce komai ba ya kuma cewa, "Dan Allah kice wani abu mana Rauda."
"Me zance to? Na fad'a maka ni ba aure zanyi ba ka fita daga rayuwata ka nemi dai-dai kai amma kak'i."
"Kece dai-dai Rauda ko shekara nawa zakiyi nan gaba zan jira ki har ki shirya yin auren, Ina son ki Allah ya sani."

Bata ce komai ba yace, "ki bani number wayar ki zanyi tafiya ina so muryar ki ta dinga debe min kewa."
"Bani da waya, na gode da abinda ka bawa mahaifina Allah ya saka alkhairi, sai anjima" ta fad'a zata wuce yayi saurin cewa, "Dan girman Allah ki tsaya." Ba musu ta tsaya ya ya bud'e mota ya d'auko farar envelop ya mik'o mata yace, "ki karb'i wannan kya sha ruwa."
Kallon sa tayi ta kalli takardar tace, "na gode."
"Dan Allah ki karb'a."
"Kayi hak'uri bazan iya ba."

"Da hannu a jikin ki kice baza ki iya karb'a ba?, Rauda meyasa kike.mayar da hannun kyauta baya bayan kin san babu kyau hakan?!" Baba ya fad'a yana k'arasowa wajan yana kallon ta.

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now