Duk da cewa ran Muhsin a b'ace yake, sosai ya sha jinin jikin shi da jin zancen ta, bai tab'a kawowa a ranshi Sulaimi zata yi suggesting haka ba. Dan masoyiyar shi ma'abociyar hakuri da tausayi ce.

"Habibtie rape? Fyad'e fa kika ce?" So yake ya tabbatar ba wasa kunnen sa suke mishi ba. Jin yadda yayi maganar ne yasa Sulaimi ta fashe da kuka nan ta fara mishi karya tana hura mishi wuta. Daga karshe dai sai da ya amince.

Allah Sarki Rahma da bata san hawa ko sauka ba, tun da ta tashi da asuba bata koma bacci ba, azkar tayi na awa daya da mintuna sannan ta fara karanta Alqur'ani mai girma.

Daga gefenta kuwa Jannah ce da ta daura kanta bisa cinyar 'yar uwarta. Kwana tayi tana kallon series a laptop dinta, sai kusan asuba tayi bacci. Da kyar ta iya kammala wasu daga cikin azkar dinta ko data idar da sallar ma. Tun Rahma na tashin ta har ta hakura ta kyale ta.

Ko da ta kammala suratul baqara, kallon Jannah tayi dake gyara kwanciyar ta bisa cinyar ta. Hannu ta kai ta shafa gashin ta sannan ta sumbaci goshin ta, tana jin matukar so da tausayi kanwarta har cikin ranta.

"Ya Allah please protect my sister wherever she is, Ka kare mata mutuncin ta, Ya Allah preserve her faith, guide her to the right path. Ka saukaka mata al'amuran ta, fill her life with utmost happiness, Ka azurta ta da kyakkyawar karshe. Ya Allah You are sufficient for us, Ya Allah Ka bani ikon maye mata gurbin uwa. Amin Ya Rabbi".

Ko da ta kammala addu'ar, bata damu da ta tashi ba, gudun kar ta tashi Jannah dake bacci. Sai kusan 8:30 kafin ta maida kan Jannah bisa pillow, nan ma sai data tofe ta addu'o'i kafin ta fice.

A kitchen ta tarar da Aisha tana jefa dan wake yayin da Mairo ke wanke-wanke. Gaishe su tayi, da fara'a Aisha ta amsa, ita kuwa Mairo kamar wanda dole aka sata amsawa, dan ita ma tana cikin wadanda basa kaunar Rahma da Jannah.

Kallon Aisha tayi, cikin sanyin muryar ta tace "what's for breakfast?". Da murmushi Aisha tace "dan wake" gyad'a kai Rahma tayi sannan tayi wa Aisha murmushi. Ta san aikin hannun Aunty Hafsa ne wannan dan ita kadai ke sa a jefa dan wake da safe.

Kuma duk sanda aka yi dan waken, ita Aunty Hafsa dasu Aisha da Mairo kadai ke ci. Dan yaran ko kallon shi basa yi, haka zalika Ya Umar da yake bai cika cin abu mai maiko ba sai bai damu da dan waken ba.

Hannun rigar jikinta ta daga sama sannan ta zare gyalen kanta ta daura shi kamar dan kwali. Gani tayi su Aisha da Mairo na binta da ido. Har yanzu kyau irin na Rahma sosai yake basu mamaki. Barin ma inta zare dan kwali ta dogon gashin ta ya bayyana, sai tayi wani irin kyau da annuri. Gata fara sol tamkar madara.

Cabinets ta bud'e tana nazarin abin da za'a girka, abincin mutanen Iraq ne ya fad'o mata rai. Nan ta hau girka khubz da bigilla, sai Makhlama da kuma Shayin da yaji kayan kanshi Ko kad'an bata kaunar 'dan wake, tun wani lokaci da ya bata musu ciki ita da Jannah.

Ko da ta kammala, sai da ta zubawa Aisha da Mairo nasu. Sake gyara zaman mayafin ta tayi ta tabbata dukkan jikin ta a rufe sannan ta fice da sauran ta kai dining.

Isar ta dining room din ta jiyo sallamar Jannah nan ta ji an yi hugging d'inta ta baya, murmushi me sauti Jannah tayi tace  "Morning big sis". Girgiza kai Rahma tayi da fara'a ta amsa ta "Morning sleepyhead. Finally you're awake!".

Nan ma smiling tayi, yau ta tashi da wani irin farin ciki, zuciyar ta fal da nutsuwa. Hakan yasa take ta fara'a " yup. A tantalizing aroma invaded my sleep, hence I had to wake up. Ashe kanshin girkin ki ne. I should have known". Tana maganar ne yayin da take bud'e casseroles din abincin da 'yar uwar ta ta girka. Har had'iyan yawu take ganin ya jima bata ci ba.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 11, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ILLAR MARAICIWhere stories live. Discover now