BAHAGUWAR RAYUWA

101 7 0
                                    

Na
QURRATUL-AYN

Wattpad@JannatQurratulayn.

FITA TA BIYU.

Gunjin ihu da kirarin da suka fara jiyowa ne ya sanya dukkan al'ummar dake wajen dakatawa daga abin da suke yi, mintuna kadan da yin shirun gayyar 'yan bangan Dalladi da tawagarsa suka iso wajen, mutum ne garjeje ga tsawo da fadi, duk da duhun da ya fara yi hakan bai hana hasken 'yar fitilar ya hasko maka jajayen idanuwansa kamar gauta ba, labbansa baki wuluk kamar ya shafa bakin tukunya, yana sanye da 'yar shara da hula irin wacce ake kira da obasanjo, tuni aka shimfida masa tabarma ya zauna da sauran jama'arsa kafin ya ba da umarnin a cigaba da wasa, Ishatu da Zainaba shiru suka yi suna duban sarautar Allah tare da jiran tsammani.

Daya daga cikin tawagar tasa ne ya karaso gabansu da fadin.

"Ke ki zo Manya na kiranki".

Da yake sunan da ake kiransa kenan kaf garin, cikin darin jiki suka mike tare da bin bayan dan aiken nasa, suna isa ya kare musu duba sama da kasa kafin ya yi umarni yaran nasa duk suka mike daga wajen tare da nufar inda ake wasan suka dasa nasu, nuni ya yi wa Ishatu da tq zauna kusa gareshi ba musu ta zauna, yayin da Zainaba ta yi niyar zama kusa da ita ya watsa mata wani irin kallo mai dauke da wucin wuta a cikin idonsa, da sauri ta ja gefe ta tsaya, bai kuma bi ta kanta ba ya dawo da dubansa ga Ishatu cikin irin kallo na cikakkun yan bariki kafin ya lashe labbansa kadan ya ce.

"Har yanzu kina fushi ne akan auren mu?".

"A'a, mene amfanin fushi akan abin da nasan ko zan mutum ba za'a fasa ba?".

"Kina da gaskiya".

Manya ya kai maganar yana mai bushe da mahaukaciyar dariyarsa, kafin ya tsagaita ya cigaba da magana.

"Kina burgeni saboda tsiwarki, ko babu komai mutane sun shaida matar Manya ba kyalle ba ce".

Shiru ya ziyarce su, yayin da Ishatu ke harararsa kasa-kasa, suna hada ido ta wayance da murmushi, shima murmushin yake amma sai ka rantse kuka yake shirin yi, saboda shi mutum ne da Shaidan ya samu wajen zama sosai a jikinsa komai nasa yanayi ne da shi naban tsoro.

"Tsakanin ni da ke waye ya taimaki wani akan wannan auren?"

Sosai maganar ta bawa Ishatu mamaki, ta kuma rasa amsar sa zata bashi tuni kwakwalwa da dukkan tunaninta suka tsaya saboda tsoran amsar da zata bashi, tasan ko ya ta yi tuntuben harshe tabbas kashinta ya boshe a wajen, bata san hukuncin da zai dauka ba, Ishatu takai dubanta ga Zainaba dake tsaye kamar falwaya ta turo baki gaba sai cika da batsewa take, sosai ta kuntata da tsayuwar amma bata jin zata iya tafiya tabar Ishatu saboda Manya mutum ne da bashi da alkibla ko kadan, mutunci da yardarsa ga mutane na mintuna ne, Zainaba dake tsaye tana jinsu ta dubi Ishatu tare da yi mata nuni da cewar shi ne.

"Kai ne ka taimaki ni".

Kallon da ya watsa mata ya sanya hantar cikinta kadawa, ta yi tunanin ko tabashi amsar da bata gamsar da shi ba ne, bushewa ya yi da dariyar tasa da ya saba ko da yaushe, Ishatu da Zainaba kusan a tare suka sauke wata bayyananniyar ajiyar zuciya, Yana shirin sake magana wajen ya kaure da haniyar mutane alamun fada, ko ba'a fada ba ansan mutanen Manya suka janyo da sauri ya mike ya nufi filin Ishatu da Zainaba suna masu take masa baya.

Yana isa wajen duk suka sha jinin jikinsu, cikin samarin da suke wasa a wajen har an yanki mutum daya a hannu Amma saboda aldalci irin na Manya ko jin ba'asi bai yi ba ya yi umarnin yaran su biyoshi su tafi, tare da iza keyar su Ishatu a gaba zai rakasu gida ba tare da ya kuma bi takan mutanen wajen ba, wanda duk ta dalilinsa suka taru kuma a wajen, har suka isa gida babu Wanda ya tankawa wani a cikin su, suna isa kofar gidan mai zagaye da dangar kara Ishatu da Zainaba suka fada ciki tare da barin su Manya nan wajen, Manya ya yi sororo tsaye alamun fushi bayyane akan fuskarsa.

BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now