Part 2

334 22 4
                                    

Biki yayi biki, an raqashe anci an sha yammata sunyi rawa, Umaimah bata an kare da lokaci ba seda aka tashi ta kunna waya lokacin qarfe goma harda rabi tayi, daga gurin zuwa gidansu kuwa taci kusan Minti talatin a qiyasi dai sha daya ce zata kaita gida lallai kam yau ta taro Match me zafi dan tasan ma kafin taje tuni an kulle gida.

A motar Mijin Fannah suka tafi da yake hanyar su daya, ita bayin daren ne yafi daga mata hankali ba, Aa Abayar data saka da zata fito ta barota a gidan Maman Nana saboda bazata shiga jakarta ba kuma batayi zaton zasuyi dare har haka ba.

Cikin taraddadin abinda zata tarar suka sauketa a qofar gidan su, jiki a sabule ta sauka tana gyara yafen dan babban mayafin data samu sukayi musanye da Fannah ko ta dan qara rufe jikinta. A darare ta qarasa jikin qaramar qofar Get din da niyyar bugawa dan tasan dai an kulle se taji takun takalma a bayan ta.

A mugun zabure ta matsa, Abbane, da torchlight a hannunsa saboda an dauke wuta yayi mata kallo daya kafin ya saka muqulli ya bude gidan ya shiga ba tareda ya ce mata komai ba haka ta bishi zugui zugui a baya, ganin yayi kamar ma besan da wanzuwarta ba yasa ta kwasa da saurin gaske tayi ciki tana qara godewa Allah da ya saka babu hasken Nepa kuma be haska jikinta da fitilar hannunsa ba balle yaga irin shigar da tayi.

Dan dama daman da ta sake ji dayaga dawowarta ba ita kadai ba dan seda Fannah ta fito ta bude mata murfin motar da ya samu matsala, yanzu da ace saurayi ne ya ajiyeta a daren nan tana ga kawai tsirenta za suyi su huta.

Dakinsu ta fada tana sauke numfashi, bata tsaya ba seda ta tube kayan ta jefa can cikin wardrobe kafin tayi maza ta fada bandaki ta watsa ruwa tareda Alwala. Tayi mamakin ganin harta idar da sallah babu wanda ya biyo sahunta, amma tasan tarko ne. Tana jin yunwa haka nan ta haye gado ta kwanta, tunda dai ta shigo gidan zance ya qare duk wacce zaayi ayi da safe ai.

Washe gari ta kama Asabar, yanda taga babu wanda ko a fuska ya nuna mata tayi laifi jiyan ya fara daga mata hankali, tana so ta tafi gidan su Halima Daurin aure tana tsoron abinda tambayar hakan ze janyo mata.

Wuraren 11 tana zaune a dakinsu, tsoro take ta fita tsakar gidan su hadu da wani daga cikin Mama ko Abban ga Yunwar data kwana da ita ta hadu da ta safiya tana ta sakudarta. Nuratu Yayarta da take bima ta shiga dakin da farantin qosai da kofin da ta zubo kunun gyada ta nemi gefen gadonta ta zauna tana aikawa da Umaiman harara dan daman tun Asuba data farka ta ganta bata ce mata komai ba sedai idan sun hada ido ta maka mata harara kawai.

Ganin qosan da kunu ya qara wutar rura yunwar da take ji amma yanayin fuskar Yaya Nuratun yasa ta kasa ce mata zata ci, gashi babu motsin kowa a tsakar gidan qannensu duk sun tafi Tahfiz bare ta yafito wani ta saka ya debo mata. Ganinfa tana neman illata kanta dan damanita bame jumurin yubwa bace yasa ta yunqura da niyyar ta roqi yayar tata sega sallamar Qaninta.

Daga bakin qofar yace
" Yaya Umaimah kije inji Abba yana kiranki" ya juya abinsa. Seda cikinta ya bada wani qulululu, ashe ba kyaketa akayi ba jira suke gari ya gama wayewa tas ayi mata taron dangi dan taji shigowar Baba Abdullahi da Yaya Aminu babban Yayansu gidan.

"Yaya Nuratu dan Allah ki bani ko kunun ne nasha wallahi banajin zan iya tafiya ma yunwa nake ji" ta fada a marairaice dan gara ta karya bille ta roqeta, bata sani ba ko baa girka da ita ba kar taje garin diba ta qarayin wani laifin.

Banza Nuratun ta mata seda ta sake roqonta kafin ta turo mata kwanon qosan da kunun da ko rabi bata ci ba dan tana yi tana duba wani texbook nasu na yan medicine tace mata
"Gashinan Mayya se kici ai"

"Idan ni mayyace ke ma ai mayyar ce" Umaimah ta fada cikin qunquni ta ja kayan ta fara ci hannu baka hannu kwarya cikin dan lokaci ta cinye tas ta zura dogon Hijab har qasa ta fita tana nanata La'ilaha illah anta subhanaka innikuntu minazzalimin a zuciyarta harta isa qofar Sitting room din Abbansu.

HALIN KISHI (NADAMAR UMAIMAH)Where stories live. Discover now