Page 4

9 2 0
                                    

Murmushi tayi wanda kumatunta lotsawa, lumshe idanuwa tayi ta kifa kanta kamar mejin bacci,bata ƙara ce masa uffan ba, domin tasan zolayarta yake yi ina ita ina Ya Jameel, wane ita tasan yafi ƙarfinta kawai jikinta na bata so yake yayi amfani da yarintarta ya ɓata mata rayuwa.
   Tada motar yayi ganin bata ce masa uffan ba yana tuƙi a hankali yayinda yaji wata irin annashuwa ta natsuwa ta saukar masa a zuciya, ganin sun tsaya Chicken Republic yayi parking, "Ina zuwa" yace sannan ya doshi ƙofar shop ɗin, a hankali ta ɗago da fuskarta tana kallan bayansa, komi nashi daban yake, yana abu cikin natsuwa, tabbas tasan Jameel namiji ne inta tuna da wasu halayensa takanji tsanarsa cikin zuciyarta, sauri tayi ta kauda kanta gefe ganin ya tsaya da wata kyakkyawar mace son kowa wanda ya rasa, ko a jikinta ganin yarinyar na ƙoƙarin hugging ɗin sa ne ta kauda kanta gefe tana wasa da yatsun hannunta, _"Ko mata nawa yake wa haka Oho"_ ta faɗa a cikin zuciyarta.
    Jameel ganin Farha na ƙoƙarin hugging ɗin sa a Titi ya ɗan yi sauri ya matsa yana wurga mata harara, kallan inda Ruƙayyah take yaga ko kaɗan hankalinta baya kansu, ƙara juyawa yayi yana kallan Farha cikin faɗa-faɗa yana faɗin "Farha yaushe zaki zama mace me kamun kai ne?, A Titi zaki yunkurin hugging ɗina saboda baki da hankali" ya ƙarshe faɗa yana ƙarewa kayan jikinta kallo tamkar ba ƴar Hausawa ba.
   Jingina tayi da jikin motar ta tana turo baki gaba tana faɗin "Na kiraka 4 missed calls baka ɗauki waya na ba, me yasa?"
   "Kawai" amsar daya faɗa mata.
  Murmushi tayi saboda tasan halin gogon nata, "Kallanshi tayi hawaye na ƙoƙarin gangarowa daga fuskarta.
Waige-waige Jameel ya fara kamar mara gaskiya tamkar me raɗa yace "Maye haka Farha a Titi muke fa"
   Bata damu da hakan ba tace "Se yaushe Jameel zaka gane niɗin me ƙaunar ka ce, se yaushe zaka daina azabtar da zuciyata akanka,don Allah" ta faɗa tana haɗa hannayanta waje guda.
"Shhhh" ya faɗa yana sa hannunsa akan bakinsa,"Zan kiraki"
  Ya faɗa yana ƙoƙarin barin gurin jin ta kamo hannunsa ne yaji ransa na ƙoƙarin ɓaci, nace "Zan kiraki....."
Idanunsa ne ya sauka akan Ruƙayya da sauri ya zame hannunsa cikin na Farha haka kawai ya tsinci kansa da faɗuwar gaba.
  "Jameel!"
Farha tace da ɗan ƙarfin, ko da wasa be ƙara waigo inda take ba ya shigo cikin motar, kayan da ya siyo ya miƙa mata zuciyarsa na harbawa da ƙarfi da ƙarfi.
  "Ya Jameel wace waccar take kiranka"
   Jameel kallan Ruƙayyah yayi yana mamakin ta ganin ko kaɗan ganin datai musu be dame ta ba, hakan yasa yaji babu daɗin cikin ransa,wato shi kaɗai yake kiɗarsa yake rawarsa akan ta.
  Haɗe rai yayi tamkar be magana yayi banza da ita, ganin haka yasa ta ɗan ɗaga kafaɗa irin she don't care ɗin nan.
   Yana parking motarsa ta fito ganin tabar masa kayan daya siyo mata cikin motar yasa yace "Wannan kayan wa ze kwashe Miki su?" Ya faɗa ba fara'a a fuskarsa, cikin sauri da sassarfa yasa ta ɗauko bakinta na rawa tace "Na gode" tai maza ta shiga gida.

  Da sallama ta shiga ihu ta saki ta yar da ledar dake hannunta ta haye jikinsa tana murna "Oyoyooooooo Babana " ta faɗa tana dariyar jin dadi, ganin zata kada shi yasa mahaifiyar ta cewa "To sakeshi kar ki yada shi"
   Sakin shi tayi ta faɗa ɗakinta da gudu tana ƙoƙarin cire Uniform ɗin dake jikinta.
     Mamanta ne ta shigo hannunta ruƙe da ledar data shigo da ita tace "Ungo kin yadda kaya"
Karɓa tayi tace "Au ai Ya Jameel ne ya siyamin" ta karɓa tana ƙoƙarin buɗe ledar taga menene a ciki, chocolate ne dasu biscuits a ciki da yawa, murmushi ta saki...

Mamanta ne ta katse mata tunani tace "A ina kika ga Jameel ɗin?"
  Ɗazu ai shi ya kaini kuma da aka taso ze wuce yaga ina tafiya yace na shigo ya kawo ni gida, shine ya biya dani ta wani shop ya siyamin"
Ta faɗa tana ƙoƙarin ɓare ɗaya daga cikin chocolate din daya siya mata.
   Mahaifiyarta ƙoƙarin fita tayi daga ɗakin, Ruƙayya tace "Mamanmu Kinga wata budurwar sa kuwa wallahi Mama kamar aljana saboda kyau, kyakkyawan gaske" ta ƙarashe faɗa tana murmushi domin ita kanta Farha kyanta ya tafi da ita inaga Jameel.
   Girgiza kai tayi batace mata uffan ba ta fita daga ɗakin.
    Maroon ɗin doguwar riga ta saka haɗe da mayafinta ta fito tsakar gida ta zauna akan tabarmar da mahaifinta yake zaune, "Baba ya Lagos?" Ta faɗa tana washe baki.
  "Lagos Alhamdulillah ƴar Baba, naga kin ɗan ramemin ne..."
Mahaifiyarta ce ta katse shi da cewa "Ruƙayya a kwanakin nan wallahi damuwa ta sakawa ranta, kamar Ruƙayyah ace tasan menene damuwa, dudu Ruƙayya guda nawa take"
   Mahaifinta hankalinsa kacokan ya maidashi kanta yace "Ruƙayyah meke damunki?, Akwai wani abu da kike ɓoyewa iyayanki ne bamu sani ba?"
   Girgiza kai tayi tace "Baba lokacin zamu fara test ne shine hankalina na maidashi ga test ɗin da zamuyi, kasan jarabawar ƙarshen fita daga aji uku zamuyi in ban maida hankali ba zan fadi"
  Ta faɗa tana ƙoƙarin tabbatar musu da maganar datake faɗa musu, domin bazata iya fadan zahirin abinda ke damunta ba, bazata iya fallasa abinda ke *Tsakaninsu* da Ya Jameel ba.

TSAKANIN MUWhere stories live. Discover now