Page 7

34 2 0
                                    

Shiru tayi bata ce komi ba, maida hankalinsa yayi akan tuƙin da yake, ba wanda ya ƙara cewa da ɗan uwansa komai a haka har ya isa gida, yana zuwa ƙofar gidansu yayi horn, kafin Get Man yazo ya buɗe masa Get ya buɗe mata ƙofa ta fita, "Kayi haƙuri" ta faɗa bata jira amsar sa ba ta fara tafiya, bin bayanta yayi da kallo tare da sauke wata irin nannnauyar ajiyar zuciya, yana ganin ta shiga gida ya tada motar ya shiga cikin gidan.
   Yana parking motarsa Direct Part ɗin mahaifiyar sa yayi, don shi bayyi tsammani Secretariat ɗin sa ta cewa baƙin nan su jira shi ba, yana shiga da sallama a bakinsa, ganin mahaifiyar Ruƙayya zaune fuskar Ummi kuma ba fara'a yasha jinin jikinsa akwai maganar da suke, cike da girmamawa ya gaishe da ita, "Umma ashe kina nan Ruƙayyah ta dawo"
  Mahaifiyar Ruƙayya tace "Nima yanzu zan tafi ba daɗewa zanyi ba"
  "A ina kaga Ruƙayya ɗin?" Ummi ta tambaye sa.
Dakewa yayi yace "A school ɗin su ba ganta, shine na ce tazo muje Nima gida zani"
  Ɗan taɓe baki tayi tace "Maman Ruƙayya tacemin a satin nan zasu tafi, zasu koma Lagos da zama, Baban Ruƙayya ya buƙaci haka"
   "Ummi amma ai naga Exams take zanawa" Jameel ya faɗa cikin tashin hankali wanda bazasu iya gane halin da yake ciki ba.
   Mahaifiyar Ruƙayya ce tace "Eh nasani Jameel a satin nan ai zasu gama"
"Result ɗin ta fa" ya faɗa yana furzar da wata iska.
Ummi ce ta karɓi zancan tace "Babanta ze dawo in lokacin fitowar sa yayi"
  Rausayar da kanshi yayi jiki ba ƙwari ya tashi ya nufa Bedroom ɗin mahaifiyar sa, abunda be taɓa yi ba tunda ya girma ya mallaki hankalinsa.
  "Jameel!" Mahaifiyar sa ta kira sunansa da mamakin ganin ya nufa Bedroom ɗin ta.
"Umma in kin sallameta ina jiranki zamuyi magana ne"
   Be jira amsar ta ba ya buɗe ƙofa ya shiga, ya samu Stool ya zauna.
   Tunda ya shiga Mahaifiyar sa ta kasa samun sukuni dan ta hango damuwa a ƙwayar idon ɗan nata, "Bari naje kar Ruƙayya taimin ɓarna taga bana nan" numfasawa Ummi tayi tace "Idan Alhaji ya dawo zan shigo gidan in sha Allahu, ki gaida gida"
Amsawa tayi itama haɗe da yi mata sallama.
   Ganin ta fita yasa ta doshi hanyar shiga Bedroom ɗin ta don hankalinta nakan shi, da sallama ta shiga yayinda taga Jameel ya ƙurawa waje ɗaya ido yana tunanin wani abu, jin motsinta yasa saurin tashi daga zaune da yake, "Ummi ta tafi?" Ya faɗa yana kallan ƙofa.
Ummi kallan ɗan nata tayi se yanzu ma ta lura da ya ɗan rame, "Jameel meke damunka?"
  Kamo hannunta yayi ta zauna kan Bed yayinda shi kuma ya zauna kan Bedside Drawer "Jameel ka faɗamin abinda ke damunka man, kaifa  ba yaro bane, banaso ina ganin ka cikin damuwa"
  Lumshe ido yayi ya sauke kanta, "Ummi Don Allah kar ki bari su tafi da Ruƙayya"
Tsayawa tayi tana kallanshi tace "Saboda me?"
"Ummi wallahi ina son ta...."
Shiru yayi ya kasa ƙara sawa dan shi be ɗauka maganar tashi a fili yake yin ta ba.
"Kana son ta?" Ta tambayesa da mamaki, shiru yayi bai ƙara ce mata uffan ba "Tun yaushe ka fara son nata?" Ta tambayesa.
   "Ummi wallahi ban sani ba Nima" ya faɗa muryarsa na Cracking.
"Uhmm, amma kasan an mata miji ko?, Mai yasa baka faɗamin tun da wuri ba se yanzu da lokaci ya ƙure?"
"Ummi lokaci be ƙure ba don Allah ki taimaka min, bana jin zan iya aurar wata mace in ba ita ba, wallahi Ummi bansan ina son ta ba se da naga tana ƙoƙarin kuɓucewa rayuwa ta, kuma wanda aka bata bata sonshi ta Faɗamin"
"Ita Ruƙayyah ce ta faɗa maka haka?, Tasan kana son ta?"
"Uhmmmmmmmm" kawai tace don ya fara gajiya da maganar.
  Miƙewa yayi ya kalli mahaifiyar sa yace "Please Ummi do something"
  Fita yayi ya ciro wayarsa ganin tarin Missed calls yayita mamakin tayaya akaita kiransa be ji ƙara ba, yana duba missed calls ɗin yaga tarin kiran Secretariat ɗin sa ce, tsaki ya ɗan ja ya kira ta.
"Hello Sir!" Cewar Secretariat ɗin.
"Uhm, ina jinki"
"Sir baƙin ka nata jiranka"
Dafe Head ɗin sa yayi "Kina nufin wai suna nan har yanzu?"
"Yes Sir, nace baza ka daɗe ba"
  "Okay I'm Coming" ya faɗa ya kashe wayar, part ɗin sa ya wuce yana so ya watsa ruwa.
  A hankali yake tafiyarsa maganganun Ruƙayya ke masa yawo a zuciya, murɗa Handle ɗin ƙofarsa yayi ya shiga, don yanaso yayi wanka ya koma Office.

     Tayi tsaki babu adadi a cikin gidan, zama tayi tai jugum tana tunanin Ya Jameel ganin yadda taga ɓacin rai a fuskarsa, "Kinci Abinci?" Mahaifiyarta ta tambaye ta, numfasawa tayi tace "Umma ina kikaje?"
Na leƙa gidan Umminki ne na faɗa mata tafiyarmu, gyaɗa kai kawai tayi, ta tashi ta ɗauko abincinta, cokali ta saka tana ta jujjuyawa ta kasa cin abinci, "Umma Kinga Ya Jameel?"
Mahaifiyar ta kallanta tayi tace "A'a ba shi ya dawo dake daga makaranta ba"
Ɗaga mata kai kawai tayi tai spoon biyu tace "Umma bari naje gun Ummi....."
  Mamanta dakatar da ita tayi tace "Kinsan dai Babanki bayaso kina fita, kuma ko wani lokaci zai iya dawowa"
Ajiyar zuciya Ruƙayya ta sauke tace "Umma wallahi yanzun nan zan dawo" miƙewa tayi ta janyo gyalenta dake kan igiya ta fita.
  
    Ummi tunda ya fita ta kasa sukuni ta kasa yadda cewar Jameel da gaske yake faɗa mata yanason Ruƙayya, Tayaya tasan Jameel zece yanason Ruƙayya bayan duk Matan da suke Bibiyar sa yaran masu kuɗi da sarauta, Jameel Miskili ne na gaske tasan tabbas suna shiri da Ruƙayya amma kwana 2 ko kaɗan taga bata ganin su inuwa ɗaya, Jameel jinin Fulani da Shuwa Arab ne tayaya ze iya soyayya da jinin mahauta wacca mahaifin ta ba kowan ko wa bane, Jameel yafi Ruƙayya kyau, asali, kuɗi da duk wani abu na rayuwa, duk wanda ze ga Ruƙayya da Jameel yasan ko kaɗan basu dace da juna ba.
Numfasawa tayi tana tunanin Liyana yaya zatai da ita, yaya zatai da Iyayan Liyana, tabbas Liyana taji wannan labarin sunan Ruƙayya Sorry.
Miƙewa tayi ta tsaya jikin window tana hango bishiyoyin da ke kaɗawa, ɗaga kanta tayi ta hango Ruƙayya na shigowa, batasan lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba, ganin Ruƙayya na kallan wani wurin ne yasata duba inda take kalla, Jameel ta hango ya fito daga ɗaki ya riƙe Handle ɗin ƙofarsa, ganin irin kallan da ya watsawa Ruƙayya ne abun ya ɗan bata mamaki.
    Ruƙayyah sadda kanta ƙasa tayi tana wasa da yatsun hannunta, a hankali ta kara ɗago da idanunta suka sauka kan nashi taga yayi sauri ya koma ɗakinsa ya rufe.
   Jameel jingina yayi a jikin ƙofarsa yana mai da numfashi a hankali, murmushi kawai yayi ganin irin kallan da Ruƙayya take mishi hakan ya tabbatar masa da cewar ta kasa sukuni kan abinda ta faɗa masa.
   Kallan Part ɗin Ummi tayi sannan ta kalli na Jameel cikin sanyin jiki ta doshi hanyar part ɗin Jameel, ta daɗe a ƙofar ɗakin ta kasa Knocking domin tana fargabar shiga, a hankali ta murɗa ƙofar se ta jita a buɗe shiga tayi ta zauna akan 3 seaters ɗin dake Parlourn, ta daɗe a cikin Parlourn amma bataji motsinsa ba, har zaman ya fara gundurarta, tashi tayi ta na ƙoƙarin fita se taji motsi, a ɗan firgice ta kalli ƙofar Bedroom ɗin, ganin ya fito daga shi se gajeren wando ga Towel saman kansa ya sa ta ɗan daburce, tana ƙoƙarin fita, don tunda take dashi bata taɓa ganinsa a haka ba, sosai ta razana batasan lokacin data yar da Cup ɗin dake ajiye kan Stool ba, still bata waigo taga me ya faɗi ba ta fara kicinniyar buɗe ƙofa, "Wait" taji ya faɗa, runtse ido tayi gabanta na faɗuwa, tsayawa tayi ta kasa juyowa, "Me kikemin a ɗaki?" Ya jefo mata tambaya, cikin Muryar Cracking tace "Na..na zo ne..."
Ya katse ta da cewar "Kinzo me?"
Dakewa tayi tace "Ba komi" ganin zata fita yasashi bata umarnin karta buɗe ƙofar, Ruƙayya ji tayi kamar ta saki fitsari a gun, "Zo nan" yace mata "Don Allah Yaya Jameel...." Maganarta tsayawa tayi cak jin ƙamshin sabulun wankansa kusa da ita, ji tayi numfashinta na barazanar ɗauke wa, Cikin Whisper Voice yace "Me kikazo yi ɗaki na?"
  "Yaya don Allah kayi hakuri wallahi haƙuri nazo baka, bari naje waje zan jira ka"
"Ruƙayyah!" Ya kira sunanta, wani iri taji ta kasa juyawa ta fuskanceshi, "Innalillahi wa inna ilayyir raju'un " ta faɗa cikin tashin hankali, sauri tayi ta matsa daga wajanshi hawaye na son sauka daga idanunta "Don Allah ka barni na fita" ta faɗa tana kallon ƙwayar idanunsa.
  Ummi tun tana jiran fitowar Ruƙayya har ta gaji tana mamakin daɗewar ta a ɗakin, don tasan tabbas Jameel yana da matuƙar kamun kai da zuciyar ta ta raɗa mata wani abun, sede ganin yadda ta aminta da tarbiyyar Ruƙayya data nata ɗan yasata numfasawa, tana zaune kan kujera a balcony ɗinta tana jiran fitowar ta amma ta ji shiru, nan zuciyarta ta ɗan fara raya mata abubuwa da dama, kamar wacca aka zabura ta miƙe ta nufi part ɗin Jameel.
   Hawaye ne masu zafi suka sauka kan kuncinta, tama rasa me zata faɗawa Jameel ya fahimceta, tsayawa tayi tana kallansa ganin ya matso gabda ita, kamar wani ɗan ƙwaya haka yake mata magana "Me ya kawo ki dakin nan?"
"Kayi hakuri Bazan kuma  shigowa ba"
Kallan lips ɗin ta yayi a hankali ya fara ƙoƙarin haɗa bakinsu guri guda, runtse ido tayi domin tabbas ba yadda zatai da Jameel don tasan ko ihu tayi babu me jiyota da ma Fahad yana nan ne ze iya jin duk wani ihu da zatai, jin bakinsa cikin nata yasa tsigar jikinta tashi gabanta na faɗuwa, kallanta yayi da lumshashshun idanunsa ta runtse ido ba abinda ke sauka daga cikin idanunta se ruwan Hawaye, jin kamar tafiyar mutum yasa ta turashi baya tana ƙoƙarin buɗe ƙofar, tana buɗe wa suka haɗa ido da Ummi, gaban Ruƙayya ne yayi mummunan faɗuwa, yayinda Ummi ta bita da kallan tuhuma, shigowa cikin ɗakin tayi tana kallansu, Jameel zaune kan kujera ya dafe kanshi idanunsa a rufe.
  Sosai Ummi take ƙare musu kallo, Ruƙayya ta sadda kanta ƙasa still hawaye na zuba a fuskanta.
"Jameel me kai mata?, Ruƙayyah..."
Ruƙayyah sauri tayi ta rungume Ummi jikinta na rawa "Ummi..." Kasa furta komi tayi ta fashe da kuka.
  Jameel yana zaune be ɗago ya kallesu ba, duk abinda ke faruwa yana jinsu.
   Ummi wurgawa Jameel harara take Tamkar idanunta zasu faɗo ƙasa, bubbuga bayanta tayi ta ja hannunta suka fito daga ɗakin, duk da Ummi ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, ta rasa dalilin kukan Ruƙayyah, Liyana tana zaune a Parlor tasa ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kallo, ganin Ruƙayya da Ummi yasa ta saki baki tana kallansu, direct Bedroom suka shiga ta zaunar da ita kan Bed, ƙirjin Ummi kamar ya fado ƙasa saboda tsoro da fargaba, "Ruƙayya ki natsu ki Faɗamin, me Jameel yayi Miki, ki kalleni dakyau kika sake kikaimin ƙarya wallahi Sena samu mahaifinki na faɗa masa.
   Jikin Ruƙayya ba ƙaramin rawa yake ba, ji tayi ta shiga wani irin tashin hankali wanda bata taɓa shigansa ba tunda take a rayuwa ta.

*#Comments*
*#Shares*
*#Votes*
*#Likes*

TSAKANIN MUWhere stories live. Discover now