Bayan kwana biyu suna zaune a dining room suna breakfast sai Alhaji Inuwa ya kalli agogo yaga karfe takwas saura minti takwas.

           Alhaji Inuwa ya zare ido cikin mamaki yace "Ummina lokacin makaranta yayi, tashi ki kira driver yazo ku tafi"

           Aisha cikin shagwaba tana sanye da uniform din makaranta tace "Gaskiya daddy yau kaine zaka kaini school"

           Alhaji Inuwa tace "Kinga fa kin kusa makara, ni kuma yau muna da meeting karfe takwas gara ki hakura drivernki ya kai ki kurum"

            Aisha cikin shagwaba tayi kamar zatayi kuka tace "Ni gaskiya kaine zaka kaini ko kuma in fasa zuwa inyi ta kuka" sai ta nannarke ta fara kuka.

            Alhaji Inuwa yace "Muje in kaiki karki soma yi mana kuka" sai su tashi su nufi kofar fita Aisha tana murna, sai da suka je daf da kofar fita ta dagowa Hajiya Sailuba hannu sannan su fice.

         Suna tafiya a mota Aisha tana tayi masa hira har suje bakin gate din makarantar sannan Aisha ta bude motar ta fita tana dagawa Alhaji Inuwa hannu har ta shige cikin makarantar da gudunta, shi kuma ya jinjina kai cikin shauki da kaunar 'yar tasa sannan yaja motar yayi gaba.

           
              WAYE ALHAJI INUWA ?

       Muhammadu Inuwa shine ainihin sunansa, dana ne a wajen Alaramma Malam Muhammadu Bello malamin soro ne mutum ne shi mai ilimin addini ne sosai, ya tsufa kuma ya tara 'ya'yaye da jikoki, matansa hudu 'ya'yansa talatin da takwas da tarin jikoki.

         Duk cikin 'ya'yansa babu wanda yayi ilimin boko mai zurfi kamar Alhaji Inuwa don har degree biyu gare shi wato masters, daga bisani kuma ya shiga harkar siyasa, Allah ya bashi sa'a yayi chairman din karamar hukumarsu ta Dala har kaso biyu tsawon shekara takwas kenan, ya rike mukamin sakataren gwamnatin jiha, kuma yayi dan majalisar jiha.

        Hajiya Sailuba matar Alhaji Inuwa 'yar uwarsa ce don da uwarta da uwarsa uwarsu daya ubansu daya a takaice dai auren zumunci suka yi tun bashi da komai har Allah ya azurtashi. Babban abinda yake ci musu tuwo a kwarya shine matsalar rashin haihuwa kuma sun ki zuwa asibiti a ga waye mai matsalar wai don kada wanda yake da matsalar yaji rashin jin dadi a ransa a haka suka zauna suka mika komai ga Allah, har a karshe Allah ya hadasu da Aisha.

CONTINUES TO STORY

        A can asibiti cikin dakin jinya Rahima tana kwance bisa gadon jinya na asibitin, Rahina da Rahila suna kusa da ita.

          Rahima ta juyo ta kalle su tace "Aunty kun ga abinda nake gaya muku ko yarinyar nan taki yarda dani a matsayin uwar data haifeta, dama kunga ai nayi tunanin haka ko su mutanen suki yarda ko ita 'yar!"

          Rahina cikin yanayin tausayawa tace "Komai nisan jifan kasa zai fado ai ba'a canjawa tuwo suna, in dai ke kika haifeta komai daren dadewa zata dawo gareki"

          Rahima ta girgiza kai tace "Kayya! abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, kin san ance juma'ar daza tai kyau tun daga laraba ake ganeta, Aisha ba zata yarda ba"

          Rahila ta girgiza kai yace "Ai naka sai naka Rahima, jini jini ne akwai wani sirri da Allah ya boye a tsakanin iyaye da 'ya'yaye"

      Kawai sai Alhaji Inuwa da Hajiya Sailuba su shigo tare da Aisha, su shiga da sallama.

         Rahima ta kalli bakin kofar inda taji sallamar, sai tagansu, Rahina da Rahila su amsa musu sallama, Aisha ta tafi da gudu ta rungume Rahima tana kuka.

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon