BAHAGUWAR RAYUWA.

44 2 0
                                    


FITA TA  SHA DAYA.

   NA
QURRATUL-AYN.

 
  Mutumin ya nemi guri ya tsaya tare da duban Shatu cikin kulawa kafin ya ce.

"Sunana Sulaiman ni dan jahar Kebbi ne kasuwanci ya kawo ni nan garin Kano, ko zan iya sanin abin da ya fito dake daga gida?".

Shatu ta gyada kai da sauri, bawai dan ta k'agauta ba, illa tana yin duban da taimakon da ya yi mata ne kawai.

"Sunana Ishatu..!".

Hawaye ya sauko mata kafin a ce ta fara bashi labari kukan ya ci karfinta, kalmar sunanta kawai ta iya ambata masa, Sulaiman ya sake dubanta karo na biyu da fadin.

   "Idan har zanyi wa rayuwarki da yanayin da kike ciki duba na fahimta, hakan ka dai ya isa gamsar dani cewar rayuwarki na cike da sarkakiya, nasan yanzu baki da kwarin gwiwar sanar dani ko ke wacece, kuma a ganina ni dinma babu amfanin ji daga gareki yanzu, saboda iyakacin taimakon da zan iyayi a gareki kenan Ishatu, nima kaina shagon mu na kasuwa nake kwana, da dukkan alamu rabuwarmu daga nan zata fara, ina yi miki fatan alkhairi tare da addu'ar Allah ya kaiki hannu na gari, idan da rabon zamu sake ganawa ina farin cikin Allah ya sake hadamu, amma babban fatana a gareki ki koma gida gaban iyayenki ko da kuwa kasheki zamuyi zama cikin danginki yafi miki shigowa duniya..!".

Shatu ta kasa furta komai illa kalmar "Nagode" tana shash-shekar kuka, Sulaiman ya juya tare da bata baya zai wuce, da sauri Shatu ta tsaida dashi da fadin.

"Wanne gari ne nan?".

"Kano babban gari na kasuwanci, zaki ga al'umma mabanbantan halayya da kabilu kala-kala".

Daga haka bai sake furta komai ba ya cigaba da tafiya, har ya yi nisa sosai ya waigo har a lokacin Shatu na tsaye tana bin bayansa da kallo, kome ya tuna? Ya dawo da baya zuwa gareta tare da sanya hannu cikin aljihu ya ciro duba daya 'yan dari biyar guda biyu ya bata yana fadin.

  "Ki ci abinci da wannan kudin kinji?".

Shatu ta gyada kai babu bakin godiya, Sulaiman ya yi murmushi tare da sake barinta nan tsaye, har sai da ya bacewa ganinta, wasu samari dake lure da abin da yake wakana dayan ya rugu da gudu daya na binsa a baya kafin Shatu ta yi azamar matsawa na gaban ya fauce kudin hannun nata sun shige wani layi a cikin tashar gashi dare ya yi dama, binsu ta yi da kallo kawai domin dama bata san ta yanda zata yi amfani da abin da ya bata ba, wannan ne karo na farko ma data fara ganin irin kudin domin babu gudan daribiyar a karkararsu.

  Neman guri ta yi cikin runfar wata mata mai sayar da abinci ta zauna tana karewa al'ummar dake harkokinsu hankali kwance kallo, tana ji inama ace ita ce take cikin yanayin farin ciki kamar haka, takai dubanta ga mai abincin yayin da wasu samari ke ci sai a lokacin ta tuna da irin bakar yunwar dake tattare da ita, ta mike da nufin zuwa neman abincin tare da fiddo irin kudin dake daure jikinta wanda dan Tsoho ya bata, gudan naira ashirin irin wacce aka canja ta tun da jimawa, mika wa matar ta yi da nufin ta bata abinci.

Matar ta dubeta shek'ek'e yayin da sauran samarin wajen suka kece da dariya, sauran na fadin.

"Ya tabbata dai wannan bata cikin hayyacinta".

"Tab...har na manta rabon da naga irin wannan kudin".

"Ashe akwai su har yanzu a duniya?".

"Aa ko dai a bola ta tsinta?".

"Kai kana tunanin a bola ma yanzu za'a iya samun wannan kudin?".

"Mai zai hana kuwa idan mutane sun gaji da ajiya ai zasu zubar".

Maganganun da samarin ke ta yi kenan a cikin runfar cin abinci, Mai abinci kuwa tun da ga kallo dayan nan bata sake duban Shatu ba, tabarta nan tsaye, wani saurayi da bai tanka ba tun da suka fara zancensu ya tako zuwa ga mai abincin yana fadin.

BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now