BAHAGUWAR RAYUWA.

65 2 0
                                    


   Na
QURRATUL-AYN.

  Wattpad@JannatQurratulayn.

FITA TA HUDU.

***

A yanda 'yan rabon fada suka watse suka bar Innar Ishatu a haka su Ishatun suka tadda ita ta yi ta gumi, da dukkan alamu ta yi nisa cikin tunanin mai zurfi, Ishatu ta sanya hannu ta dan girgiza kafadarta tare da fadin.

"Inna mai ya faru?".

A jiyar zuciya ta saki mai sauti a daidai sanda ta sauke kallonta akan fuskar Ishatu dake tsugunne gabanta, kokarin aron murmushi ta yi ta sanya akan fuskarta, a kokarinta na nade shimfidar damuwar dake kan fuskarta.

"Babu komai Shatu, gajiya ce kawai ta zaunar dani nadan huta".

"Dan Bitir ya ce min fada ake yi Inna, me ya faru?".

Ishatu takai maganar kamar zata yi kuka, Innar ta dafa kanta kafin ta ce.

"Fada tsakanin Iyan mairamu ne da Iyan Zainaba".

Ajiyar zuciya Ishatu ta sauke har tana dafe kirjinta, sai lokacin Inna ta dago kai ta ga su Manya tsaye gefansu sun zuba musu na mujiya da sauri ta gyara zamanta tana murmushi, Manya ya dauke kai gefe, Ishatu takai dubanta itama wajensu a daidai sanda Iyan Mairamu ta fito daga daki baki a washe ta tarbi Manya ta janye shi zuwa cikin bukkarta, gajeren tsaki Ishatu ta ja tare da kama hannun Innarta suka bar filin tsakar gidan, sai lokacin ta tuna da Zainaba bata damu ba domin tasan tana can wajen Iyanta.

            "Yau ni naga mugun abu Manya..! Duniya daban tsoro take kamar ni Ishatu da wannan bakar yarinyar zasu karewa zagi? Ka dai San dama Uwarta taki jinin wannan auren, duk take-takenta bai wuce ganin wannan hidimar auren ta rushe ba, kai yanzu sai ka bari hakan ta faru kenan?".

Manya ya zubawa wa Iyan Mairamu Ido yana sauraronta, ganin shirun da ya yi hakan ya tabbatar mata maganarta tana shiga kunnensa kenan, bata damu da tankawarsa ba ta cigaba da fadin.

"Gara ka dauki mataki tun da wuri wallahi, ka da makircin wannan matar ya yi tasiri har Tsaraki ya janye daga maganar auren nan, duk da dai sauran kwana uku auren amma ina gudun abin da zai faru kafin ranar, nasan kana sane da cewar tun sanda aka sanya auren nan take shige da fice ganin Tsaraki ya janye wannan batun, yanzu hakan zaka zuba Ido har hakanta ya cimma ruwa? Ni mai sonka ce kasan kaf garin Maina babu wanda ya yi sa'ar mace irin Shatu mace dirarriya dakyan diri samunta sai anbincika, kuma ba tun yanzu ba nake fadi tashi ganin cewa ka aureta domin da kai ta dace..!".

"Ya isa..!".

Ya dakatar da ita daga zubar da take yi kamar kanya, mikewa ya yi rai a bace ba tare da ya kuma cewa komai ba ya fice ransa idan ya yi dubu ya baci, Iyan Mairamu ta rushe da guda da shewa bayan fitarsa diyarta Mairamu dake labe ta fito suna keta dariya, kafin su lafa Iyan ta dubi Mairamu da fadin.

"Iyan Mairamu nake, bakar dawa mai bata tuwo, a Ido babu kyau a sanya a baka babu dadi, ni ce kadangaren bakin tulu ta gidan Tsaraki zama dole rabuwa sai mutuwa, Uwa ga Mairamu autar mata, aurenki sai Dan sarki, biyan kudin aure sai sarki, duk bakin cikin mai hassada sai dai ya mutu da Kunar zuci".

Kirarin da take yi wa kanta kenan, a duk sanda ta shuka wani abin tsiyar, Mairamu na gefe tana dariya, domin kaf bakin hali da mugun nufi babu abin da Mairamu ta bari na daga mahaifiyarta, shi yasa kaf cikin 'yayanta tafi kaunar Mairamu.

Manya ya yi tsaye ya kasa zama, idan ya zauna zama ya gagareshi, ya kai gauro ya kai mari, safa yake da marwa tsayin a wannin lokaci ya shude ba tare da ya ankare ba, maganganun Iyan Mairamu ne ke zarya cikin zuciya da kwakwalwarsa, neman mafita yake amma kwanyar ta goshe, nazari yake son yi amma tunanin ya gushe, neman abin yi yake sai dai zuciyar ta bushe, take ya ji kansa kamar tsutsa na yi masa yawo ya kai hannu biyu ya dafe kansa tare da kwala wani irin gigitaccen ihu wanda tun da yaransa suke tare da shi basu taba jin ya yi irinsa ba, sosai yau al'amarin ya gigita su, har sai da ya kaisu ga mikewa tsaye cirko-cirko suna jiran tsammani daga gare shi.

Lakwas ya yi tare da komawa waje guda ya zauna, Yana zane a kasa tamkar mai lissafi, tsayin wasu dakiku kafin ya dago kai ya dubi sauran yaran nasa da murmushin da yafi ihun da ya yi basu tsoro shimfide saman fuskarsa, amma hakan bai hanasu rissinawa ba suna jiran umarninsa.

"Wanne hukunci kuke ganin ya dace na yi wa duk wanda ya yi kokarin rusamin burina na wannan auren?".

Shiru suka yi kawunansu a kasa, babu wanda ya yi yinkurin tankawa.

"Magana nake yi da ku fa?".

Ya harziko musu cikin hargagi, Daya daga cikinsu ya ce.

"Oga kawai muga bayansa"

"Aa ba haka za'a yi ba, Oga ka bada umarni a batar da shi a duniya".

"Oga kawai ka yi masa hukunci mafi muni wanda ba zai manta da shi ba tsayin rayuwarsa".

Haka kowa ya dinga kawo shawarwari dan gane ga abin da ya tambaya daga garesu, har sai da ya gaji da ji dan kansa ya dakatar da su da fadin.

"Ku wuce muje majalisa kawai".

"Oga ka sauko kenan?"

Cewar wani karami daga cikinsu, Manya ya yi murmushin gefan baki ba tare da ya ce komai ba ya wuce gaba suka take masa baya tamkar bakin zaki da 'yayansa.

    "Inna wai har yanzu ba zaki bar damuwa akan abin da ya faru ba? Ya riga ya wuce fa, kuma kince ba dake aka yi fadan ba, to damuwar ta mece Inna?".

"Shatu kenan, dukkan wata damuwa a yanzu ba wai ina yinta akan kaina ba ne, Aa ina yinta ne akanki Shatu, ni uwace dole zan damu da damuwarki fiye da ke kanki, nasan duk wannan kokarin kina yi ne kawai saboda ni, baki son ki nuna damuwarki akan auren nan saboda ka da na damu, amma ba tun yanzu ba nasan tabbas kina lullube damuwa sosai a cikin zuciyarki Shatu, kina da juriyar iya danne damuwa da murmushi abin da ba kowa ne zai iya hakan ba, a kullum tsoron dariyarki nake, domin nasan sau tari kina dariya ne a lokacin da damuwa tayi tsamari cikin ranki, a kokarin ki na danne damuwar da baki son kowa ya fahimta, Shatu ki daure ki koyawa kanki bayyanar da damuwa a fili ko yaya ne, hakan ne zai sanya ki samu damar yayyafa ruwa ga wutar radadin dake ci a zuciyarki".

Shiru ya jiyarci dakin nasu, sosai jikin Ishatu ya yi sanyi, saboda ita kanta tasan Innarta gaskiya ta fada, kuma ita ce mutum ta farko dake iya gano abin da ke kasan ranta kafin bayyanuwarsa, to a ma ita din haka take haka ta taso cikin rayuwar kuna da bakin ciki, bata tunanin ko zuwa gaba akwai ranar da zata yi murmushin farin ciki, abu ne wanda take ganin mawuyaci ne ta iya raba ranta da damuwa a halin da take ciki, amma kuma mafi kololuwar damuwa shi ne bayyanar damuwarta a fili domin bata san halin da Innarta zata shiga ba, bata shirya rasata ba saboda ita kadai take gani a matsayin gatanta a yanzu, baya ga ita sai Zainaba wacce take mayar da damuwarta tankar tata, wanne hali zasu shiga idan suka fahimci damuwarta? Hakan yasa ta ajiye a ranta ko zata mutu da bakin ciki zata ci gaba da dakon damuwar da Mahaifinta yake shuka mata tare da matarsa.

A fili murmushi ta yi kafin ta dubi Innarta ta ce.

"Karki damu Inna, komai ya zo karshe ai, ni yanzu ko kadan bana damuwa akan auren Manya damuwata kawai halin da kike ciki".

Inna ta dafa kan Shatu da murmushi akan fuskarta yayin da Shatu ta gyara mata kwanciya akan sakwar-kwaraccen gadonsu na kaba dake yashe tsakar dakin, mafici ta dauka tana yi mata fifita kadan-kadan suna hira jefi-jefi tana kokarin kawar mata da damuwar dake ranta, har dai ta samu bacci ya yi awon gaba da ita, Ishatu ta mike da sauri ta fice daya dakin ta nufi wajen Zainaba.

Tana isa Zainaba na tsakar gidansu tana mayar da abin da ya faru da sauran dangi 'yan biki wadanda suka zo yanzu da gudu ta mike ta tarbi Ishatu tamkar sun jima basu hadu ba, hannun Shatu Zainaba taja suka yi waje tana fadin.

"Dama ke nake jira zaman gidan ya ishe ni wallahi, kin san me ya faru ne bayan mun fita daga gida dazu?".

"Aa sai kin fada, amma ina zamu je ne kike faman jana?".

"Ke dai muje kawai, muna tafe ina baki labarin da Iyata ta bani, kai wallahi Iyan Mairamu makirace Allah, ni harta fara bani tsoro fa".

Ishatu ta yi dariya tana girgiza kai, haka Zainaba ta zage tana Bata labarin abin da ya faru suna tafe a hanya kamar masu shirin barin garin Maina, sun yi tafiya mai nisa kafin Ishatu ta takura Zainaba suka dawo da baya zuwa gida.


ALLAH YA JIKAN WADANDA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA.

BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now