Mammy ce tsaye gaban getman tace "Iliya kana ina kabar Moon ta fita,ka riga kasar tunda muka zo ƙasar nan babu inda aka taɓa barinta ta fita ko?" Cikin girmamawa yace "wlh Hajiya na shiga ɗaki kenan ɗaukan redio don jin labarai" juyawa tayi tace "koda wasa Moon ta ƙara barin gidanan ranka zai ɓaci" bayanta yabi da kallo yana mmkin dalilin daya sanya basaso yarinyar tana fita bayan yafi kowa sanin yarinyar a takure take.

Gidan dake farcing gidansu Moon ɗin mai gadin gidan daya kasance matashi fari tass kyakkyawan gske,yyi murmushi tare da ɗaukan wayarsa wacce ta kasance ƙarama ya kara a kunansa,babu jimawa daga can side ɗin akai picking call,cije baki yyi kafin a hankali yace "sai yau yarinyar ta fito,amma tayi ƙarama da yawa,banjin takai 10yrs ma" mutumin da yake a can ɓangaren ya kalli tarin matan dage gabansa yace " babu ruwanka da kankantarta kayi abinda yake dai-dai" jinjina kai getman ɗin gidan yyi ba tare kuma da yace komai ba ya kashe wayar tare da tsorawa ƙofar gidansu Moon idanu.

Mamy na shiga cikin parlour ta samu Dad da Moon suna game kowa da remote a hannunsa,game ɗin ta kashe tare da kallon Moon tace "Ohh ice cream ko? Nace ice cream kika sha ko Moon!!?" ta ƙare mgnar tana ɗaga murya,Dad ne ya kalleta yace "uwata ice cream kika sha da gske?" Kaita ɗaga masu alamar "eh" yace "Moon ina kika samu ice cream?wane ya baki" hawaye ya fara saukar mata a fuska kafin ta ɓoye jikinta a jikin Dad tace "Kuɗi na gani a dressing mirror shine na ɗauki ɗaya naje titi na siya" zaro ido Dad yyi yace "what!? Kin kashenu Moon,kin rugazamin duk wani plan nawa, shikenan tamu ta ƙare" yana faɗin hakan yyi saurin miƙewa tare da nufar part ɗinsa,Mamy ma Moon ta kama hannu Moon suka shige nata part ɗin zcyarta sai bugawa take.

Dad na shiga bedroom ɗin sa ya buɗe wata box ya ɗauki wata ƙaramar gun ya zuba mata bullet,yana gamawa ya sanya bindigar a cikin wandonsa kafin ya ɗauki wani dairy ya fara rubutu a jikinsa,yana gamawa ya sanya dairy'n a cikin box ɗin kafin ya haura upstairs,ya buɗe ƙofar kitchen tare da buɗe window na kitchen ɗin ya cilla box ɗin baya window'n ,Mamy tana shiga tace "Moon kina wasa da lfyarki ko? kin san idan kika sha abu mai sanyi baki da kwanciyar hankali ko,ciwon nan a jikinki yake kinfi kowa sanin wahalar da kike sha, muna da kuɗin daza mu siya maki ice cream da duk wani abu da kike buƙata,amma bamu da kuɗin daza musiya maki lfy,kina kallo a idanunki ƙanninki ya mutu idan kema kinfi son ki mutu shikenan,sai na zauna bana da kowa,dan Allah Moon kii ki yaye komai mahaifinki yake dashi na kine,damuwarsa inda zamu kaiki ki samu lfy tabbas ko nawa muka mallaka zamu iya ƙarar dashi indai zaki samu lfy, dalilin ki munata yawo ƙasa-ƙasa tamkar marasa gsky" shuru Moon tayi tana kallon Mamy kafin tace "ban ƙarawa" murmushi Mamy tayi tace yimin al'ƙawari" murmushi tayi wanda ya haifar da lumawar dimples ɗinta kafin ta lanƙwasa ƙaramin yatsarta tace "nayi maki" peak ta bata a kumatu kafin tace Ohh yaaa jeki ƙwanta ki huta" kallon Mamy tayi tace "Mamy ina teddy na?" Tace "yana bedroom ɗinki" fakar idanun Mamy tayi ta shige bedroom ɗinta tana zuwa ta buɗe wardrobe ta ɗauki wani album tayi waje da sauri,tana zuwa bedroom ɗinta ta ɗauki ƙaton teddy ta buɗe zip ɗin jikin teddy ta zura album ɗin.

tana gamawa ta ƙwanta a ƙaramin bed ɗinta da sauri ta tashi ta nufi part ɗin Dad ɗinta,zaune ta samesa da Kur'ani a hannu yana karantawa,zama tayi kusa dashi tare dasa hannu ta dafe haɓarta,kallonta yayi kana ya saka hannunsa ya cire nata hannun da tayi tagumi dashi yace "Moon wannan tagumi kamar ance wani ya mutu" murmushi tayi masa kafin ya subaci goshinta yace "jeki ƙwanta"

Mai gadin ne zaune yana kallon gidansu Moon har dare yyi,horn yaji anyi a bakin get ɗin,yana zaune bashi da niyar tashi daga wajan har wani matashin saurayi ya fito daga cikin gidan ya ƙarasu wajansa yace "kai mene aikin ka ne?" Ya faɗa yana kallon Deen wanda yake zaune ya lumshe idanunsa,ware idanunsa yyi ya sauke su akan Farouk,bai ce masa komai ba ya miƙe tamkar baiso ya ƙarasa gaban get ɗin,ya buɗe get ɗin wata ferari ce ta shigo cikin compound ɗin gidan,a dai-dai inda Deen yake tsaye ya tsaya yace "Deen lfy inata horn shuru?" Kallonsa yyi tare control na kansa yace "ina bacci ne" kai ya jinjina yaje yayi parking motar, Farouk wani kallo yyiwa Deen tare faɗin "kazo hadda kuka kana neman aiki ko gadine amma yanzu kanawa mutane wulaƙanci,wlh laifin Abba ne da yake barin ƙasƙantattu irinku a cikin gidan sa" yana faɗin hakan ya shige cikin gidan,wani murmushi gefen baki Deen yyi kafin ya ciro wata babbar wayarsa ya fara latsawa,I.G ya shiga ya fara ganin photo nan ƴan mata,kafin yaci karo da wata da aka sanyawa suna Nana khadii, message ya ajjiye mata na fatan alkairi, kafin tai masa reply da gdy, offer ya tura mata ta aiki idan tana buƙata amma aikin na cikin gida ne,duk wata kuma za'a na bata 100k,yana gama yi mata bayani yay offline.

Misalin 2 na dare,aka fara bubbuga get ɗin gidan,Iliya yana tsaka da bacci yaji bugun ƙofa miƙewa yyi tare ɗaukan torchlight ya nufi bakin get ɗin yace "waye da wannan daran?" Daga can waje aka saita Muryar akace "ƙanin me gidanne bai gaya maka jirgina zai sauka cikin dare bane,ka buɗan ƙofa sanyi" shuru Iliya yyi kafin ya ɗauki wayarsa ya kira number Dad switch off,matsawa kusa da get ɗin yyi jin ana ƙara bugawa, a tsorace ya buɗe get ɗin yana buɗe wa aka sakar masa bullet a tsakiyar ƙirjinsa,mutane ne sama da mutum goma suka fara shigowa cikin gidan,ko wannan su ɗauke da ƙatuwar bindiga fuskarsu rufe da wani baƙin yafi,Dad na ƙwance yana bacci shida Mamy suka ji ƙarar bindiga cikin sauri Dad ya sakkowa daga saman bed ɗinsa tare da ɗaukan bindigar sa ya nufi part ɗin Moon,a ƙwance ya sameta ta rungome teddy a jikinta,sanin tana da nauyin bacci ne,yasa yaja mata kofar da ƙarfi ya rufe ta key,komawa yyi yana shiga part ɗinsa suna shigowa upstairs ɗin,a hankali suka fara dudduba ɗakunan amma babu kowa,ta gaban ɗakin Moon suka shige ganin rufe yasa ba suyi tunanin da mutum ciki ba,Mamy dake parlour'n Dad jikinta Duk rawa yake babu abinda take tunani sai Moon, jin shuru Dad bai shigo ba,yasa ta nufi ɗaya ƙofar tana fita Dad yana shigowa,dubata ya farayi, Mamy ƙofar ta buɗe tana fita suna shigowa part ɗin sukaci ƙaro da juna,baki ta rufe hannunta ya fara rawa,komai na jikinta rawa yake, kallonta wani babban mutum yyi yace "ina Moon?"girgiza kai tayi cike da tsoro tace "bata gidan" murmushi yyi yace "ok" Yana faɗin hakan ya sakar mata bullet a tsakiyar kanta,ihu tayi a take kuma rai yyi halinsa, Dad dake cikin parlour'nsa ya saita bindiga jin ihun Mamy da kuma ƙarar bindiga yayi Saurin zubewa wajan tare da rufe bakinsa wasu hawayen baƙin ciki suka fara sauka ta cikin idanunsa,da sauri ya miƙe yace "Moon" yana faɗin hakan ya nufi part ɗinta ta ɗaya ƙofar a ƙwance ya sameta,cak ya ɗauke ta it da teddyn ya nufi wata ƙofa da ita,yana zuwa tana farkawa a bacci baki ta buɗe zatai mgn yayi sauri rufe mata baki, rungome ta yyi sosai a jikinsa idanunsa na zubar da hawaye zafin ya ciri wani ƙaramin ring ya sanya mata a hannunta, raɗa mata wani abu yyi a kunne kafin yyi murmushi,jin ana taɓa ƙofar yyi sauri buɗe window'n ɗakin yana gama buɗewa suna shigowa cikin sauri ya saki Moon ta window ta faɗa ƙasan benen ta bayan gida,hakan kuma yyi dai-dai da lokacin da suka sakar masa bullet ta keyarsa..

Idan kin karanta yyi mki daɗi kiyi share sbd Allah

Sarauta

MOONWhere stories live. Discover now