Page 6

15 2 0
                                    

Runtse idanuwa tayi ta buɗe a hankali tamkar wacca taga mugun abu, ganin hankalinsa baya kanta yasa ta fara tafiya a hankali, tana zuwa saitin ƙofar gidansu Jameel ta sadda kanta ƙasa tace "Ya Jameel ina kwana?" Bata jira amsarsa ba ta cigaba da tafiya.
"Ruƙayya!" Taji ya kira sunanta tsayawa tayi ta ɗan waigo tana kallansa, inka ganshi bazaka taɓa cewa shi ya kirata ba, don hankalinsa nakan wayar dake hannunsa, rausayar da kanta tayi tare da juya idanunta sama, ganin still be kalli inda take ba yasata taɓe baki kamar wacca zatai kuka tace "Ya Jameel ka kirani kuma kai banza dani"
"Ki jirani bari na kaiki" yana gama faɗan haka ya buɗe ƙofar gidan ya shiga, bayansa tabi da harara tace "Se kace nace ya kaini, se wani shan ƙamshi yake ma mutum...."
Bata ƙara sa faɗar maganarta ba taga Get Man ya wage masa Get ɗin gidan, parking yayi a gaban ta baice mata komi ba, kama Handle ɗin motar tayi ta buɗe ta shiga, "Ya Jameel ina kwana" ta ƙara gaishesa a karo na biyu.
   "Lafiya kalau, yau ya na ganki ke kaɗai ina Baban?"
Ya jefo mata tambaya.
Shiru tayi tana tunani tayaya yasan shi yake kaita alhalin basa ganin shi a anguwar lokacin da ze kaita School.
  "Ruƙayyatu!"
"Na'am" ta faɗa tana Confusing ɗin sunan.
  "Baba ya tafi ne?"
"A'a, yana nan" ta faɗa tana ɗan satar kallansa.
Be ƙara ce mata komai ba, a haka har suka ƙara sa makarantar.
Ƙoƙarin fitowa ta fara ya katse ta da cewa "Ƙarfe nawa zaku tashi?, Ko Baba zezo ya ɗauke ki?"
"Girgiza kai tayi tace "Ya tafi ƙauye maybe da yamma ze dawo".
"Okay ƙarfe nawa zaku tashi?"
Ƙara kallanshi tayi tanaso ta ga full face ɗin sa amma yaƙi barin su haɗa idanu.
"Ƙarfe 9 zamu shiga Exams kuma yau Paper ɗaya zamuyi da zarar na fito kawai zan dawo gida" ji tayi ba daɗi, ganin yadda yake mata magana kamar wanda akaiwa dole ya kawota.
"Okay 11:00AM zanzo na maidaki gida"
Gyaɗa kanta tayi jiki a sanyaye tace masa "To shikenan, Nagode"
Satar kallanta yayi kaɗan ya kauda kansa gefe.
  Tana sauka yaja motar ya fita daga harabar makarantar.

  Ganin da sauran lokaci yasata ƙara sawa Senior Section don ta samu tayi karatu a tsanake, samu tayi ta zauna gabda wani Class da ba'a komai dashi don ya ɗan samu matsala hakan yasa ba'a karatu a cikin.
   Haka kawai ta tsinci kanta da annashuwa cike da farin ciki ta ciro book ɗin ta ta fara karantawa, bini-bini ta saki murmushi.
  Shiru tayi jin motsi a bayan Class ɗin, jin kamar iska ce yasata ƙara maida hankali wajan karatun.
    "Tsaya mana!"
Taji Muryar Uncle Sufyan ta bayan, murmushi tayi jin Muryar sa don tana da tabbacin gunta ya zo.
   "Kaga an fara taruwa" jin Muryar mace ta ƙarajin a inda taji sautin muryar Uncle Sufyan, gabanta ne yayi mummunan faɗuwa, ta aje Notebook ɗin a hankali ta fara bin inda take jiyo sound ɗin wannan budurwar.
  Cak ta tsaya ganin Uncle Sufyan yana ƙoƙarin Kissing ɗin wannan ɗalibar, gashi ko kaɗan basa jituwa da *Alanta* sunan da Class Mate ɗin ta suka saka mata, yarinya ce mara kamun kai, duk wani malami da aka ga yana tarayya da ita to wannan malamin daga ranar ya tashi daga mutumin kirki ya koma na banza, bata yadda Uncle Sufyan bane, ta kasa yadda cewar shine yazo bayan Class yake ƙoƙarin Lalata da Students ɗin sa, yaushe ya zama haka, ko dama halin sa ne haka bata sani ba, wani saliva ta haɗiye me zafin gaske daga maƙogwaronta, a hankali ta dafa bangon dake kusa da ita tanaji kamar zata faɗi, tana kallan ikon Allah, ta runtse ido ba adadi tana so ta tabbatar wa da kanta mafarki take, runtse idanu tayi batasan lokacin data saki wata ƙaramar ƙara ba ganin yadda suke ƙoƙarin haɗe bakinsu waje guda, a ɗan firgice Uncle Sufyan ya tura Alanta gabansa na faɗuwa, buɗe idanuwanta tayi yayinda siraran hawaye suka biyo baya ta ɗaga kai tana kallanshi, dafe kanshi yayi yana faɗin "Please Ruƙayya ki fahimce ni......" Hannu ta ɗaga mai alamun ya dakata tai sauri tabar wajan, tafiya take amma ita kanta bata ganin hanyar da zata bi kasancewar idanunta sun ciko da ruwan Hawaye, can cikin makarantar ta kutsa in da bakajin motsin komai se kukan tsintsiye, ƙasan Bishiya ta samu ta zauna ta dafe kanta jin yadda yake sara mata, kifa kanta tayi a tsakiyan cinyoyin ta, wani irin kuka ne ya ƙwace mata, ba abinda kakeji face sautin kukanta.

     Akai-akai yake duba agogon dake ɗaure jikin hannunsa yana duba lokaci, hankalinsa gabaki ɗaya yana kanta don yana da tabbacin sun gama Exams, fitowa yayi daga Office ɗin sa yana ƙoƙarin fita, ganin Secretariat ɗin sa ta shigo ya dakata da fitar da zayyi, cike da girmamawa tace "Sir kayi baƙi"
  Furzar da iskar dake bakinsa yayi yace "Kije kice na fita"
   Ya faɗa yana ƙoƙarin bin wata ƙofar ta daban, ganin bakin nasu suna da mahimmanci yasa ta ɗan ɗaga murya ganin ze fita tace "But Sir....." Shiru tayi ganin ya ɗaga mata hannun ya fice.
  Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin ta ina zata fara da baƙin, domin tabbas ta tabbatar musu da yana cikin Office,
   Jiki ba ƙwari ta fita taje ta samesu tayi musu bayani akan ya fita amma ba ze dade ba ze dawo.

TSAKANIN MUWhere stories live. Discover now