“Mota...”

“Minene haka?”

“Wani karfe ne da suke hawa, mai tsananin gudu fiye da dabobinmu, kala kalar karfe ne wasu sun fi wasu tsada wasu kuma a sake suke wasu kanana ne wasu suna da kafa hudu wasu kuma uku wasu biyu, suna cin abincin da ba irin na ku ba, ko kadan rayuwar bata kama da ta mu”

“Ta ina ka sansu?”

“Saboda ni ina tsallakawa na bar garin Garuk na iya yarensu na ci irin abincinsu, na saka kalar tufafinsu na kwanta a irin muhallinsu na shiga abun hawansu, sai dai ke duk baki san wannan ba saboda baki taba leka wani garin ba, amman jama'ar garin nan da yawa sun san da wadannan abubuwan saboda suna fita, wasu kuma suna shigowa a garin neman sa'a ko nasara akan wasu abubuwan, akwai yan garin nan da aka kora suka koma can, akwai kuma wadanda suka tsalle garin nan suka auri mutanen can suna maida rayuwarsu a can”

“Hmmmm uhmm  a can ka koyo iya magana kenan?”

“Na koyo abubuwa da yawa daga garin, kuma na koyar da wadanda na aminta da su”

Ta rausayar da kai tana kallon wani katon tsauni mai tsananin tsawo, a take ta dauke hannunsa daga kafadarta ta nufi tsaunin da gudunta, daga inda yake tsaye ya daga muryarsa yana fadin.

“Suna da gidaje masu tsawo kamar tsaunin nan, wasu kuma ba su kai haka ba, wasu kuma sun dara, sai dai su ba a hawansu kamar yadda kike hawa”

“Ba su more rayuwa ba, wanda baya hawan tsaunuka yadda nake hawa be more rayuwa ba, wanda baya hawan itace be more rayuwa ba, ka fada musu duniyarsu bata kai ta mu dadi ba”

Tsayawa yayi yana kallonta cike da burgewa fuskarsa da murmushi, yadda take falfala gudu sai na rantse da Allah wani ya biyo ta ko yake kokarin kamata, sai dai ba ko daya tsananin kiriniya da iya hawan tsaunuka da tsananin gudu ya saka ta kware sosai, irin kwararwar da ace gasa ake ita ce zata zo ta daya, kamar ribi haka ta haye tsaunin har can sama ta mike tsaye tana kallon dajin da ba bakonta ba ne dajin dake cike da albarkar itatuwa da ciyayi ga kuma ruwa ta ko'ina, babu abun da take dai dariya ba tare da aman mata komai ba haka take a duk lokacin da take cikin nishadi.




AMEER  POV.

Sai da ya shiga dakinsa ya dauko dollars ya saka aljihunsa sannan ya dauki wayarsa da makullin mota ya fice. Babu abun da ke tashi a motar sai kidan disco ya kure volume kamar yadda ya kure gudu kai ka rantse da Allah shi kadai ne a titin Abuja, haka yake daman can be damu da rayuwar kowa ba sai tashi, gashi yana wasa da kudi kamar shi kadai ne dan mai nera a Abujar, ga uban girman kai gaisuwar tsiya ma bata hada shi da mutane balle ta arziki. Kai tsaye Q-town ya nufi wata mahada ce ta samari da yan mata, sai dai shi da abokansa ta su mahadar a VIP take wanda suke biyan kudin da ko shekara suka yi ba su zo gurin ba ma'aikatan gurin da mamallakinta be isa ya bawa wasu inzinin zama a gurin ba, yana faka motarsa sai da kowa dake gurin ya kalli motar domin ta banbanta da sauran motocin da suke guri, ba dan mahaifinsu ko kuma su ya fisu kudi ba, sai dan shi din ya fi su girman kai da ba zai iya hawan motar da suke hawa ba, haka kuma duk wata sabuwar mutane da ta shigo a garin Abuja yana cikin mayan matasan da suke fara hawanta, irin motocin da yake hawa daidaikun yayan manya zaka gani da ita a Abuja.

Sai da ya fito sannan ya rufe motar ya shiga cikin gurin, mutane dake harabar gurin hashakatawa sai kallonsa suke, wasu na masa kallon burgewa wasu kuma na masa kallon haushi saboda girman kansa da yadda yake jin isa, wasu yan mata kuma na kyasawa duk da kasancewar suna tare da samarinsu domin Ameer namiji ne cikakken namiji.
VIP ya shiga turare na masa escorting, daman shi da kamshi da tsabta kamar dan jumma da ďan jummai ne they're 5&6 duk inda yake tsabta da kamshi na gurin, haka ma duk inda tsabta da kamshi yake yana gurin. Zaratan samari uku ne suka dago kai suka kalleshi ban da Maleek da ya maida hankalinsa gurin wayar dake hannunsa kamar be san da shigowar Ameer ba, zamansu a tare ya zama kamar na dole tun ana karatun kasar waje har suka dawo a naija suka hada team dinsu na 5 buddies Ameer da Maleek basa ga maciji da juna, Sabida ra'ayinsu da tafiyar rayuwarsu da ta banbanta da ta juna, ko kadan Maleek baya son wani abun da ya shafi mata, sannan mutum ne da babu ruwansa da girman ko son wulakanta wani, tsabanin Ameer da wani lokacin yana kan taba mu'amala da mata, ga almubazzaranci da duniyar da aka sama masa ita tun kamin girmansa, sai dai ba sa iya rabuwa da shi shi ma kuma baya iya barinsu zama da junansu ya zama kamar dole, sauran samarin kam suna shiri da kowa kuma babu munafurci a tare da zamansu, sai dai ko wanne yana ji da kansa domin iyayensu suna da arzikin da za su dama su sha su watsar a yadda suke so a garin Abuja kuma a aka musu ido. Sai da ya zauna sannan shi ma ya kalli gurin da Maleek yake.

WANI GARIHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin