57-58

1.2K 122 31
                                    

After 4mouth
Mutuwar Deen ta girgiza dukkan ahalinsa Musamman Moon da besty, Moon kullum cikin surutai take tare mafarkin Deen da kuma Irin kalaman soyayyar daya dinga gaya mata a cikin jirgi, ta zama wata iriya tayi waek ta zama shiru shiru kamar kurma, abinci sai da aka yi da gske ta fara ci, besty kam ji yay garin yay masa zafi he wish ya samu damar barin garin amma babu dama,wanda yake tunanin zai zama jagoran talakawa yau gashi ya tafi ya barsa,a yadda yake yanzu baya jin kuma zai iya komawa kan kujerarsa, kullum cikin tunanin wanda zai maye gurbin Deen yake, Adyan kam ganin abun yake tamkar a mafarki bai taɓa tunanin haka bom yake raba jikin mutum ba sai yanzu,duk da cewa shi soja ne amma bai taɓa shiga dajin da ake data bom ba,daman irin Wannan haɗarin anfi tura Deen da Ammar daman ance wani aikinsa shike zama aljalinsa, kullum addu'ar sa Allah ya jiƙan Deen kuma yay masa Rahama, Lokacin da aka buƙaci wani daga cikin dangin Deen yazo ya amshi lambar girmamawa Moon ce ta shirya ta amsa banda kuka babu abinda take.

Zaune suke gaba ɗaya a babban parlour a garin Barno wanda tun safe Besty da Yayinda da kuma Nene suka sauka dalilin kiran da Ammar yay masu, ajjiyar zuciya ya sauke Sarki Aliyu Al'amin yace "Go on! Ammar" kan Ammar a ƙasa yace "Wata rana muna zaune a Aliyou bayan dawowarsa daga Illori, yake faɗa min abinda yake damunsa,da mmki na kallesa nace "me kuma yake damunka?" Deen yace "nayi searching akan Human trafficking da muke fama dashi a society namu, kuma ina zargin mutane da yawa, amma ance zato zunubi ne koda gsky ce,na nemi izini daga sama Aban ma'aikata ina son yin aikin sirrin wanda ko iyaye na basu san da abun ba, aban dama yin hakan so na zaɓe ka da kuma Adyan, nayi bincike akan wata yarinya Nana khadii ina son aikina ya fara ta kanta, amma dole sai ya kasance wani daga cikinmu ya aureta, kuma na riga dana yanke shawarar kai Amma kai ne zaka aureta za muyi mgn da mahaifinta nai masa bayanin komai amma bana buƙatar yarinyar tasan komai ka gane?" Babu musu Ammar yace "duk yadda kayi dai-dai ne,amma akanwa zakai aikin" kai tsaye Deen yace "Alhaji Bashir Yahya gidan iko,ban yarda da shi ba,yana da fuska biyu,kafin naje garesa zan fara zuwa inda suke da zama a can  Banglandesh, daga nan zan maka bayanin abinda ake ciki". Kamar yadda Deen ya faɗa min yaje Banglandesh kai tsaye Renaissance Dhaka Gulshan Hotel ya shiga, yana zaune a reception kuda da wani babban mutum baki ne mai kauri, Ɗaga waya yay kamar mai kira Deen ya shiga faɗin "Kai wawa ne, ina bayanin yadda zamu dinga samun kuɗi kana mgnar banza, kai wlh da zan samu mataimaka kidnapping zan fara meye a ciki to? Bana tsoran komai wlh zuciyata a bushe take" Mutumin tunda  Deen ya fara magana yake kallonsa yana mmkin rashin tsoran Deen, baya tunanin wani zaiji abinda yake faɗa? Numfashi yaja yace "Hi" kamar Deen bazai magana ba sai kuma yace "How can i help you?" Ranin hankali kenan cewar mutumin kafin yace "Damus my name, ina son muyi mgn very impressed wacce zai taimaka maka" shiru Deen sai kuma ya ɗan saki fuska yace "ok" Damus yaywa Deen bayanin komai akan Human trafficking ɗin da suke kana yace "zanwa Oga mgn akan ka idan kana so,yadda mukai zan gaya maka ai a hotel ɗin nan kake ko?" Jinjina kai Deen yay yace "idan kayi ka gama min komai zanyi biyayya gareku indai akwai samuwa" daga nan sukai sharing number waya tare dayin sallama.
Bayan kwana biyu Oga Taju ya buƙaci mgn da Deen ta hanyar vedio'n call, yana daga can Bangkok tunda Deen yaga mutumin zargin sa ya fara zama gsky, daga nan Oga Taju ya bawa Aliyou sunan Deen tunda yay masu ƙarya yace sunansa Isma'il, rashin kenan Oga Taju bai sunnan grandfather ɗin Deen Kamluddeen shiyasa ya amince ya amshi sunan Deen, sosai Oga Taju ya bawa Deen yarda da kuma amince komai yace Deen.
Wata rana Oga Taju ya buƙaci Deen ya fara aiki kuma zai fara akan Moon, da mmki Deen yace "why ita Oga?" Murmushi Oga Taju yace "she's beautiful za'a iya bawa yarinyar most beautiful a wannan ƙasar baki ɗaya tun tana yarinya, ƴar gidan Sarki Aliyu Al'amin sarkin Barno ce, sunyi hatsari a hanyarsu na dawo gida daga airport, wanda hatsari ni na haddasa sbd na samu damar ɗauke yarinyar, idan muka samu yarinyar mun gama samun komai, abin mmki aka nemi yarinyar aka rasa iyayenta sun jigata babu wanda yasan halin da yake ciki,ashe yarinyar wani ya ɗauke ta domin yaji abinda muke faɗa bayan hatsarin ya faru kafin zuwan securities, tun daga ranar ban sake samun labarinta ba, shi kuma Mutumin baya sakewa da jama'a domin ya ɗauki al'ƙawarin ingata rayuwarta tunda bashi da wata yarinya, kwanci tashi na samu labarin inda yake da zama a nan Nigeria a cikin garin Kano, zan baka komai na mutumin address da bayanai da kuma photon yarinyar" daga nan Deen ya shirya zuwa Nigeria ƙasar da bai taɓa zuwa ba,  cikin wata shiga ta talakawa ya shirya ya nufi wani gida wanda yake farcing gidansu Moon, ya nemi aiki, cikin sauƙi Deen ya samu aiki ashe mutumin gidan shine wannan Oga Taju yana sane ya amshi Deen matsayin mai gadi sbd yasan aikinsa ne, shima Deen kallo guda yayawa Alhaji Bashir yasan cewa shine Oga Taju, tunda yaje kuma basa ga maciji da Farouk kullum cikin faɗa yake wannan mutum yana da hali sai dai wani dalilin yasa yay haka, bai taɓa ganin Moon ta fito ba sai ranar data fito ciyan ice cream,Duk Abinda take akan idanunsa, tunda idanunsa suka sauka akan yaji soyayyar yarinyar ta sauka a zuciyarsa kuma ya ɗauki alwashin babu mai raba sa ita.
A ranar da daddare aka kashe iyayen Moon wanda tunanin kowa ƴarsu amma asalin iyayenta suna Barno, akan idanun Deen aka cillo Moon daga upstairs ta window bai ƙasa gwuiwa ba yaje ya ɗauke ta ya koma inda yake da zama.
Alrdy an ɗaura auren na da Nana khadii dan haka mun shirya da sunje zan buƙaci siyan Nana, ban taɓa baƙin ciki Auren ta ba kullum sanya mata albarka nake,ina mata barazana koda wasa kada ta bawa wani kanta sbd nasan akwai igiyar aure na a kanta, hatta zuwan Deen Niger nasan komai,kuma abin mmki ranare da aka ɗaurawa Deen Aure da Moon real father ɗinta yana wajan shi ya bada sadaki ma, Deen ya daɗe da bani Wannan bayanin yace idan ya samu damar faɗa da kansa to idan bai samu nina isar gareku, kowa yasan Deen bai son shiga jama'a bare ai photonsa ya ɗura sa a media hakan yasa su Oga Taju suka amince dashi sbd basu san matsayinsa ba, dukkan kuɗin da Deen yake samu baya cin ko kaɗan baya haɗasu da kuɗin sa na halal yanzu haka kuɗin sunkai 50.5m. Shiru parlour'n ya ɗauka bayan Ammar ya gama bada labarin, kowa da abinda yake tunani a ransa musamman Sarki Aliyu Al'amin wanda ya tafi tunanin abubuwan da suka huce na shekaru masu yawan gaske, kallan kallo aka shigayi tsakanin Moon da Fulani da Sarki Aliyu Al'amin, Faizak kam yasan yadda yake jin Moon a ransa zai wahala ace ba jininsa bace musamman zallar kamarta da Sarki Aliyu Al'amin daya bai yana, Murmushin jin daɗi Besty yay domin ya tabbatar gudan jinin nasa gwarzo ne kuma zai girbi dukkan abinda ya shuka a lahira halinsa na kwarai zai bisa, Numfashi Besty ya sauke yace "Ita Nana khadii tana ina" sunkuyar dakai Ammar yay yace "na kaita gida bayan na ɗauke ta sbd juna biyu da take dashi,amma yanzu na maidata gidana bayan an mata bayanin komai" jinjina kai yay yace "Allah ya raba lfy" aka amsa da Ameen, jin shirun yay yawa yasa Besty ya numfasa yace "Ina ganin ita Maimunatou tunda ta fita a takaba sai a bata wani ta aura ko kuma takoma makaranta" Murmushi Sarki Aliyu Al'amin yay yace "ita tace su take ta maye gurbin tsuhun mijinta,ta zama sarauniyar Nufaz" baya kaɗan Besty yaja cike da jin daɗi da kuma murna yace "zan so hakan,amma ki fara tunanin future naki mana, You have to be Educated, ki zama big lawyer mai zaman kanta after nan saiki zama Queen" kanta a ƙasa tana jin zuciyarta na mata zafi da kuma tsoya duk abinda take cikin dauriya take yinsa, wasu hot tears ne suka fara shatati a saman fuskarta da ɗan sauri Sarki Aliyu Al'amin yace "Go inside.." harga Allah bai son ganin kukan Autar tasa,kamar jira take ta miƙe da sauri tana toshe bakinta sbd kukan daya tawo mata.
"Zata koma karatu a ƙasar Paris ƙilan hakan yasa ta samu sauƙi a ranta" da sauri Faizak yace "Abba tayaya tana mace zata bar ƙasa ita ɗaya..?" Kallon da Sarki Aliyu Al'amin yay masa yasa yay saurin faɗin "tuba nake Allah ya huce Sarkin Musulmi" cikin Ƙasaita yace "kaje wajan sarkin Aska ya kwashe wannan sumar" miƙewa yay domin bai son yi masa gaddama, yana fita Sarki Aliyu Al'amin ya kalli Ammar tare da matayensa yace "kowa zai iya tafiya" miƙewa sukai ɗaya bayan ɗaya kowa da shigar alfarma suka nufi falt ɗinsa, Fulani taso zuwa wajan tilon ƴarta amma tsoran kada ace tayi rashin kunya yasa ta hqr, bayan tafiyar su Besty yace "Ina jinka" cikin ƙasa da Murya Sarki Aliyu Al'amin yace "Daman ina son kafin tafiyarta na aura mata faizak,amma bana son ɗura mata nauyi mai girma a kanta tunda is still young ba komai zata iya ɗauka ba, shiyasa nace bari na nemi shawara a wajanka" cikin nutsuwa da Ƙasaita Besty yace "Uhm, zaifi kyau ace ta kammala karatun afti nan sai a fara preparing na auran,amma a farayin Engagement nasu zaifi"
Murmushin jin daɗi Sarki Aliyu Al'amin yay yace "nice idea,kasan tun tana zanin goyo aka bawa Faizak aurenta rashinta yasa aka hqr da mgnar kuma har yanzu yaƙi Auren" Besty yace "ikon Allah daman ana haka?" Sarki Aliyu Al'amin yay dry yace "Eh sosai ma, mu fulani haka muke ana haifar yarinya aka wanke ta a za'a ce an bawa wane ɗan gidan wane,to yarinyar na ɗan girma duk wahalhalun yarinyar zai koma kan saurayin,tana shekara 15 uban yaro zai siyo goro da alawa ai ɗaurin auren, za'a ɗauke ta akaita koda kullum zata gudu sai an mayar da ita gidan miji a haka hatta saba,amma Fulanin Adamawa sunfi yin wannan" Besty jin abun yake kamar almara..A hankali ya buɗe ƙofar ɗakin tare da shiga ya rufe ƙofar, kanta ta ɗaga suka haɗa ido da sauri Moon ta ɗauke kanta daga garesa, idanunsa a kanta yace "Me kika zaɓawa kan ki Maimunatou?" Shiru tai masa domin ita yanzu duk wanda yace tai aure kallon mara hankali take masa, burinta ɗaya tayi tabar ƙasar nan ko zata ji sauƙin wasu abubuwan, ƙasa yay da murya sosai yace "You have to think, shawara nake baki dole kicire mutuwar nan a zuciyarki mun riga munyi rashi, Aliyou bazai taɓa dawowa ba" kuka ne ya ƙwance mata tace "Dan Allah Yaya Faizak ka daina ambatan mutuwar nan, zuciyata zafi take sosai ji nake kamar nima zan mutu" bai ce mata komai ya juya yabar ɗakin,domin sam baya son jimawa tare da ita, kullum soyayyarta yawa take masa a rai,yay shiru sbd rasuwar Aliyou bai son aga rashin kyautawarsa.
Suna zaune saman danning Area suna yin lunch kowa da abinda yake tunani a ransa,time to time Fulani idanunta na kan yarinyar ta,so take ta nemi izini ganin Sarki a wajan Mai babban ɗaki,tana su tattauna dashi akan ƴar tasu,bayan sun kammala Besty da Yayinda sai Nene wacce yanzu ko mgn ba tayi sai dai tabi kowa da ido, har airport Sarki Aliyu Al'amin yay masu rakiya kana ya juya zuwa cikin Masarauta.

    *_RANA KUN POSTING SATURDAY AND SUNDAY_*

****
Zaune take a cikin office ɗin Doctor Joseph yana sauraran abinda yake faɗa, budurwa ce mai kimanin 21yrs fara ƙyakkyawar gaske kana ganinta kasan bata san zafin talauci ba ko kaɗan, Lumshe idanunta tayi tare da juya kujerar kaɗan,tana kar kada key car ɗinta, Doctor Joseph yaci gaba da faɗin "Everyone forgets things at times. How often have you misplaced your car keys or forgotten the name of a person you just met?

Some degree of memory problems, as well as a modest decline in other thinking skills, is a fairly common part of aging. There's a difference, however, between normal changes in memory and memory loss associated with Alzheimer's disease and related disorders. And some memory problems are the result of treatable conditions" ware idanunta budurwar tayi kafin da turanci tace "Kenan bazai iya tuna komai daya huce ba,sai dai abinda zai fuskanta a gabansa? More explanation pls" zare farin eyes glass ɗinsa yay yace "he loses his memory, he can't remember anything about his life, And Normal age-related memory loss doesn't prevent you from living a full, productive life. For example, you might occasionally forget a person's name, but recall it later in the day. You might misplace your glasses sometimes. Or maybe you need to make lists more often than in the past to remember appointments or tasks.
These changes in memory are generally manageable and don't disrupt your ability to work, live independently or maintain a social life" Murmushi kawai tayi tare da miƙewa, sai lokacin na ƙara Kallonta duguwa dai-dai tsayin Moon bata da wani jiki domin shekarunta basu nuna a jikinta ba, Sallama taiwa Doctor Joseph kana ta nufi Male surgical ward, wani prvt room na mutum guda, babu abun babu a ciki saika ɗauka ɗakin mace ne, Yana kwance flat babu ko riga jikinsa kana an naɗe da bandeji, ƙirjinsa ma duk bandeji Yadda yake fidda numfashi da sauri da sauri kuma wahalarce zaka gane ya farfaɗo daga guguwar sumar da yay ya shiga Coma or unconsciousness.

_Unconsciousness is when a person is unable to respond to people and activities. Doctors often call this a coma or being in a comatose state. Other changes in awareness can occur without becoming unconscious. These are called altered mental status or changed mental status_

Ƙofar room ɗin ta rufe tare ƙarasawa inda yake kwance, da alama ya tafi wani tunani mai zurfi ne,cikin nutsuwa taja ta tsaya a kansa tana kallon zallar kyau da yake da shi,taga maza kala-kala amma bata taɓa ganin mutum mai kyau da cikar zati irinsa ba, cikin ƙasa da murya tace "How are feeling now?" Da sauri ya juya ya kalleta tsuru yay mata ido yana ɗan lumshe idanunsa kana ya buɗe su a kanta, ganin Kallon da yake mata yasa tace "Ya jikin naka?" Zabura yay tare da cilli da drip yana yana zuwa wajanta yasa hanunsa ya fisgota ta faɗa jikinsa, rungome ta yay sosai ya shiga sauke ajjiyar zuciya kafin cikin rawar murya irinta marasa Lfy da wanda basa cikin hayyacinsu yace "Mai...Mai.. Maimunatou...

Comment
Vote Please

MOONWhere stories live. Discover now