5

1.2K 34 0
                                    

💫 _DISASTROUS LOVE_💫

          _MASIFAFFIYAR KAUNA_

 

          ✍️M SHAKUR

EPISODE 5️⃣
_FREE PAGE_

Karban takardan Baba yayi kaman mara lafiya yajuya yana tafiya ahankali yafita daga dakin yay reception, tsayawa awajen yan kati yayi yabude  kati da folder, folder dubu daya, karamin kati kuma  dari uku yarage duka kudin saura dari bakwai, bai karayaba yarike komi a hannunshi yawuce Pharmacy ya tsaya gaban kanta tareda mika musu takardan da Dr yabashi, gani yayi anciro gorunan ruwa, allurai daban daban dawasu magunguna ankawo gaban table anyi wani tabe tabe a computer sanan aka fitomai da wata yar takarda, namijin wajen ya mikamai yace "Baba ga takardan biyan kudi je chan wajen account kabiya kudin saika dawo mana da takardan biyan kudin saika amshi magungunan katafi" karban takardan yayi ya kalli kudin dake rubuce awajen dubu takwas da naira Dari da talatin wani irin mugun faduwa gabanshi yayi ahankali yajuyo ya kalli saurayin dahar ya juya yakoma wajen zamanshi, dan gyara muryanshi dayaji ta shakemai yayi yace "Yallabai jimana" tasowa saurayin yayi yazo yace "gani Baba" cikeda damuwa Baba yace "kaga y'ata ce ba lpy, rai a hannun Allah, duka duka yanzu chanjin hannuna basufi dari shida ba, nace kozaka bani abubuwan nafara kaima likita afara mata treatment, inyaso kafin mubar nan wajen saina biya kudin daga baya yanzu dai afara bata taimakon gaggawa" dan murmushi pharmacist din yayi yace "Baba kenan, kayakuri Baba bama haka awanan asibitin" yanamai maganan yashiga attending to wasu mutane dasukazo wajen siyan magani, gajiya da tsayuwa Baba yayi awajen kafin ahankali yadaga kafafuwan shi dayaji sunmai nauyi sosai yawuce yafita, ahankali yake tafiya haryakai wajen parking space, sabida kar mutane su ganshi yasa ya zaga ta gaban motoci yazauna kan dakalin wajen yay shiru yana kallon folder da katin daya bude mata ga sunanta ajiki baro baro, Fatima Zara'u Muhammad, yarinyar nan tun tana yarinya wahala take yanzu gashi tana ciwo baida kudin kulada ita, jiya da yafita neman kudi yaje babu wanda yasani dayabashi kudi koda sisine, Rukayya ko yasan ko Mutuwa Zara'u zatayi bazata taba cire kudin ta tabada ba, dudda yasan itama ba lallai yasamu irin wanan huge kudin a hannunta ba amman bazai rasa yarsu dubu dubu biyuba, toya fita yay bara ne? Ya tambayi kanshi, but ayanda duniya ta chanza babu wanda zai ganshi yanzu haka ya yarda yabashi kudi yayi tsaf tsaf dashi gayar shaddar shine tsaf tsaf ne za'a yarda abashi taimako, jiyayi wasu hawaye masu shegen zafi sun zubomai yakai hannu ya share amman suka kasa dena zuba hakan yasa kawai ya barsu suka slcigaba d kwarara.

Agogon hannunshi kirar iwatch dake daure a wrist dinshi ya kalla about 25min kenan Baban Patient dinan bai dawoba, dagakai yayi ya kalli yarinyar ganin har yanzu she is stable bacci take yasa yadauki stethoscope dinshi yarataya awuya ya kalli nurse din dake wajen yace "stay with her, idan her Dad yakawo magungunan call me, idan ta tashi call me" yana maganan yajuya yafita daga dakin yay hanyar fita waje batare daya kalli dumbannin mutanen dake GOPD ba, tun 4 nasafe ya shigo asibitin nan emergency baici komiba har yanzu yunwa yakeji sosai by 1 yakeso yatafi gida yahuta yay bacci, wajen parking space yakarasa yay wajen wata hadaddiyar Black suv bude motar yayi da key dinshi sanan yamika hannu yadauko wani haddedden moderate flask dake kan dayan sit din gaban mota, bude marfin flask din yayi da saurinshi sabida tsabaragen yunwan dayakeji yakai flask din bakinshi yana kwalkwalan coffee dake cikin flask din daya hada da asuba dazai fito, saida yay kusan rabin flask din sanan ya sauke daga bakinshi yana sauke ajiyan zuciyan gajiya, saida yadan huta sanan yadaga flask din zai kara komar dashi baki kaman ance ya kalli bangaren damashina ke parking ya hango wani mutumi dan magidanci dabai ganin fuskarshi da kyau zaune gaban wata mota a side dinshi rikeda folder a hannunshi yana share hawayen dake bin fuskarshi looking so confused and sad, jiyayi zuciyarshi ta tsinke dan haka Allah yayishi yanada tausayi sosai, kasa cigaba dashan coffee shi yayi dudda uban yunwan dayakeji, maida flask din yayi ya ijiye,  yamaida kofan yarufe yamata key sanan yataka ahankali yana tafiya  harya isa inda Baba yake zaune kanshi akasa yana share hawayen dake zubomai baima lurada wani yazoba dan hankalinshi yay nisa yana tunai. "is everthing okay Sir, mesa kazo nan kazauna kana kuka"? Wata zazzakan muryan da Baba yaji akanshi namai magana cikeda kamala hakan yasa yadago kanshi da sauri da idanunshi dasukai jajir yahada ido da Dr daya rubutamai maganin Zara, Dr na ganin Baba yaganeshi shima at a spot ai mutumin dazune Baban yarinyar dake emergency ward, ganin Baba yace "what is it Sir? Mesa kazonan kake kuka ina magungunan danace kasayo"? Dr yay tambayan yana kallon Baba yana kara nazarin yanayinshi, baki Baba yabude zaiyi magana saikuma wani irin takunkumin bakin ciki yakara tokaremai wuya wasu hawayen suka sake zubomai, kaman wanda notin kanshi ya kwance baisan lokacin daya kwaso yan chanjikan dasuka ragemai ba a aljihu yanuna ma Dr idanunshi sunyi jajir ga hawaye sun cika idanun kana ganinshi kasan he is pain yace "kagansu wanan ne kudin danake dashi gaba da baya, banda hanyan samun wasu, Zara'u na nachan kwance rai a hannun Allah an rubutamin maganinta nakasa saya sabida bandashi, bandashi, ina zansa raina? Asibitin gwamnati ma nakasa biya ba dole nazo nan na zauna ba likita" yanda yake maganan kaman ma wanda baya cikin hayyacinshi tsabagen damuwa yasa Dr yacigaba da tsayuwa a inda yake batare dayay motsi ba yay shiru yana kallonshi kawai, hawaye Baba yasake sharewa yace "Kaga Zara'u itace y'ata ta farko, tunda yarinyar nan tazo duniya bata tabajin dadi naba ni Mahaifinta, bana saya mata kaya, kaya irin nakowace yarinya budurwa datake tasowa, Zara'u bata tabamin korafi ba kokuma tace saina mata, yarinyar nan bata taba bude baki ta tambayeni abuba, kotamin korafi kotanunamin bacin rai, banmata kayan salla, bansiya mata takalmi, babu abinda nakema Zara'u sabida bandashi, yarinyar nan bata taba yimin kocemin Baba yimin kaza ba, yarinyar dake tausayin mahaifinta nake wahalarwa haka gashi yanzu ma datake rashin lpy nakasa mata komi, wlh ban cancanci zama mahaifint........" kafin Yakarasa maganan Dr ya tsugunna da sauri yakai hannunshi kan bakinshi hakan yasa Baba yay shiru yana kallon kyakkyawan fuskar Dr dake sanye da glasses, cikeda tausayi Dr yajanye hannunshi daga bakin Baba ganin yadan natsu yana kallonshi, hakanan yaji Baba ya mugun bashi tausayi, ahankali yace "Sir ba'a magana haka, Allah daya baka yarka yasan ka chanchanci zama mahaifinta ne saisa yabaka ita a matsayin y'a, sanan aganina godiya yakamata kama Allah daya baka y'a irin wanan wanda tun anan duniya take jinķanka, and just because bamu bama yaranmu abinda yakamata mubasu ba, or bamu wadatasu da kayan alatun duniya ba ba doesn't mean we are not good fathers to them, karka kara magana haka Sir, I know yarka na alfahari dakai, and stop crying, yanzu dai nawane kudin magungunan"? Ahankali Baba yace "8150 sukace" gyadamai kai Dr yayi sanan yamike tsaye yakai hannunshi bayan wandonshi  wallet dinshi yaciro yabude yazaro wasu kudade yan dubu dubu dashi kanshi baisan yawansu ba ya tsugunna, hannun Baba yakama yasaka kudaden aciki yace "jeka sayo magungunan kazo mufarama yarka treatment ko" yay maganan yana sakinma Baba coolest smile dake comforting any kind of heart,  wani natsuwa Baba yaji ya shigeshi tareda sake rike kudin da kyau yana kallon fuskan Dr ya nisa zai bude baki yay magana wayan Dr dake aljihun lab coat dinshi yahau ringing ciro wayan yayi yana mikewa tsaye yana gani inda ake kiranshi yatashi da sauri yajuyo ya kalli Baba yace "get magungunan now ka kawomin she's convulsing again" da gudu yajuya yabar wajen shima Baba sake damke kudin yay gam gam ya tattare su folder yatashi yay pharmacy harda gudun shi.

MASIFAFFIYAR KAUNAWhere stories live. Discover now