“Don't touch me”

Tana isowa ya dakatar da ita, ta fi kowa sanin idan ya ce kar ta aikata abu he meant it tana aikatawa za su samu matsala.

“I miss you Ameer”

“Waye ya fita da mota yanzu?”

Ya wani yi kamar bata fahimce ba, sai kuma ta yi dariya tana kokarin yi masa wasa da hankali.

“Oh... Kawata ce Nanita”

“Really? Kina tunanin ni wawa ne?”

Ta mika hannu zata fara yaudararsa da kalamanta, ya daka mata tsawa.

“Na ce karki taba ni, kin fi kowa sanin abun da nake kyama shi ne sharing, and because of that na ware miki komai, na dauke miki komai ashe bayan idona kina iya cin amanata?”

“Nono karka je da nisa Ameer wannan fa kawata ce ta kwana nan ne, yanzu nan ta fita kai kasan ba zan iya cin amanarka ba God Forbid ni zan aikata haka ba, yanzu dai shigo ciki mu yi magana”

Harara ya watsa mata tun daga saman kanta har kasa, sannan ya kara ja baya.

“Kin yi sa'a ina jin kyamarki a yanzu, idan ba haka ba, Wallahi sai na kusa kasheki a gurin nan, but matsalar ba zan iya taba ki da hannuna ba ne, ki hada duk wani abu da kika san naki ne ki bar gidan nan we done”

Ko bahaushiyace ba zata yarda ta rasa wannan gatan na Ameer ba balle kuma inyamura da suka fi kowa sanin zafin neman kudi, zubewa ta yi kasa ta fara rikonsa tana dukan kanta da ke a haske kamar na maza, ko kadan be saurareta ba ya juya ya shige motarsa motar ma da take kokarin tarewa sai da yayi cikinta da ita, da bata yi hanzarin kaucewa ba kadeta zai yi yayi tafiyarsa. Bacin ransa ya karu he never thought Angel zata iya cin amanarsa a bayan idonsa kamar haka, duk da be tabbatar ba amman yasan ta aikata domin akwai alamun rashin gaskiya a tare da ita, idan ba haka ba wace kawace zata zo ta kwana a gidan ta fita a irin wannan time da da sasafe kamar an koreta? Kamin bata taba fada masa kawarta ta zo ko zata zo ba, and shi da idonsa Namiji ya gani a motar ba mace ce, duk kudin da yake kashe mata yana yi ne saboda ta tsare masa mutunta ta hana kowa kanta sai shi, a tunaninsa matan hausawa su da rikon amana kamar na kafirai wannan ya saka be taba gwada yi da ba haushiya ba, sai ita da yake bata ko wane kalar umarni ta bi ciki har da aske gashin kanta da tayi saboda shi, domin tsabtarsa bata tsaya iya ga tufafi ba har da gashi baya so more Especially na wasu matan da yake ganin attachment ne ba ainahin na su ba.

  Rasa gurin zuwa ya saka shi zuwa gurinsa ba a time da ya saba zuwa ba, ba dan ya saba lati ba, sam baya lati a zuwa aiki kuma no matter how yana shiga office yayi duk abun da yake aikinsa ne, sai dai ya wulakanta mutane yadda yake so ko ya kori wasu, wannan halinsa ne da kowa ya sani. Shiyasa suke taka tsantsan da bin dokokisa gudun kar ya jefa su a matsala yayi musu sallamar dole. Ba halinsa bane yin Sallama balle kuma amsa gaisuwa, hakan ya saka be kula masu aikin tsabtacen muhallin dake ta gaisheshi ba, har ya isa gurin kofarsa Office dinsa ya saka code bude kofar ta bude masa ya shiga ciki ya zauna, nan kadai gurin da be yi marmarin zuwa ba, musamman a yanzu da ya shigo cikin damuwa. kujerarsa ya nufa ya zauna ya runtse ido kujerar ta fara juyawa da shi tana tunanin yadda abubuwa suke masa zafi a yan kwanakin nan. Zaman baya masa dadi haka ya saka shi mikewa tsaye ya nufi fridge ya dauko gorar ruwa ya kai bakinsa, sai da ya sha rabinta sannan ya aje saman fridge din ya nufi Window ya bude fararen Curtains din da suke gurin ya tsaya gaban glass din yana hango kasan begen da mutanen dake kokarin shigowa masu aikin gyara harabar kuma na ta yi. Hannunsa daya ya saka aljihu sannan ya juyo ya nufi gurin Telephone din dake gefen teburinsa kira yayi sannan ya kara a kunne.

“Idan Faruk ya zo ina nemansa”

Shine abun da ya fada ya aje telephone din, ya sake zaunawa wannan karon kofar shigowar yake kallon. Faruk be shigo office din ba sai takwas da rabi, ciki tsoro da fargaba ya shigo sanin waye Ameer zai iya cewa ya masa laifi, domin tun kamin ya shigo office dina ka fada masa Ameer na nemansa kuma shigowar safiya yayi. Da katinsa yayi amfani ya bude kofar sannan ya shigo Office din dake dauke da kyamarorin tsaro, kamar yadda ko wane Office yake. Da ido Ameer ya fara tsare shi sannan ya mike tsaye ya dauki pen din dake gurin ya yagi diary ya rubuta masa numbers dinsa duka biyu ya mika masa, da kamar tsoro Faruk din ya karasa ya karba.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 15, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

WANI GARIWhere stories live. Discover now