32

3.1K 55 10
                                    

💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫

_MASIFAFFIYAR KAUNA_

✍🏾M SHAKUR

EPISODE 3️⃣2️⃣

Gyadamai kai kawai yayi batare dayace komi ba, yana tuki amman yana lura dashi zafi yakeji amman baison yanuna hakan yasa idanunshi nakan hanya yace "dazaran kaje gida kasha maganin nan within an hour zaka nemi zafin karasa, nan da 2 zuwa 3days zai warke, next time don't get into fight again I know it was fun" dan lumshe ido yayi yabude saikuma ahankali yace "I've heard" wayanshi ne yashiga ringing dake in between sit din gaban atare suka kalli wayan dan shima yazaci tashice dan ringing tone na iPhone ne ganin Dad dinshi ke kiranshi yasa yadanja tsaki yadaue kanshi daga kallon wayan, harta katse another kiran yashigo Mum, itama ta katse bai daukaba, saikuma Dad yasake kiranshi ganin baida niyyan dauka yasa ahankali yace "please pick up sunga dare yayi basu ganka bane" mika hannu yayi yadauki wayan daidai ta katse saiga wani kirin kuma yana shigowa hakan yasa yakai wayan kunne yace "Dad what" jim yayi yana sauraron Babannashi saikuma adan kubure yace "am on my way back home already" sanan ya katse wayan ya jefar yana maida kanshi jikin kujera yacigaba da nunamai inda zai bi har sukazo ta wajejen anguwansu amman ba'a kai layinsu ba sanan yace "dan gangara gefe kai parking" ahankali yace "but ai nan kan hanya ne" "don't worry am close to gida I can manage" gyadamai kai yayi Tobi yace "lemme call Uber yazo yadaukeka dan ana ganinka ansan you don't belong to the street of Lagos this ghetto Boys will rob u" yana maganan yana shiga app din yakira uber within 5min duk suna zaune acikin motan ya lumshe ido uber direba ya kira bude kofa yayi zai fita da sauri Dr Imam yace "no" dan murmushi yayi yace "i can manage" fitowa yayi yanama uber direba waving hannu hakan yasa yakaraso shima fitowa Dr Imam yayi, uber direban nazuwa Tobi yaciro kudi about 10k yabama uber direban yace "take my man to his hotel, idan y sauka just call me i will end the ride" sanan yadago yajuyo yana cizan baki, hannu Imam yabashi yace "I really appreciate this" gyadamai kai Tobi yayi, ahankali Dr Imam yace "please take care" I will yace sanan yajuya yashiga mota shima Dr Imam yashiga motanshi yanabin Tobi da kallo he's one the the nicest person yahadu dashi a lagos, jan motan Tobi yayi yamike sukuma suka juya suka fita daga layin.

Gidansu yashiga yana addu'a Allah karya hadu da iyayenshi sukaga riganshi da jini ai saisun sunyi panicking halama akara hanashi fita, saida yay parking yaga basa tsakar gida sanan yabude motan yafito, da sauri guards sukazo kafinma su iso yace "nobody should come here dissmiss" bacemai sukayi, sanan yabude boot ya kwaso abinda yasayo ma Boy, da ledojin yay amfani ya kare inda jinin yabata ariganshi yawuce flat dinshi yana bude kofa ya shiga yaga babanshi azaune akan kujera faduwa gabanshi yayi yawani batarai tareda saka leda yasake rufe wajen da kyau, Dad yajuyo yana binshi da kallo yace "iyye I can see anyi aski an chanza style, your face looks very fresh kaje spa ne" dauke kai yayi yace "uhn" sanan Dad yay murmushi yace "dakace kanaso damun kirasu home service suzo sumaka" shiru yayi yana tsaye inda yake baice kalaba Dad dake kallonshi yace "you look very dirty Tobi kaman wanda yaje yay dambe jibi kayanka" yanuna kayanshi da duk yabaci da kasa hakan yasa yace "are you investigating me newai Dad"? Da sauri Baban yace "no Son, just saying it ne sabida naga kai datti" tabe baki yayi yace "i played ball ne" gyadamai kai Baban yayi yace "i see meka sawo a ledojin nan" yanuna ledojin hanunshi, sake rungume ledojin yayi yace "is not mine, I actually got some clothes for Boy, sai gobe zan bashi" sosai Babanshi yay murmushi yace "Tobi u really like that boy, dats the first gift dana taba baka naga kanaso sosai" wucewa yayi yay stairs da sauri yace "i am sleepy when u are done ka kashe tv" binshi da kallo yayi yace "but Son i actually come muyi kallon match tare" "not interested Dad, gud night" night babanshi yace ahankali yana kallonshi, shiga dakinshi yayi yamaida kofan yarufe ya danna key da sauri yana cije lips yanabin dakin da kallo ganin Boy bai gyaraba kaman ma baima zobane kwata kwata ba yau.

Wanka yashiga yayi da hot water sanan yafito ya chanza wasu kayan zuwa pj, yarike magungunan shi yay dinning abincin daya gani wajen yabude yadan tsakuri amalan kadan dan bayawani so kuma yasan da gangan Mum takawomai tanason yay kibane yaci sanan yasha magungunan yatsiyaya juice a glass cup yadawo falo ya zauna yana kallon tashan news din dake aiki wanda ta tabbatar Dad ne yasaka danshi he hardly watch news, yana sipping din juice din yana chanza channel hakanan yake mamakin maiya hana boy zuwa yau aiki, but deep down yasan it will be something daya hanashi zuwa, dan tabe baki yayi sanan yay murmushi tuna irin fadan dayayi dazu, ba yana gayama su Dad yanada karfi basa yardaba just look at the gang he took down shi kadai dan dat Dr babu wani abun arziki daya tabuka. Sai wajajen one sanan ya kashe komi yawuce sama yafada gado sai bacci.

MASIFAFFIYAR KAUNAWhere stories live. Discover now