chapter 1-2

3.4K 255 12
                                    


*_Free book_* _Allahamdulillah ina gdy da Allah subhanahu wata'ala Rubutun littafi kamar kwanakin rayuwa ne,abinda zai faru da mutum yau daban,abinda zai faru da mutum gobe daban,haka nan kuma babu wanda yasan abinda zai faru da mutum jibi,labarin littafin haka yake,abu ɗaya marubuci ya sani tsara labari daga farko zuwa ƙarshe,rubutawa kawai ya rage masa, littafin *HUMAN TRAFFICKING* ina cikin typing littafi na Uncle ne labarinsa HUMAN TRAFFICKING yazo min,bansan yaya ne zan faɗa maku ba,amma HUMAN TRAFFICKING yana ɗauke da manyan ƙalubale masu hargitsa tunanin mutum kuma wanda suke faruwa cikin al'umma, wasu na tunanin kamar an daina SAFARAR MATA NE a'a har gobe a nayi kawai sallon yadda suke abunne ya sauya,ban fara rubutawa ba sai da gama searching akan yadda akai SAFARAR da manyan DRUGS da ake amfani dasu,da kuma mutanan da suke siyan wanda akai SAFARAR tasun,da kuma keɓantaccen guru da aka ware domin su,zan iya cewa Wannan littafin yana ɗaya daga cikin littafan dana fita naje wajan police headquarters da kuma domin jin cikakken bayani akan safarar mata, tabbas da zanyi Wannan littafin na kuɗi zan samu ƙarowa dashi amma hakan ba buri na bane,ina son kowa ya karanta ya kuma amfana_

_Warning HUMAN TRAFFICKING mallakin mallakar Nieemerh ne,kada kayi gangancin sauyamin labari,ko kuma ka ɗauki wani part na cikin labarina ba tare da sani na ba,idan kunne yaji...!!_

_Gareku Readers bazan buɗe wani grp akan wannan littafin ba,dukkan wanda ya karanta yayi ƙoƙarin share ɗinsa zuwa wani GROUPS ɗin sbd ALLAH da kuma Manzon sa,dan ALLAH ko daina tambaya littafaina kuje wattpad kuyi searching nimcyluv zaku ganni, masu tambayar Uncle ne..! na kuɗi ne akan 300 0116886423 Sulaiman Naima s union bank kayi subscribe saika tura evidence of payment to 08119237616 Salon littafin Uncle ne na daban ne, ahhh littafin HUMAN TRAFFICKING ba kullum za'a na posting nasa ba,sbd littafin kuɗi da nake,duk bayan ƙwana biyu zannayi idan kuma na samu time zaku iya jina kafin lokacin,tabbas idan banga comments a ko wanne GROUPS dana tura ba,zan daina posting a whatsapp zan koma wattpad sai dai zaku ke ganin link ɗin wattpad ɗin,in kuka danna chrome ko Google zai buɗe ga wanda basu da wattpad kenan,ina maku sahihiyar ƙauna ina alfahari da masoya na a duk inda suke🌚Sarauta da ɗura al'ƙalaminta a littafin SAFARAR MATA Ubangiji ya bani damar rubuta dai-dai_

*_Bisimillahir rahmanin rahim_*


A hankali da fito daga cikin gidansu zuwa tsallaken titi,tana sanye da riga da wando na Pakistan an ɗaure mata sumar kanta da ribbon wanda ya sauka gadon bayanta,hannunta ƙaramin ta tura cikin ma dai-dai cin bakinta sai juya manyan idanunta take,wajan mai ice cream ɗin ta ƙarasa tare kuntu gefen rigar ta ta ciro sabuwar ɗari biyar,ɗan washe bakinta tayi wanda suke jere da fararan haƙora tare da miƙa masa kuɗin hannunta tace "kaban ice cream" baki ya buɗe tare da yin dry yace "ƴar yarinya mene sunanki?" rarraba idanunta tayi kafin tace "Moon" kanta ya shafa yace "a'a Moon ai ba suna bane,a makarantar yaya ake ce maki?" Ice cream ɗin da yake bata ta amsa kafin tace "Maimunatu Abdullah" tana faɗin hakan ta juya a hankali tare da tsallaka wa titin daya raba tsananin gidansu,kai tsaye wajan get ta nufa tana ta kallon wani getman na gidan dake farcing gidansu,knowking tayi da sauri mai gadin ya buɗe mata ƙaramin ƙofa kallonta yyi da mmki yace "Moon yaushe kika fita" ƙaramin yatsanta ta ɗura a ƙaramin bakinta tare da faɗin "shiiit" bai ƙara ce mata komai ba ya bata hanya ta shige,direct lambun gidan ta huce ta zauna saman wata ƙaramar kujerar dake ƙarƙashin bishiyar mango, lumshe idanunta tayi cikin nutsuwarta ta fara shan ice cream ɗin tana gamawa ta miƙe ta nufi cikin gidan.

Cikin sanɗa ta shiga cikin main parlour ajjiyar zcy ta sauke ganin babu kowa ciki,tana ƙoƙarin zama taji anyi sama da ita, tsoro ne ya kamata ta buɗe baki zatai kuka ganin Dad ɗinta ne yasa ta saka dry ta nayi tana jan gemunsa,sauketa yyi yace "Moon ina kikaje Mamynki tai ta cigiya?" Idanu ta fara rabawa domin tasan idan tace waje ta fita an tai mata faɗa kenan,kallonta yyi yace "my dear gobe zamu bar wannan ƙasar wacce ƙasa kike sha'awar zuwa?" cikin murna tace "Dad ina son Paris" kanta ya shafa yace "ina kika san Paris kina ƙaramarki Moon?" juya idanunta tayi tace "Dad Paris is my dream city ina son zuwa"

MOONWhere stories live. Discover now