BAHAGUWAR RAYUWA.

40 1 0
                                    


NA
QURRATUL-AYN.

ASHIRIN DA BIYU.

Tashin kiran sallah da kunnuwanta ya jiyo mata ne ya yi sanadiyyar farkawarta da yake masallcin unguwar nan kusa da gidan yake, a hankali ta bude idonta kafin ta waresu baki daya a tare ta mike zumbur kamar antsikareta, da mamaki ta cigaba da karewa Khalid kallo, da yake yana zaune ne akan kujerar da ke fuskantar ta, kansa na kwance jikin kujerar hannunsa na dama kuma dauke da kofin glass haka kan center table din da ke gabansa kwalabe ne guda biyu ya dora kafarsa daya bisa table din dayar kuma na ajiye kan carpet da dukkan alamu barawon barci ne ya yi awon gaba da shi ba tare da ya shirya ba.
Sosai Ishatu ta gyara zama tare da cigaba da kare masa kallo tana nazartar yanayinsa, sosai shi kyakkyawa ne ga kuma karin hutu da fatarsa ta samu, Khalid bashi da makusa ta ko ina duk macen da ta sameshi hakika za ta yi alfahari da mallakarsa, matsalarsa guda ita ce bariki.
Ishatu ta yi ajiyar zuciya tare da mikewa taku kadan ta karasa gare shi ta dan sunkuyo tana mai sanya hannu ta janye kofin dake hannunsa take wani wari ya bugeta da sauri ta juya ta kwashe sauran kwalaben ta a jiye saman frige dake nan falo har zata wuce ta dawo da baya tare da shan-shana kofin.

'Tabbas giya ce'.

Ta fada cikin ranta tana mai mayar da kofin ta a jiye tare da satar kallonsa kafin ta cigaba da fadin.

"Abin har ya yi maka yawa, ko da yake barikin kenan kamar yanda Hafsy ta fadamin dan suma suna irin wannan shaye-shayen".

A fili ta yi maganar tare da jan guntun tsaki ta nufi kofar falon da zummar bude wa, ta murda ko motsi kofar bata yi ba alamun ya kulle, Ishatu ta girgiza kai tana mai kai kallonta jikin bangon dakin idonta ya sauka akan katon agogon dake kafe ya nuna karfe bakwai har da rabi, goshinta ta dafe da hannu tare da juyowa a ranta tana fadin.
'ko mene silar wannan dogon barcin nawa?'.

Bata kai da karasawa ba sai ji ta yi ta yi karo da abu janye hannunta ta yi da sauri tare da waro idonta waje, da murmushi ya bita da kallo yana mai daga mata gira, sai lokacin ta lura da cewar jikinsa ta yi karo da shi, cikin sauri ta ja baya tare da murga masa harara kasa-kasa Khalid ya yi murmushi kawai ba tare da ya ce da ita komai ba ya juya yabar wajen har ya kai bakin wata kofa ya juyo tare da daga hannunsa yana yi mata nuni da wata kofar ya furta.

"Za ki iya amfani da wancan dakin".

Bai jira amsarta ba ya sanya hannu tare da bude kofar dakin ya shige abinsa, Ishatu ta sauke wata irin a jiyar zuciya da karfi har tana dan dafe kirjinta kadan, kai tsaye kuma ta nufi kofar dakin da ya nuna mata cike da fargaba ta sanya kai dakin tana zaro ido waje.
Tsananin mamaki ya kanainayeta yayin da ta yi tozali da abubuwan amfanin da ke dakin duk kayan da mace zata yi amfani da su ne, tunawa da ta yi da waye Khalid ya sanyata ajiye mamakinta gefe kai tsaye wata kofa ta nufa a cikin dakin wacce take kyautata zaton toilet ne, kamar yanda ta zata hakan ne ya faru da sauri ta karasa shigewa yayin da taga toilet fes kamar ana gyaransa ko da yaushe wanka ta yi tare da dauro towel din da ta gani jere ba zasu kirgu ba alamun duk sabbi ne alwala ta yi a gurguje ta fito ganin tafiyar lokaci na neman kure mata.
Kan mirror ta tsaya tana karewa mayukan dake a jire akai kallo, kafin ta ja guntun tsaki bayan ta bude wardrobe din kaya ne birjit a ciki kala-kala da karfi ta mayar da murfin ta rufe yayin da ta koma toilet ta dauka rigarta data cire ta mayar fitowa ta yi falo a hankali babu kowa babu motsin komai sai sautin karar AC dana TV dake kunne hand bag dinta ta dauka tare da komawa cikin dakin bayan ta bude jakarta ta fiddo da mayafin rigarta ta rufa akanta tare da tayar da sallah.

Sai bayan da ya kammala komai nasa ya yi fes abinsa sai tashin kamshi yake yi kamar wata mace, ya fito zuwa falo kamar yanda ya zata hakance ta faru zaune ya ganta kan daya daga cikin kujerun falon wacce ke fuskantar kofar dakinsa, suna hada ido ta yi kasa da kanta shi kuwa kallo ne mai cike da mamaki yake binta da shi, kafin ya karaso tsakiyar falon ya zauna kan kujera kusa da ita har jikinsu na dan gogar juna Ishatu ta dan matsa kadan tare da sake dauke kai gefe, a hankali ya motsa labbansa wajen fadin.

BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now