BAHAGUWAR RAYUWA.

58 4 0
                                    


Na
QURRATUL-AYN.

FITA TA BIYAR.

Wattpad@JannatQurratulayn.

ANA WATA GA WATA..!.

Haka su Ishatu suka rankaya zuwa gida, suna tafe suna hirarsu har sai da Zainaba ta mantar da ita damuwar dake sarkafe cikin zuciyarta, yayin da duhu ya yi kamar kullum yanda suka saba aka sake tafiya filin Maina domin yin wasannin gada da sauran abin al'adar garin Maina ta gada shekaru masu yawa.

BAYAN KWANA UKU.

Wasa-wasa har kwanaki ukun da suka yi saura na ranar auren Shatu da Manya sun zo, cikin kwanakin abubuwa da dama sun faru masu dadi da akasin hakan, a bangaren Manya kuwa har tsayin kwanakin suka shude bashi da cikakkiyar kwanciyar hankali kamar yanda yake ga Ishatu duk kuwa da cewar ita tana da karfin halin basarwa, amma shi sosai damuwar ta bayyana a dukkan wani sassa na jikin har zuwa kan fuskarsa damuwar bata buya ko mene dalili?.

Da misalin hudowar alfijir na ranar asabar Zakara ya basu sa'a, kamar yanda yanda suka saba a al'adance, Amarya da danginta zaune gefe haka Ango da nasa dangin zaune sai kuma mai garin na Maina da sauran al'ummar gari ke waye, ana jiran mai shela ya sanar da aure kamar yanda suke yi, daga bangaren Amarya mai ganga zai buga sau uku haka bangaren Ango shima za'a buga ganga sau uku, sai mai shela ya sanar da sunan miji da mata sun yi aure za'a ba da farin goro goma sha biyu da shanu ko tunkiya guda bakwai ya danganta daga abin da mijin yake kiwo zai mika wannan kaya matsayin sadakin aure.

  Hakan ya faru a wannan ranar, Amarya Ishatu da Angonta Manya sun sha kwalliyarsu tsaf irin nasu na kauye, tare da dukkan mahalaccin wannan aure, daga bangaren Manya anbuga gangan sau uku mutane aka yi tafi, daga bangaren Amarya an buga daya zuwa biyu ana shirin buga ta uku Tsaraki Mahaifin Ishatu ya fito daga gidan a fusace babu wanda ya yi tunanin cewar baya zaune a wajen auren ma, sai jin saukar muryarsa aka yi yana fadin.

"Mai ganga a dakata..! Ni Mahaifin Shatu na dakatar da wannan auren..!".

Baki daya al'ummar dake wajen suka juya da kallonsu wajen Tsaraki dake tsaye yana huci tamkar mayunwacin zaki, Manya da Ishatu kuwa tamkar wadanda aka junawa shocking a tare suka mike zumbur, Manya na raba ido cike da mamakin jin furucin da baiyi tsammanin fitarsa daga bakin Tsaraki ba, haka abin yake ga Ishatu jin abin ta yi tamkar mafarki, har 'yar kwallar na fita a idanuwanta na farin ciki, mai garin ya kai dubansa ga Tsaraki yana mai fadin.

"Ko mene dalilinka na tsaida wannan auren?".

"Babu wani dalili ya mai girma, amma indai nine mahaifin Shatu a wanan gari na Maina ba da yawuna ba Manya ya auri Shatu na janye wannan batu".

Kamar an kunno dangin Manya suka yi caa akan al'amarin a ganinsu Tsaraki ya shirya wa hakan ne dama kawai dan ya wanzar da cin mutunci a tsakaninsu, suna ganin kamar ya shirya wa daukar fansa ne akan abin da ya wuce tsayin shekaru wanda an yi tunanin ya wuce tun da an sulhunta dalilin sulhun ya sanya har wannan ahali zasu daura auratayya a tsakaninsu dan kawar da wannan bakar gabar, amma kuma mene zai faru?.

"Ba dai har yanzu kana kan bakanka akan abin da ya wuce ba".

Cewar Mai garin Maina kenan, Tsaraki ya dubeshi yana hura hanci kafin ya ce.

"Idan har zan iya yafewa to tabbas sai bayan da naga bayan daya daga cikin ahalin Dan Zabuwa, tsakanina da su babu yafiya bare alfarma, yanzu kiyayyar zata fara tasiri indai nine Tsaraki Dukku sai na cika wannan alkawari da..!".

Bai kai ga karasa maganar da ya faro ba wajen ya kaure da hayaniya kafin kace kwabo waje ya dinke da kurar fada, ga kuma duhun gari da bai karasa wayewa ba, Manya na gefe tsaye tamkar an dasa shi amma kallo daya zaka yi masa hanjin cikinka ya kada yanda fuskarsa ta canja launi ta yi baki wuluk idanuwansa sun rine har baka iya tantance jan idon da farin, labbansa sai kakkarwa suke tsabar wutar bala'i da bacin rai dake ci a cikin gangar jikinsa da zuciya, zubewa ya yi gwiwa a kasa tare da sakin wani hargagin ihu da kurari wanda ya yi sanadiyyar dakatar da fadan da yake shirin canja salo a wannan filin, kowa ya yi cirko-cirko ana kallon-kallon, a daidai lokacin mahaifin Manya ya tuma a kasa ya yi birgima ya yi ihu tamkar wani bijimin sa, tuni hankulan manyan garin ya tashi domin tunawa da abin da ya shude kimanin shekaru talatin da biyar baya, Mai gari da sauran mutan fada suka zube a gabasu suna neman afuwa da gafara, Tsaraki dake shirin shiga filin kaninsa Kalla da abokansa suka rirrike shi domin basa fatan labari ya sake maimaita kansa a cikin wadannan shekarun, Mahaifin Manya ya mike tsaye tare da kama hannun dansa suka kade jikinsu basu kara bi takan mutanen wajen ba suka juya musu baya tare da barin wajen, sai bayan tafiyarsu Zainaba dake tsaye hawaye shabe-shabe tsabar kaduwa da ganin tashin hankalin da bata taba tsammani ba gashi ta ganshi a yau, a she labarin da Iyanta ke bata gaskiya ne?.
       Juyawa ta yi gefanta dan ganin halin da Ishatu ke ciki, taga wayam babu ma alamunta, Zainaba ta mike da sauri ta shige cikin gida ko ta shiga gida ne, domin tasan Shatu da gujewa tashin hankali, Innarta kadai ta tarar daki ta tambayeta inda Shatu take ta sanar mata bata shigo ba, nan suka bazama nema cikin gidan amma babu alamun Shatu a guje Zainaba ta fito tana kwala ihun.

"Ba'a ga Ishatu ba..".

Wani babban tashin hankalin ya bayyana, tuni aka bazu nema lokacin gari ya yi haske sosai duk inda ake tunanin za'a ganta an duba babu ko alamunta, har kan iyakar garin Mai gari ya sanya aka duba ba'a ga sahun kafarta ba, take Inna ta zube tana riskar kuka mai cike da kuna da dacin rai, haka abin yake ga Zainaba tuni gida kowa ya yi cirko-cirko ana mamakin inda Ishatu ta shiga a wannan lokacin, yayin da Tsaraki nacan daure cikin daki yana ihu da gunjin a kwance shi babu wanda ya kula da al'amarin sa bare har a yi gigin sanar masa halin da ake ciki domin sun san sakamakon ba zai yi kyau ba.

Iyan Mairamu tafi kowa narai-narai da idanuwa a dole damuwa biyu tahau kanta, ana tsaka da haka sai ga Manya ya fado afujajan saboda jin labarin batan Shatu da ya yi, shi ne ma ya banka cikin dakin ya kwance Tsaraki yana fadin.

"Duk laifinka ne, duk kaine ka jawo, nasan dama tabbas Shatu na sona tana burin auren nan amma ka dakatar, tun da kace ka fasa aure ni bazan cigaba da bibiyar fansar kiyayya ba, amma sai inda karfina ya kare wajen neman Shatu ko da kuwa zan shiga duniya ne, idan ta kama na rasa raina, amma zan tabbatar maka da cewar Raina fansa ne ga Shatu ina kaunarta, kaunar da bana jin zan iya jure rashinta ko ganin yankewar alakarmu, dole zan rayu da Shatu domin ita din bangare guda ce na jikina, idan ka ga dama ka cigaba da dakon kiyayya, ka raineta fiye da komai a rayuwarka har zuwa lokacin da wutar kiyayyar zata yi maka amfani wajen daukar fansa da hujja amma ba a yanzu ba".

Manya na gama fadin hakan ya juya ya fice daga gidan baki daya, har ya gama maganarsa babu wanda ya ce ci kanka, kowa da abin da ya dameshi a cikin rai, shi yasa babu wanda ya damu da fassarar maganganunsa, Tsaraki kuwa mutuwar tsaye ya yi jin cewar an nemi Shatu an rasa, baki daya kofofin tunaninsa sun kulle ya gaza wanne abu zai sanya a linzamin tunaninsa na farko fansar kiyayya ko maganganun Manya? Ko batun batan Shatu?.

Da kyar dai aka samu aka lallashi Inna aka wuce da ita dakinta, haka Zainaba ma Iyanta ta sanya a gaba tana mai cigaba da kuka a cikin daki, lallashin duniya ta gagara tsai da hadarin idanuwanta daga zub da ruwa sosai hankalinta ya tashi, domin tun tasowarta tare da Shatu take rayuwa akwai kauna da sabo mai karfi dake bin jijiyoyi da kofofin jinin jikin kowannensu duk kuwa da cewar babu zaman lafiya a cikin zuri'ar Dukku tun tasowarsu babu hasken ranar da zai fito har duhu ya mamaye shi ba tare da hatsaniya ta gifta tsakani ba, amma tsakaninta da Shatu akwai So yarda aminchi tare tsantsar kaunar da bazata iya kwatanta adadinta ba.

"Ina kike Ishatu? Ki bayyana a gare ni ko da cikin bacci ne Shatu, zuciyata ba zata iya jure rashin ki ba Shatu ina yi miki fatan kasancewa cikin aminchi a duk halin da kike Shatu".

Zainaba ta karashe maganar tana mai rushewa da wani irin gigitaccen kuka na ban tausayi, har sai da ta kai Iyanta dake zaune kusa gareta hawaye ya zubo bisa fuskarta Wanda ta sanya gefan zanin sakinta ta share ba tare da ta bari Zainaba ta ankare da hakan ba, saboda son gujewa abin da zai Kara dagawa yarinyarta ta hankali.

UWA KENAN..!.

YA ALLAH KA YAFE MANA DUKKAN KURA-KURANMU NA FILI DANA BOYE AMIN.

 

   

BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now