Na saka mashi dariya nace Yaya muna fa tare kullum to meye na wani sai na koma can duka daya ne......

Yace a'ah wallahi ba daya bane yanzu ai kinga bazan iya sakewa nayi yanda nake so ba......

Nace eh hakane ai kuwa yazo zaiyi hugging nawa sai ga Kausar yace oh to kin ga abunda nake cewa ko?

Na daga gira nan ya fita ya barmu,Kausar nata hada kayanta shirin tafiya nace ai ba zaki barni ba nima zanje yawon arba'in kaduna saboda idan kika tafi kila sai nayi kuka.....

Tace bari Andeeja idan naje insha Allah ai next dawowa shikenan na dawo Abuja kinga atleast muna Country daya.....

Nace wallahi zanyi missing naku ku duka,muna ta hira bayan kwana biyu muka je parlour din Daddy mana.....

Hajiya tace Daddy dama Kubra nace ta shirya taje yawon arba'in sai taje Kaduna daga can taje Abuja.....

Idan ta dawo sai a mayar da ita gidanta,Daddy yace wai amma kam zasu bamu kewa sosai....

Nasan su duka 3 zan nema na rasa,Kausar tace Daddy mu biyu ne fa zamu tafi,yace a'ah ai da kina tunanin Abbaty zai tsaya nan ne?

Jiyan nan ya zo wai yaushe zamu mayar da Kubra na rufe ido da tafukan hannuna wai Yaya yana saka ni jin kunya....

Dama na hada kayana driver zai sauke mu Kaduna Kausar ta shiga train zuwa. Abuja idan ta kwana daya,yana shigowa gidan,ya samu Daddy da Hajiya suka yi masa tuni dama sun gaya masa.....

Ya marairace yace haba Daddy mana yanzu sai ta tafi,Hajiya fa bata tausaya mun ne dan Allah ku bari daga baya zan kaita.....

Hajiya tace idan bata nan ne zaka rasa ne?Akwai abinci zan dinga aika maka idan ba zaka iya dinga zuwa ba,duk safe kana fita zan aika a gyara maka gidan....

Daddy na ta dariya yace Hajiya da Abbanta bansan me zan fe muku ba,Daddy yayi gyaran murya yace Abbaty kayi hakuri taje taga Mamanta ko sati daya tayi sai ta dawo week din da ta dawo zata koma dakinta insha Allah......

Hajiya tace kayi hakuri kaga tana kewan Mamanta ne sosai ai yakamata mu barta tunda Maman tana nuna kawaici ka gane?

Yace to na yarda Allah ya dawo da ita lafiya,fuskarsa ba yabo dai ba fallasa,yana shigowa ya sameni ina breastfeeding Abul khair ya harareni...

Nace Herbeebina sannu da zuwa i missed you so much,yace ba wani missing dina tunda zaki tafi ki barni.....

I pouted nace ka shirya mu tafi kaga Mamana dinne taki tazo ganinta kawai zanyi na dawo,kwana nawa ka bani?

Yace  sati daya kuma Daddy ya tabbatar mun kina dawowa zaki koma gidanki,nayi murmushi nace to Dr na na yarda nayi pecking nashi....

Nace to zo muci abinci dama kai nake jira duk yunwa ya isheni,yace ayya sorry My Baby me yasa baki mun waya ba....

Nace ai Abul ne ya hanani komai yau,yace sorry kin gama ne?Nace eh nayi zipping rigana na sauko na zauna.....

Na bashi Abul nayi serving ina bashi a baki nima ina ci,yace Baby yau ba fada ko?

Nace na isa ni missing dinka da zanyi ya dameni tun ban tafi ba kodai na fasa ne Yayana?

FOREVER YOURSWhere stories live. Discover now