09

934 69 11
                                    

If you're not living around these people, you will never know what they are going through, fiye da haka ma yana faruwa, kawai dai Allah ya tsare mu su kuma yai musu mafita.
Tun daga jin sunan Labarin kun san abun da ya kunsa. Ban san abun da readers suke so ba, idan an saka kudi da luxury life sai ace writers suna bude idon mutane, and when we're talking about reality kuma ba mu tsira ba, anyway if you don't like the story you can quit it.

*** *** ***

Har past 12am Talba yana zaune bangaren Momy doing nothing, haka nan kawai yake jin yanayinsa sai a hankali. Idan zaka tambaye shi damuwarsa ba zai ce maka ga matsalarsa ba. Mikewa yai tsaye ya isa gaban plasma ya kashe sannan ya wuce kitchen domin samu abun da zai sakawa cikinsa, rabonsa da abinci tun da rana, ko lunch din Momy ta hada be ci ba. Tea ya fara hadawa kansa sannan ya bude freezer dake kashe ya dauko cake ya kunna oven ya saka shi a ciki, sannan ya dauki tea ya rike a hannunsa yana ta kallon harabar gidan ta windows kitchen din, ko ina haske ne kamar rana.
Juyowa yai a hankali jin kamar shesshekar kuka a falo, aje cup din dake hannunsa yai ya tako a hankali zuwa bakin kofar kitchen din ya tsaya. Sai ya hango Leila zaune a bakin stairs din sanye da kayan bachi riga da wando sai kuma safar dake kafarta, kanta ba dankwali sai hawaye take tana kallon wani bangare na falon, sam bata lura da shi ba har sai da ta juyo tana cigaba da rera kukan a hankali. Suna hada ido sai tai sauri share hawayenta ta dauke kai sannan ta mike tsaye ta juya a hankali zata hau stairs din.
Har tai rabi ban da kallon mamaki babu abun da Talba yake mata.

"Leila..."

Ya kira sunanta kamar wanda baya son magana, tsayawa tai cak gabanta na mugun faduwa, domin har ga Allah bata dauka yana zaune a falon har lokacin ba, da b zata fito daga dakinta ba, juyowa tai a hankali sai dai bata yarda ta kalleshi, sanin kanta ne ba zai tambaye ta me take yi ma kuka ba, kiran sunanta kawai da yai ya isa ya sanar da ita cewar tambayar damuwarta yake.

"Na yi mafarkin tsoro ne..."

Ta fada tana wasa da yatsun hannunta, bata tsaya jiran abun da zai ce mata ba ta juya da sauri ta haura sama. Da kallo ya bita har ta bace masa sannan ya juyo ya dawo cikin kitchen din, mamaki karara a fuskarsa.

'Mafarki tsoro?'

Ya maimaita aransa, idan mafarkin tsoro tai me zai saka ta fito a nan ta zauna ita kadai?

"Ko dai saboda ni ne?"

Ya tambayi kansa yana kokarin kai hannunsa ya dauki tea, domin ya san abun da zai tashi hankalin Leila ba karami ba ne, and bayan shi ba ya ji akwai wani abu da zai saka Leila ta yi kuka ko ta shiga damuwa. Kamar wanda baya son bude baki haka ya kai cup din a bakinsa ya soma sha a hankali, dayan hannunsa ya saka a aljihu yana kallon oven din sai dai gaba daya tunaninsa ba a nan yake ba.
Sai da ya sha rabin tea sannan ya kashe oven din ya ciro cake din daya dumama ya aje, ya dauki tissue ya saka a hannunsa sannan ya fara daukar cake din yana ci. Bayan ya gama ya kashe wutar kitchen din ya fito falo ya kashe wutar sannan ya wuce bangarensa. Shirt din jikinsa ya fara cirewa wanda hakan ya bawa kyakkyawar surarsa da murdaden kirjinsa bayyana, a kafadarsa ya dora rigar sannan ya nufi wani madaidaicin daki dake hannunsa na dama, a hankali ya murda kofar ya bude ya shiga, kai tsaye ya nufi teburinsa ya ja kujera ya zauna ya bude system dinsa yana duba sakon da Jahid ya turo masa na adadin kudin da za a kashe wannan watan na gidan marayu.

"Okay"

Ya furta sannan ya rufe system din ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa ya kunna data ya shiga WhatsApp.

'Zan rubuta maka cheque gobe, after that, ka bincika abun da yan gudun hijira suka fi bukata ka kirga ko nawa za akashe na mutun 300'

Bayan ya gama rubuta masaya kashe data ba tare da ya duba sako ko daya da yake shigo masa ba, balle har ya amsa. Fitowa yai daga dakin ya nufi Bedroom dinsa yana shiga ya aje rigar dake kafardarsa a muhallinta ya cire jean din jikinsa ya nufi bathroom ya jika jikinsa da ruwa ba tare da ya saka sabulu ba yai alwala ya fito, sai da ya tsane jikinsa sannan ya nufi closet din ya dauko kayansa na bachi.
Wando kawai ya saka domin abu ne mai wahala ya kwana da riga komai tsananin sanyi, sai dai ya rufa da bargo, riga na cikin abun da ke takura shi ta hana shi sakewa idan zai yi bachin dare.

BAKAR WASIKAWhere stories live. Discover now