TSAKANIN MU

59 6 2
                                    

*TSAKANIN MU*

_Mallakar Mum Irfaan_ *_Wattpad~MumIrfaan_*

*Page 1*

Mamanta kallanta tayi ta zauna tai tagumi, ga dukkan alama tunani take, kallanta tayi tana mamanki shekarun Ruƙayya dudu nawane, bazasu wuce she Kara Sha biyar ba amma Abunda ke ɗaure mata kai yawan zaman da take tana yawan tunani, girgiza kai tayi tana faɗin yaran zamani kenan sunsan menene rayuwa, "Ki tashi Maman Jameel na kiranki"
Ta faɗa tana ƙarewa fuskarta kallo, ko kaɗan Ruƙayya bataji Abunda ta faɗa mata ba, shiru mahaifiyarta tayi cikin natsuwa tace "Ruƙayya!" Da ɗan ƙarfi, a ɗan firgice ta juyo tana kallan mahaifiyar tata, cikin natsuwa Mamanta tace "Wai meke damunki ne haka Ruƙayya?, Ace inhar zaki zauna ke kaɗai sai kin ta tunane-tunane, anya..." Ta ƙarashe tana mata kallan tuhuma, tanaso ta gano wani abu game da ƴar tata.
Matuƙa abun na damunta sede tana tsoron yadda zata sanar da mahaifiyar ta abinda ke faruwa game da ita, batasan ya zata ɗauki abun ba, rausayar dakai tayi tace "Umma ba komi, kawai banajin daɗi" ta faɗa hawaye nabin kuncinta.
Shiru Mamanta tayi tana me mamakin zurfin ciki na Ruƙayya, shinkafar dake faranti ta kalla ta cigaba da tsintar ta hankalin ta naga shinkafar tana tsinceta tace "Maman Jameel na kiranki"
Gabanta ne ya yanke yayi wani irin mummunan faɗuwa, har ga Allah batason tana zuwa gidansu Jameel, jiki ba ƙwari ta shiga ɗaki ta ɗauko mayafinta, ta nufa gidansu Jameel dake maƙotansu, mahaifiyarta duk ta fuskanci yanayin ta data ce taje gidansu, haka kawai itama se jikinta bai bata ba dan ta lura da ɗiyarta a kwanakin nan ko kaɗan bata ƙaunar taje gidan, cikin kyakkyawan zato ta cigaba da aikinta ganin yamma ta gabato.
Cikin sanɗa ta shiga cikin gidan ko sallama batai ba, har seda taje ƙofar ɗakin Ummii kasancewar haka suke kiranta, sannan ta daidaita natsuwarta tai sallama cikin natsuwa da kamala.
Cikin fara'a Ummii ta ganta tace "Ai yau nayi fushi, meya faru yau kwata-kwata bakizo gidannan ba har saida na aika a kiramin ke"
Yaƙe Ruƙayya tayi tace "Banajin daɗi ne Ummii, zazzaɓi ke damuna" kanta ƙasa ganin irin kallan da Jameel ya jefeta dashi.
Shiru tayi ta zauna ƙasan wani lallau san carpert dake tsaƙiyar ɗakin.
Girgiza kai Ummii tayi tace "Na hana ki zaman ƙasa bakya ji, se sanyi ya kamaki" ta faɗa tana kallan Ruƙayya don har ga Allah tana matuƙar son yarinyar ganin Allah bai bata ɗiya mace ba duka maza ne, satar kallansa tayi taga hankalinsa nakan Curve TV ɗin dake zaune kan TV Stand Yana kallan wani Film dake MBC 2, "Ina yini" ta faɗa muryarta can ƙasa ƙirjinta na faman faɗuwa, cikin muryarsa mai daɗin saurara yace "Lafiya ƙalau" kansa nakan TV ɗin da yake kalla.
Ummii tashi tayi tace "Bari na leƙa part ɗin Abbanku, naji ya shigo" ta faɗa tana ƙoƙarin fita daga Parlourn.
Shiru ne ya biyo baya ba abinda kake ji se ƙarar A.C dake cikin ɗakin.
Yayinda kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
Jameel tunda mahaifiyarsa tabar Parlour hankalinsa da kallonsa ya koma kacokan kan Ruƙayya, yana kallanta ganin ko kaɗan yanzu ta daina yadda dashi kamar da, kuma ta daina sakin jiki dashi, numfasawa yayi a hankali ya tashi daga lumtsatstsiyar kujerar da yake kai ya dawo gab inda take, yayinda numfashinsu ya fara cunɗanya dana juna, ƙamshin turaransa ne ya sanar da ita zuwanshi a ɗan firgice ta fara ƙoƙarin tashi daga inda dake tanaso tabar ɗakin, hannunta ya kama yana ƙare mata kallo, cikin sanyi murya yace "Haba Ruƙayya horon da kikemin yamin yawa don Allah ki sassauta min"
Kukan dake kwance a ƙwayar idonta ne suka gangaro zuwa kuncinta ta kasa ce mishi uffan tana ƙoƙarin ƙwace hannunta, muryata na rawa tace "Don Allah Yaya ka sakeni"
Shiru yayi yana kallan yanayin ta , ganin gabaki ɗaya bata cikin hayyacinta wani irin tsoro ne a kwance a fuskarta, ga wani irin kallo data ke jefanshi dashi ya rasa da wani irin kallo zai masiltashi.
Cikin sanyin murya yace "I'm Sorry, bazan ƙara ba"
Rausayar da kanta tayi tana ƙoƙarin ƙwace hannunta dake cikin nashi tana jin wani irin abu na ratsa ta.
A hankali ya saki hannunta ya miƙe tsaye ba tare da ya waigo inda take fa ya fara tafiyar sa cikin natsuwa.
Kallan shi kawai take har sai da taga ya ɓace ma ganinta sannan ta saki wani irin ajiyar zuciya, tana kallan hannun daya riƙe mata, ɗan gyara zamanta tayi tana ƙarewa Parlour din kallo tamkar yau ta fara ganin ɗakin.
Kana kallan tsarin Parlour din kasan dukiya tayi kuka a wajan domin Parlour ne nagani nafaɗa duk wani abun more rayuwa najin daɗi Parlour din ya haɗa.
Jikinta ne ya bata ana kallanta a hankali ta ɗaga kanta ta kalli ƙofar da ake shigowa, batasan lokacin data saki wani irin murmushi ba, nan take fuskarta ta cika da annuri, "Yaya Fahad" ta faɗa tana wasa da ɗan ƙaramin zoben dake kwance kan tsintsiyar hannunta.
Kana ganinsa kaga ɗan gidan domin suna kama da Jameel sosai sede Jameel ya fishi kyau nesa ba kusa ba, komi na Jameel ya fita daban dana ƙannansa.
Hannunsa rungume a ƙirjinsa shima yana mata fara'a yace "Shine yau bakizo ba ko?, Nasan saboda mai yasa baki zo ba, Ina Assignment ɗin dana baki?" Ya faɗa yana kafeta da fararan idanunsa.
Turo mai baki tayi gaba, baisan Lokacin daya saki wani irin malalacin murmushi ba, a hankali ya ƙaraso inda take zaune yana kallan ɗan ƙaramin bakinta ganin yadda ta turoshi gaba yace "Ina Assignment ɗin"
Kanta na ƙasa tace "Yana gida, ai Ummii ce tace nazo na tayata hira, shiyasa ban taho dashi ba" ta faɗa tana ƙoƙarin guntse dariyarta.
"Uhmm" kawai yace ya tashi ya fice daga ɗakin, maida hankalinta tayi kan TV ɗin dake ɗakin tana kallan tashan Cartoon, sosai zuciyar ta take bambance mata halayyar Fahad da Jameel, Muhd kuwa ko kaɗan basa haɗa inuwa ɗaya dashi, shine Autan gidan, haka kawai suke wa juna kiyayya daga ita har shi, in ɗaya na zaune a guri to tabbas ɗaya ze tashi yabar inda ɗayan yake duk da Muhd ya girme mata kaɗan, amma hakan bai hanata ƙin sa ba, tana Mamakin zuciyar Muhd gani take tamkar ba Ummii bace ta haifesa ba saboda halinsa daban yake cikin ƴaƴanta, yarone sangartacce ga kuma rashin kunya, ko kaɗan baya ganin girman kowa inba iyayansa ba, dama Jameel baya shiga sabgar sa don mutum ne wanda bayason raini ko kaɗan.
Ƴar aikin gidan ce ta shigo Parlourn, kallan Ruƙayyah tayi tace "Yaya na kiranki"
Ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaukar bokitin Mopper.
Gabanta ne yayi wani irin mummunan faɗuwa ta kafeta da idanu cikin sanyin murya ta "Yana ina?"
"Ɗakinsa naga ya nufa" ta faɗa hankalinta nakan mopping ɗin data fara.
Shiru tai bata da niyyar tashi, ba abinda zuciyarta ke mata face dukan uku-uku, hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, a hankali ta mike ta nufa hanyar fita daga ɗakin tanaso ta tafi gida ba tare da kowa ya ganta ba.
Ummii ce ta fito kunnanta manne da waya tace "Gama tanan" ta faɗa tana kallan Ruƙayya yayinda hatta kai ƙofar fita, "Karɓi Yayanki na magana"
Daurewa tayi ta karɓa yayin da ta daidaita natsuwarta ta kara wayar a kunne jikinta na ɗan rawa "Uhmmm" kawai tace ta cire wayar a kunnanta ta miƙawa Ummii tana faman yaƙe, ganin ta juya ta koma part ɗin me gidan, hamdala tayi a zuciyarta itama ta juya ta nufa hanyar fita daga gidan.
Cikin sauri-sauri ta nufa harabar gidan, tsayawa tayi cak ta sadda kanta ƙasa, a hankali ta ɗaga kanta ta kallesa ganin irin kallan daya ke mata ne yasata motsa ƙafarta a hankali ta nufo inda yake, a hankali ya fara tafiya yayinda ita kuma tabi bayansa ba abinda bakinta ke ambata face sunayan Allah.

*#Comments*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*

TSAKANIN MUWhere stories live. Discover now