BAHAGUWAR RAYUWA.

44 3 0
                                    

FITA TA GOMA.

NA
QURRATUL-AYN.

    Gudu sosai Manya ke yi har gabashin asuba yana abu daya, hasken alfijir daya fara bayyana shi ya ankarar da shi jerin itatuwan bishiyar Maina wanda yake kan iyakar Maina da Zabir, murna sosai ta bayyana a garashi take ya kara kaimi da azama domin isa akan lokaci har yana ji a ransa tamkar yaje ya samota ma.

  Kamar daga sama ya ji an dakar masa tsakiyar kai, take juwa ta dibeshi ya fadi kasa wan-war kafin daga bisani ya mike yana raba ido domin tabbatar da abin da yake tsammani, inuwar mutum ce ta tunkaro zuwa gareshi na 'yan wasu dakiku kafin yakai layarsa daidai fuskar mutumin dan tabbatar da koma nene, sosai ya girgiza da bayyanar fuskar Mahaifin abokinsa da ya kashe Dukuma, tsabar girgiza sai da ya yi baya kamar zai fadi kafin ya koma ya tsaya da kafafuwansa sosai tare da dakewa yayin da zuciyarsa ke cigaba da tafarfasa saboda ya fahimci ya zo ne kawai domin ya bata wa kansa lokaci ya kuma bata masa, Manya ya ja tunga kafin ya yo kan Mahaifin abokin nasa suka kacame da kokawa kowa kokarinsa yaga bayan dan uwansa.

  
    Can Zabir kuma tuni Dan tsoho da iyalansa sun kammala kintsa Shatu tare da tashin babban yaronsa ya umarce shi akan ya raka Shatu kan iyakar Zabir ya kuma nuna mana hanya, Tsohon ya dubi Shatu da kulawa kafin ya ce.

    "Ku hanzarta domin tafiya, saboda Manya nakan hanya a yanda na gani a daren jiya, sannan ina mai rokonki ki kasance mai hakuri ki kara juriya akan wacce kike yi da, da sannu komai zai daidai a gareki ina fatan zaki dawo cikin alkaryarmu cikin aminci".

Dan tsoho ya yi shiru yana mai juya wa ya shige cikin gidan, mai yiyuwa yana boye hawayensa ne, sauran matan suka yi sallama da Shatu tare da mika mata daurin zannuwa guda biyu wannan kyauta ce daga garesu kasancewar daga ita sai kayan jikinta ta zo, suma suka koma cikin gidan domin ba zasu iya jurewa kallon ruwan hawayen dake zarya akan fuskar Shatu ba, Babban yaron Dan tsoho ya dubi Shatu da fadin.

  "Muje lokaci na tafiya".

Ya dauki daurin kayan nata suka kama hanya cikin su babu mai cewa da wani komai illa Shatu dake aikin sharce ruwan hawaye da majina tana tunanin Mahaifirta da Zainaba, ga kuma rabuwa da Dan tsoho da iyalansa cikin kwanaki ukun da ta yi wajensu taji dadin zama a cikinsu sosai sabo ya ratsa a zukatansu amma bata da wani zabi wanda ya wuce hakan a gareta.
   
      Tafiya ce sosai kafin ma ka fara hango ganuwar iyakar Zabir, har sai da Shatu ta fara sassarfa amma hakan bai sanya ta sare ba, illa karin kwarin gwiwa da bushewa da take jin zuciyarta ta gama yi bata jin zata sake marmari ko mafarkin komawa Maina, amma da zaran ta tuna da Innarta sai ta fara yanke kudurinta tana ji tamkar ta komo da baya ta ga Mahaifirta ko da sau daya ta samu ganawa da ita, amma ina lokaci ya riga da ya kure mata, tun tana kuka da hawaye har ya zamana ya kafe kukan zuci ne kawai take yi, sai da rana ta fara fitowa sannan suka fara hangen iyakar Zabir farin ciki da zullumi suka ziyarci zuciyar Shatu lokaci guda.

   Manya kuwa sosai karfin tsafin Mahaifin Dukuma yafi nashi take ya yi masa laga-laga ya watsar da shi a wajen ko numfashi ba ya yi, dan tunaninsa ma ya kashe shi, shi yasa ya rabu da shi anan ya yi yafiyarsa, sanyin iskar dake busawa ce ta yi sanadiyyar farfadowarsa daga suman da ya yi, ya bude ido a hankali Yana tari kafin ya tashi zaune yana mai dafe kansa take abubuwan da suka faru suka fara dawo masa, zumbur ya mike da sassarfa ya fara cigaba da tafiya ganin rana na nufin fara hudowa, yana isa cikin Zabir rana ta kwalle sosai Manya ya durkushe kasa tare da kwalla wani irin gigitaccen ihu take mutum garin na Zabir suka zagayeshi suna kallonsa cike da ayar tambaya.

Mikewa ya yi idanuwan nan nasa jajir ya dinga fadawa gidanjensu yana neman Shatu amma babu ita babu dalilinta, tambayar duniya mutan garin suka tabbatar masa da cewar basu ga wata bakuwa ba, Manya ya nemi waje guda ya zauna yana jinyar zuciyarsa da yake ji tamkar zata fito fili, mikewa ya yi zai dau hanyar iyakar Zabir take maganar Mahaifinsa Dan Zabuwa ta fara dawo masa.

"Idan har baka sameta a Zabir ba, ka da ka yi gangancin keta iyakar Zabir sai dai wani ba kai ba..".

Manya ya sake kwarara ihun da yafi na farko tare da juyawa ya Kama hanyar komawa cikin garin Maina zuciyarsa cike da kunar bakin ciki, ko ciwon jikinsa bai damu da shi ba kamar yanda yake jin na zuciyarsa.

***
  Ko da su su Shatu suka isa iyakar Zabir Saurayin ya dubeta da kulawa kafin ya ce.

  "Anan zan barki na koma kamar yanda Dan Tsoho ya umarce ni, ina yi miki fatan alkhairi, sai wani lokaci idan da rabon sake haduwarmu".

Suka yi sallama ya juya da nufin komawa bayan ya yi mata nuni da hanyar da zata cigaba da bi, Shatu ta yi tsaye tana mai bin bayansa yayin da ruwan hawaye ke zarya a fuskarta har sai da ya bace wa ganinta kafin ta juya itama ta kama hanyar tana yi tana waigen bayanta cike da kewa.

     Ta yi tafiya sosai kafin ta isa wani Dan kauye karami, ruwa kawai ta roka tasha ta cigaba da tafiya har maghriba sannan ta fito babbar hanya shiru babu motsin kowa, hanyar ta kama bi cike da tsoro da fargaba kamar da ga sama ta ji wata irin Kara wacce bata saba ji ba, kasa ta durshe tare da toshe kunnuwanta abin ya bata mamaki data dogon abu ya tsaya a gabanta da wasu irin fitulu a jikinsa,  ga motane a ciki duk a zaune a razane take binsu da kallo a tunaninta ko ba mutane ba ne.

  Kwandastan ya fito daga mota yayin da yake fadin.

"Kanwata ina zaki je?".

Al'amarin ya kara tsinke mata ganin mutum irinta kuma yana magana da irin yarenta sai dai yanayin shiga da komai ya banbanta da na garinsu, kwandastan kansa yaga alamun tsoro a tattare da ita bama sauran mutanen dake motar ba, driven ya dubi kwandastan kafin ya ce.

"Mudi zo mu tafi, da alamu ba tafiya zata yi ba, ni ganinta nake ma Kamar bata da hankali".

"Kamar dai bata cikin hayyacinta, amma idan mun barta  cikin wannan jejin ai kamar munyi ganganci 'ya maca ce fa".

Daya daga cikin mutanen dake cikin motar ya fada, kafin kwandastan ya sake furta wani furuci Shatu ta zube kasa a sume, cike da tsoro kwandastan ya dubi mutanen da fadin.

"Ta suma fa, ya za'a yi mu tafi da ita a haka alhali bata furta inda zata je ba, kuma bata cikin hayyacinta ma?".

"Babban kuskuren da zamuyi a yanzu shi ne barin baiwar Allahr nan a nan, ni a ganina mu tafi da ita da yiyuwar wahala ce ta sanyata shiga wannan halin".

Mutumin ya sake fada a karo na biyu, kwandastan ya yi shiru tsayin lokaci kafin ya dubi Driven da fadin.

"Maganarsa tana kan hanya oga".

Sauran mutanen ciki suka ba da goyon bayan a tafi da ita can tasha, watakila kafin su isa ta dawo cikin hayyacinta, akan wannan suka tsaya aka sanya wasu kabilun mata uku suka daukota tare da sanyata cikin mota kusa da su har lokacin bata farfado ba, kuma babu ruwan da zasu shafa mata ta farfado akan dole suka tafi da ita yayin da kwandastan ya miko wa matan daurin kayanta, driver ya ja motar suka bar jejin da sauri saboda da dama jejin ya yi kaurin sunan rashin kyau, ana yawan tsare motoci da satar mutane ga yawan accident na ban tsoro.


Haka Manya ya koma garin Maina  zuciyarsa kamar zata fashe, Dan Zabuwa dake zaune zaman jiran zuwansa yana ganinsa cike da tsoro da fargaba kenan yau dansa daya tilo tal ya fadi, wannan ce ranarsa ta farko a rayuwarsa da ya gaza samun abin da yake so, har suka shiga cikin gida Manya baice komai ba illa kwayar idonta da ita kadai ta isa isar da sakon dake kunshe cikin zuciyarsa, Dan Zabuwa ya zaunar da shi tare da dauko ruwan magani Yana goge masa raunin dake jikinsa, amma ko gezau Manya bai yi ba, ya zamana ma tamkar bai san halin da yake ciki ba, har Dan Zabuwa ya cika da tsoro da fargabar ko Dan nasa ya yi gamo da aljanu ne sun zautar masa da shi?.

 
    Sai sanda suka isa tasha sannan Shatu ta farfado daga dogon suman da ta yi, har lokacin tsoro da fargaba basu barta ba, wannan mutumin shi ne ya biya kudin motarta yanayin yanda suke fita daga motar ne ma ya kara bata tsoro, da kyar aka samu ta taso daga inda take zaune tana leko kai da ta ga  yanda motoci da babura ke zarya ga kuma hasken fitilun da ya haske tasha sai ta koma cikin motar da gudu tana ihu da kyar dai wannan mutumin ya kamo hannunta ta fito aka kulle motar mutanen dake yawo a tashar sai faman kallonta suke cike da tunanin ko bata da hankali ne?.

Yau dai a gafarce ni zuwa gobe insha Allah, BABU YAWA.

NAGODE SOSAI DA KAUNA.

NWA®.



BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now