0-1

2.6K 114 11
                                    

💔-BAKAR WASIKA-💔
     Mai Farin rubutu

From the writer of

RAI BIYU
HAFSATU MANGA
ZAGON KASA
ZABIN RAI
KHADIJATU
GOBENA
ZAKI
FULANI

©®Hakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a Website ko YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye ⚠

SADAUKARWA.
Na Sadaukar da littafin nan ga Hajiya Habiba da iyalanta.

GAISUWA
Ga Mutanen Kirki, Rahma Kabir, da Mrs J Moon.

GABATARWA.

BAƘAR WASIƘA...
Mai farin rubutu

Idan aka ce Bakar Wasika Mai Farin Rubutu. Ana nufin wani dunkulelen sako mai wuyar fassara, kamar mutum mai nagarta sai wani mummunnan kaddara ta fada masa.

Ban ce tafiyar mai sauki ba ce.
Ban muku alkawarin zallar soyayya ba.
Ban ce babu farincikin ba.
Kunci, bakinciki da damuwa, sune abubuwan da suka taru suka tare farincikin AMINATU, kalubalen rayuwa bayan wata rayuwar, tabbas akwai kuka akwai damuwa da bakinciki.

Labarin Tafida, Rafi'a, Laila, Madina, Ramlee, Faruk, Amal, Kabir da kuma Aminatu.
Labarin BAKAR WASIKA. Labari ne da zai tabo wani bangare na rayuwar mace, kuma wani bangare na rayuwar al'ummarta da iyayenta...
Ina fatar zaku karbe shi kamar sauran, duk kuwa da na san ba lallai ne yai muku dadi ba domin ba soyayya ce zalla ba, kalubalen rayuwa ne da fadi tashin yar gudun hijira!
A ina zata kwana? Wa zai bata masauki? Taya za a fahimce ta har a nade mata damuwarta? Wa zata kaiwa kukanta iyeyenta ko al'ummarta? Ta ina mafarkinta ke tabbatuwa? Ashe bayan wuya akwai wata wuyar, bayan dadi ma akwai wata wuyar, bayan wuya kuma akwai dadi.
Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke?
Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin rayuwar ma akwai mutuwa?

Labarin BAKAR WASIKA kirkiraren labari ne kamar sauran labaraina, kun san dai ban saba baku kunya ba ko?😉 Wannan ma zai zo muku fiye da yadda kuke tsammaninsa inshallahu. Sai dai ba free ba ne na kudi ne, but ina da free pages daga 1-10 ga masu son jin dandanon labarin kamin biya.
Kamar yadda kuka sani bana editing labari so ku yi hakuri da duk abun da zaku gani.

P. O. V
Na nufin Point Of  View.

                      بِسْمِ ٱللَّٰهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

Page -1⃣

Matashiyar yarinya ce yar shekara goma sha-bakwai dauke da farantin giɗa tana tsaye jikin window makaranta tana leken daliban da ake yi wa darasi.
Yadda ta maida hankali tana sauraren darasin da ake wa dabiban sai ka rantse da Allah har da ita a cikin daliban. Ilmin zamani na daya daga cikin abubuwan da suke matukar burge Aminatu kuma shi ne kadai abun da ta rasa a yanzu, wanda ta riga ta maye gurbinsa da talla a halin yanzu, a izuwa yanzu ta tabbatar bata da muhalli a ilmin zamani, sai dai shi ilmin yana da muhallin a zuciyarta.

"Ba ni gidar goma"

Wata dalibar ta fada da kamar rada gudun kar malamin da yake musu darasin ya ji ta, a munafunci ta jefowa Aminatu wata tsohuwar naira goma, sannan ta maida hankalinta gurin Malamin.
Aminatu ta duka kasa ta sauke farantin dake hannunta sannan ta dauki naira goma din ta daga hijabinta ta saka naira goma din cikin hular dake kanta ta gyara hijabinta sannan ta dauki giɗar ta mika mata, yarinyar ta karba da sauri ta boye.
A lokacin ne malamin ya hango Aminatu tana kallon allon da yake koya musu darasin, kusan wannan shi ne karo na barkatai da yake arba da yara na shigowa makarantar talla, wani lokacin har cikin ajijuwa suke zagayawa idan sun ga babu malamai a ciki.
Sai dai tsayawa a nasu ana daukar darasin karatu babu kamar Aminatu domin ko daliban makaranta basa nuna mata natsuwa da maida hankali sai dai su nuna mata iya rubutu da kuma fahimtar darasin yadda ya kamata domin su a kullum suna aji ne, ita kuma sai idan talla ta biyo da ita.

BAKAR WASIKAWhere stories live. Discover now