05

996 64 5
                                    

Sai after sallah isha'i ya fito harabar gidan ya zauna a inda aka jera kujerun zama domin hutawa, kusa da garden, sai kamshin turare yake kamar sabon ango, fuskarsa cike da annuri, sai dai babu walwala ko kadan a tare da shi.
A hankali ya hade yawun bakinsa ya daga kansa sama yana kallon taurarin dake samaniya, kamin ya juyo yana kallon Amal dake sanye da kayan bachi tana nufo inda yake.

“Ya Talba”

Ya dan sakar mata murmushi kadan.

“Lil Sis ya kike?”

Ta zauna a kusa dake kusa da tashi tana amsawa.

“Lafiya kalau”

Sai kuma ta yi shuru tana kallonsa.

“Kina bukatar wani abu ne?”

Ta girgiza kai ta soma wasa da yatsun hannunta.

“Talk to me Lil Sis fada min damuwarki”

Ya fada yana kallon yanayinta dake nuna akwai damuwa a tare da ita.

“Yaya ka sake yin fada da Ya Leila ne?”

Fada suka yi? Ya zai fada mata? Abun da suka yi fada ne ko aa, shi be ma tabbatar ba, all what he know is ta kira shi wani shi kuma ya fada mata magana, sincerely speaking ma ya manta me yace mata.

“Yeah Maybe”

Ya fada yana dan tabe baki.

“Miya faru?”

“Ta dawo gida tana ta kuka tun dazun, yanzu kuma kuma Daddy ya shigo yai ma Momy fada ita ma kuka take?”

“Why?”

“I don't know, kawai dai na ji Daddy yana cewa babu wanda ya isa ya wulakanta masa d'a, kuma wai ya zaba maka Leila ne saboda kar kaje neman auren wata a wani gidan ace ba za a baka ba saboda yadda kake behaving, amman a gidansa yana da iko da Leila”

Talba ya cika ma bakinsa iska ya busar.

“Ina Momy?”

“Tana dakinta...”

Amal ta karasa tana kallon Kabir daya doso inda suke zaune ta kofar gaba, kana ganinsa ka san a fusace yake.

“Look Talba, ba zaka Leila kuka saboda bakin halinka and now ka saka Momy kuka ba okay? I won't tolerate this, dole ne sai ka auri Leila ne? Idan ba ka canja hali ba ba zaka taba aure ba a rayuwarka”

Daga inda yake zaune ya dago yana yi ma Kabir wani banzan kallo.

“Ka sani ba a amin tsawa ba a nuna ni da yatsa”

“To sannu ubana, sannu Sarkin Arewa, girman kai zai kashe Mtssssssssss”

Kabir ya karasa yana jan wani dogon tsaki. Amal ta yi saurin kama hannun Talba.

“Ya taso mu bar mishi gurin gaba daya”

Uffan Talba be sake cewa ba ya bi Amal dake rike da hannunsa, har sai da suka shigo cikin falon sannan ya saki hannunta.

“Je dakinki zan yi magana da Daddy”

“To amman karka ce masa ni na maka gulmar”

Yayi murmushi ya juya zuwa bangaren Daddy. Daman can duk wata gulmar gidan gurin Amal ake jinta. Cikin natsuwa da kamala ya shiga bangaren Daddy, yai sallama Daddy ya amsa masa tare da kai hannu ya dauki remote ya kashe plasma dake kunne. Talba ya zauna kasa kusa da kafafuwan Daddy.

“Daddy yau na kawo maka karar kanka”

Daddy yayi murmushi.

“Na taba Momy ko?”

BAKAR WASIKAWhere stories live. Discover now