Baby ya kike ji ne tell me,bakomai Yaya kicking dinnan ne,Ya girgiza kai yace kizo muje hospital kina Labour ne.....

Na zaro ido nace nifa Yaya ba wani labour da nake haba bazan je wani hospital ba,yayi shiru ya kyaleni sai da na dawo idan zanje bayi sai na rike bango......

Dakyar na cije lebe na ce Yayana na rike kunkuru da hannu daya ya taso a rikice yace Babyna menene?

Ya rikeni ya zaunar dani yace kin yarda Labour kikeyi ko tun dazu da na ganki gida nasan labour kikeyi to bana iya tilasta miki......

Ya je ya dauko hospital bag din da na hada tun ciki na 7months,ya ce in tashi mu tafi,Nace Yaya ka barni na huta bazan iya dagawa ba daga zaman nan.....

Yace haba Baby bansan ki da raki ba ya kira Jamila ta dauki kayan ya kamani ya sakani mota yace ta shirya Driver zaizo ya kaisu gida......

Tana ta mun sannu har bana iy amsawa gumi nake ta yi duk AC dinda ya kunna baya mun na cakumo hannunsa na rike gam,yace Baby ki dinga Addu'a kinji....

Ina nishi sama sama,nace Yayana mutuwa zanyi na shiga 3,yana driving yana kalloni duk a rikice Yake......

Yama kasa daga waya ya kira kowa to na rike masa hannu dayan yana driving,yana ta mun sannu.....

Muna sauka hospital aka kawo wheelchair ya tayani zama ya tura ni da kansa,sai Labour room.....

Muna shiga nurses suka kwantar dani yace daya taje ta kira Dr Fateema ita kadai,tace to.....

Taje tace Dr Fateemah bata nan sai dai Dr Asiya yace a kirata ta gaya mata matanshi ke labour shi badan rules din ba  ai bazai yarda ba......

Nan wayana dake ajiye parlour na ta fara ruri Jamila na dauka taji Kausar ce tace Aunty Kausar ai Aunty Khady nakuda takeyi sun tafi hospital nan Kausar ta buga salati take gaya wa Hajiya.....

Hajiya tace yo shi Abbatyn meya hanashi kira mtsww ta kira driver tace a aje a taho da su Jamila,Kausar dama ita tace dole a bar Asmah ta kwana mata ta tashe su daga bacci Asmah tace Asmah Baby ta kareki kafin ta fito ky muje hospital din.......

Fateemah tace wai naso dai naga Fuskar Yaya Andeeja kafin ta shige da na mata hoto nasha dariya nan dazu take mana kuri ita matar likita ce ko....

Suka saka dariya Asmah ta dauko ma Kausar Yar Babynta suka fito har da Daddy aka shiga mota biyu sai hospital.....

Aka ce ai private labour room aka kai Khadijama,dama Suraj yana on call so Nurse ta gaya masa Abbaty ya kawo matarsa,nan dai baya da halin shiga kuma Abbatyn yaki fitowa da shi ake labour......

Duk su Dr Shu'aib da Zaid suna zaune a corridor din,dole dai Dr Fateemah aka mata waya tazo,tace wai duk kuna nan a zaune ta rusuna ta gaishe dasu Hajiya.....

Kausar tace wai ki koro mana Yayan to ya abri taji da abu daya tayi murmushi kasa kasa kada Hajiya taji tace ai Kausar in gaya miki ko ANC aka zo Abbaty baya barin Matarsa yau akwai masifa ai dan ko me zamuyi ba zamuyi masa daidai ba....

Kausar tace gaskia yau kuna da aiki,Allah dai ya raba lafiya yasa ta haihu da kanta tace Ameen

Ta shiga tace Dr AT duk su Hajiya har Daddy suna waje ba zaka je ki gaisa ba?

FOREVER YOURSWhere stories live. Discover now