Allah ya amsa mata Adu'ar ta kuwa sbd banko kofar kyauren da aka yi tare da kamshi irin na turarukan da Yusuf ɗin ke anfani dasu da ya bule gidan ne ya shaida mata da shi ɗinne ya shigo, kwantar da Usman tayi tare da zubawa Aisha da ta taso da gudu ta dawo bayanta ta makale idanu, shi karan kanshi Usman ɗin dake kwance rawan jikin shi ya karu, zuwan Abbansu ba alkhairi bane gare su har ma ga mahaifiyarsu wani irin tsoro suke mishi da na tabbatar ko mala'ikan ɗaukan rai ne suka ji motsin shi se haka.

Tsab fuskar shi ya bayyana fari sol tsiririn bafulatani Sam bashi da ƙiba sede yana da kyau iya kyau kaman shi ya halicci kan shi, takowa yake yana kwaɓe fuska kaman wadda ke bin cikin kashi Dukda tsakar gidan banda shatin tsintsiya na shara ko tsinke babu, komai a kimtse yake a gyare cike da tsabta irin ta matar gidan, har ya karaso varender da suke ya ɗago ya watsa musu wata muguwar harara cike da neman magana.

Babu wadda ya iya ɗaga ido ya kalle shi a cikin su se yaran ne baki na rawa suka ce
"san...sannu da zuwa Abba"
Tsaki me karfi ya ja yace
"kuma sannun in da daaɗi... Ke Hidayat ke kin fi karfin marabtata ko in na dawo cikin gidan nan? Zaki gayamin zaman uban da kike in ba nawa ba da har zan shigo cikin gidan nan ki kasa ɗaga ido ki mini sannu da dawowa, To wallahi ubanki zan ci in baki kiyaye ni ba, wannan iskancin bazan ɗauka ba wallahi..."

Sababi ya ci gaba da yi ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, kaman wacce ta aikata wani babban laifi, kanta na ƙasa bata ɗago ba, ba se rashin bashi haƙurin ya kara ɓular da shi ba ya shiga zagin ta zagin cin mutunci ba ita kaɗai ba har da iyayenta da zuri'arta gabaɗaya, bayan ya gama wanke ta son ranshi ya karasa wani kyakyawar kofa dake daga gefe gini ne na zamani da fentin shi Milk da pink ba kaman wadda suke zaune a gabanshi ba me single room da varender banda plaster ko arzikin penti be samu ba..

Key ya sa ya buɗe tsararriyar kofar ya tusa kanshi cikin parlorn, tare da kunna wuta nan haske tar ya bayyana haɗuwar parlorn me ɗauke da milk and gold royal set na kujeru da dining tsararre a gefe kayan kallo da home theaters se fridge da labulaye ruwan gold me adon milk har Ac akwai a parlorn, cikin ɗaya daga cikin kujerun ya je ya zauna yana fiddo Wayanshi kirar iPhone 12 ya fara operating cikin kwarewa kan ya sa a kunnen shi ya fara magana daidai lokacin da ta turo kofan a hankali tare da sassanyiyar sallama nan daga bakin kofan parlorn ta duke don nan ɗinne kawai take da izinin takawa a muhallin nashi idan ba shara da goge goge bane ya shigo da ita.

Wayanshi ya cigaba da yi cikin narkakkiyar murya yana zuba kalamai kaman ba shine ya gama tijaresu ba yanzu a tsakar gida, Seda ya shafe a kalla kusan awa kan ya kashe wayan nan ma be kula ta ba ya ɗauki remote ya kara muryar TV abin shi.

Kafafunta da suka fara tsami sbd tsuguno ne yasa a hankali ta ce
"Hamma Yusuf wurinka na zo, Dan Allah ka aramin mintuna biyu cikin lokacin ka magana nake so mu yi"
Seda ya bushi iska kan ya ce yana kuma haɗe gabas da yamma
"se yanzu kike da bakin magana da ni alhali kin min laifi ina faɗa a gaban waennan tsinannun yaran naki masu busashun ido irin ki baki iya bani hakuri ba?"

Lumshe idanunta da zuwa yanzu ta tabbatar baza'a samu hawaye ciki ba sbd kila sun kare tayi, 'Yarana zasu yi albarka in shaa Allah' ta faɗa a ranta a fili kuwa ta furta a hankali.
"Dan darajar Allah kayi hakuri, na san nayi kuskure kayi hakuri"
Ta riga ta saba ko da bata da laifi dolen ta ne ta bashi hakuri a duk sadda ze zage ta ko ya ci mutuncinta.

Share ta yayi, ta tattaro duk wani dauriyanta ta haɗiye miyau da da kyar take iya haɗe su a bakinta sbd azabar yunwa da ciwo da take fama dashi tana daurewa ta ce
"hamma..! Usman bashi da lafiya yau kwana biyu kenan kullum gaba gaba jikin yake yi, dan Allah ka taimaka ko chemist ne a kaishi yana jin jiki... Sannan bamu da ko kwayar hatsi a gidan nan garin masara kalilan da ta saura da shi na mana kunu da rana"

Wani mugun kallo ya watsa mata, tare da jan tsuki ya ce
"ai dama ta inda kuka fi kauri kenan kuɗi da abinci ba, ba kince kin ji kin gani daga an taɓaki se ciki a ce ki zubar bazaki zubar ba ba? Toh wallahi ba ruwana da ciwon yaron ki hakanan ba ruwana da cin su ko shan su, ke ɗin da kika zama dole na auna miki masarar da na san a cimar cikin ki ze miki wata guda churrr yanzu tsakiyar wata ki wani zo da baki kaman shadda ki ce min abinci ya kare? Toh wallahi bazan iya ba bazata saɓu ba wai bindiga a ruwa, kin tashi kin ɓace min da gani ne ko se na take ki hanjin cikinki da wannan abunda kika kuntson sun yo waje? Gantalalliya uwar fi'ili"

Duk yadda tayi kokarin haɗiye wani abu da ya tsaya mata a kirji ya tokare ta kasawa tayi, duk iya kokarin ta na ganin hawaye sun zubo mata ko da kalilan ne kasawa tayi, sun riga sun kafe sbd cin mutuncin Yusuf, se wani haki da ta fara wadda duk shekarun nan take fama dashi idan ta fara bata san denawa ba, daga kirjinta har kanta kaman zasu fice fit su bar jikinta don tsananin azaba... Da kyar ta iya fusgo maganan dake bakinta..

"Kaji tsoron Allah hamma, ka sani da ni da yaran nan zamu tsaya gaban ubangiji yayi mana hisabi, me ka tanada don kare kanka a wurin mahallicinka? Allah be hana ka ba karka tauyemu Dan Allah, Ka taimakeni Dan Allah kar in rasa ɗana zan iya jurar komai Amma Dan Allah banda su.."
Se a lokacin wasu irin hawaye masu tsananin zafi da ɗacin da take ji har ranta suka ɓalle mata.

Zuba mata idanu yayi kaman me jin tausayinta kan ya taɓe baki yana jan tsaki, hannu ya sa a aljihu ya ciro 1k sabuwa dall ya jefa mata yana cewa
"kin ci sa'ar yau baby ta hanani ɓacin rai da se na nuna miki true color na munafuka, dubu Ɗayan nan kuma har nan da wata guda in ji kin tambaye kuɗi ki ga yadda zan saɓa miki kamanni dangin Mayu kawai"

Rarrafawa tayi ta ɗauki dubu gudan, tare da mishi godiya saboda ta tabbatar in bata yin ba dubu Ɗayan se ya karɓe kuma ko kukan jini zata yi baze bata a yau ba kam gashi babban damuwanta Usman ne.

Mikewa tayi da kyar ta fice, banda ciki da idanu se karan hanci babu abunda zaka hango a jikinta gabaɗaya ta rame ta lalace, ɗaki ta shiga ta ɗauko ash himar ɗin ta da shima yayi fari sol ta saka, ta fito ta dubi Aisha dake tsugune gaban ɗan uwan nata tana share hawaye itama sanye take da doguwar rigar atampha da ya ɗangale mata sossai se milk hijab ƙarami da duk ya yage har ana ganin jan gashin ta a waje cikin yanayin sanyin ta tace

"Aisha kama min shi mu kaishi chemist ɗin Dr Musa"
Aishan ta dube ta cikin yanayi na manyancenta ta ce
"mama baki ci komai ba, Dan Allah ki sha kunun kafin mu tafi in kema kika fara rashin lafiya ban san yadda zan yi ba"
Yarinyar bata jira Cewar uwar ba ta karasa gaban murhun su ta ɗauko kunun masarar ta zo ta Mikawa maman, zama tayi ta kurɓe Dukda wani irin murɗawa da ɗan cikinta yayi a sadda abincin ya sauka gare shi, wani irin tausayinshi ne ya lulluɓe ta hannunta ta daura kan cikin ta ce
"kayi hakuri"

Bayan ta gama sha ta mike, Aisha ta taimaka mata suka dafe Usman suka fice daga gidan bayan ta sa mishi rigar wani kodaɗɗen jumfa da gefe da gefe suka yayyage, fitowa suka yi idanu ta ɗan zubawa motar Yusuf ɗin kirar Vibe sabuwa dal baƙa me ɗaukan idanu kan ta ɗauke kai suka zagaye shi suka wuce chemist...

****

Tou fa mutanena, ga Gureenjoh da wata sabuwa su waye wannan ahali wani irin zama ne wannan? Shin Hidayat bata da en uwa ne? Bata da dangi ne? Shin Ba auren soyayya bane suka yi tsakanin ta da Yusuf? Ko kuwa auren dangantaka ne tunda tana alakan ta shi da hamma...? Shin yaran ba yaranshi bane da yake alakanta su da tsinuwa? Me suka yi da zafi haka?
Duk ku biyo Ƴar mutan Gurin na jihar Adamawa don warware wannan zare da Abawar wannan littafi kyauta ce... A sha karatu lafiya.

#Vote
#share
#Comment

🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now