03

1.1K 76 2
                                    

Shigowar Daddy ne yasa Momy ta cire farin gilashin idonta tana murmushi.

“Ranka ya dade an fito?”

Kusa da Amal ya zauna yana murmushi.

“Allah ya yarda”

Ya fada yana karewa katon falon kallo ganin Momy ce kawai sai Khadija da kuma Kabir, abun da ba kasafai yake gani ba, ya saba every weekend yana zuwa falon Momy ya zauna tare da ita da kuma yaransa, kowa ya fadi bukatarsa ayi hira a bawa juna shawara, ayi nishadi. Sometimes kuma shi zai kira su a bangarensa a tare a can.

“Daddy barka da wuni”

“Yauwa, Son”

Ya amsawa yana yi ma kowa kallon tsanaki, ciki har da yar autarsa Amal da ta wani hade rai.

“Hajiya ya ga falon ku kadai? Ina sauran yarana suke?”

Momy ta kalli Kabir dake kallonta sannan ta kalli Amal kamin tace komai Kabir ya tari numfashinta.

“Daddy yaranka biyu fushi suke da juna, kasan Angry Birds ne”

Daddy ya kalli Momy.

“Since when?”

Kabir zai sake magana Daddy ya dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu, wanda hakan ke nuna kai tsaye Momy yake son ta amsa masa tambayarsa. Momy ta sauke ajiyar zuciya.

“Ni ma dazun nan na sani...”

A tsanake ta labarta masa abun da ya faru ciki har da fadan da tai ma Leila.

“Amman baki fada min ba? Taya zaki bar Mu'az ya fita ba tare da yayi breakfast ba? And baki dama ki san a wane hali yake ba?”

Momy ta lumshe ido ta bude tana murmushi.

“Wani lokacin kana maida Talba kamar wani karamin yaro, ya san yadda zai kula da kansa Alhaji”

“Ko da Mu'az zai shekara dari matukar ina raye to shi yaro ne a gurina, a shirya mana abincin rana tare”

“An gama ranka ya dade”

Ya mike tsaye sai Amal ta kalleshi.

“Daddy ni ma fa kaga ina fushin nan amman baka ce komai ba”

Sai a lokacin Daddy ya tuna da tana gefensa sai ya kalleta yana murmushi.

“Amal sorry wata taba ki?”

Ta nuna Kabir sai Kabir yai saurin daga hannayensa sama ya mike tsaye.

“Na ma bar muku falon”

Kamin Daddy yace komai ya nufi kofar fita daga falon da saurinsa yana murmushi.

“Mu yi masa uzuri amman yau kawai next idan ya sake tsokanarki zamu raba gari da shi”

Daddy ya fada yana kallon kyakkyawar yarsa. Sai ta sakar masa murmushi.

“Toh Daddy”

“Good”

Cewar Daddy yana ciro wayarsa ya kira Talba, ringing daya yai picking kamar daman can kiran yake jira.

“Hello Daddy”

“Mu'az kana Ina?”

Ya kalli katon office din da yake ciki kamar mai son tantance inda yake.

“Office Daddy”

“Me kake a office? Yau Weekend?”

“I don't know...Getting some fresh air”

“Baka fada min kana da damuwa ba, mu da kai ba abokai ba ne? Ba ma boyewa juna abu?”

Wani irin kasaitaccen murmushi ne ya bayyana a fuskarsa, ya mike tsaye daga inda yake zaune ya nufi windows.

BAKAR WASIKAWhere stories live. Discover now