BAHAGUWAR RAYUWA.

55 3 0
                                    

FITA TA TAKWAS.

Na
QURRATUL-AYN.

Wattpad@Qurratulayn.

BAYAN wasu kwana Allah ya yi min dawo wa insha Allah, godiya gareku masoya Daga masu Kiran waya har zuwa text Allah ya bar kauna, BAHAGUWAR RAYUWA zai cigaba da zuwa muku da yardar Allah ban yi alkawarin yi kullum ba dama, amma da yardar Allah ba zan sake 2dys ba tare da ban yi update ba ngd sosai.

***



"Mairan ! Mairan !! Mairan !!!".

Ta ambata sau uku tana da ga tsaye tsakaninta da bangon dutsen taku uku, ta dan buga kafarta kadan yayin data furta kalmar karshe kamar yanda ta ga ya yi a daren jiya lokacin da ya kawo mata abinci zai tafi, yanayin yanda jikinsa ya nuna kadai ya isa sanar mata a gajiye yake a wannan lokacin shi yasa ta yi ta fatan kar ya dawo har sai sanda ta ida nufinta.

Kafin ma takai ga sauke kafarta tuni kofa ta bayyana a gabanta cikin gaggawa da azama ta yi waje, amma kuma sai me? Turus ta yi yayin da takai bakin kofar tsayin dutsen da ke tsakaninsa da kasa yakai takun kafa goma sha biyar zuwa ashirin, kirjinta ta dafe domin bata da masaniya akan ta yanda zata sauka daga dutsen, tunani ya zo mata na sake maimaita sunan kabilar tasu wato Mairan, amma ko motsi dutsen bai yi bare wata kafa ta bayyanar mata wacce zata taimaka mata ta sauka, illa kofar dutsen data koma ta rufe ruf kai kace babu wata halittar kofa a jikin dutsen jikinta ya yi sanyi ainun, amma zuciyarta na cike da bata kwarin gwiwa tana ji aranta ba zata kuma komawa cikin dutsen ba, cikin dakikun da basu wuce goma ba tunaninta ya canja take ta rutse Ido tare da yin tsalle ta fada kasan dutsen a tare ta saki wata kara saboda ciwon da ta ji da azaba ga jikinta da ba lafiya ba, idonta ta bude tare da waige-waige cikin karfin halin kokarin cimma buri da manufa, kasancewar zuciyar ta riga ta bushe bata da wani zabi wanda ya wuce yin karfin halin, da sauri ta mike ta fara takawa da gudu ba tare data waiga bayanta ba, gudu take wanda ita kanta bata taba sanin ta iya gudu kamar hakan ba, a gefe guda kuma koramar idanuwanta har lokacin kwaranyar da ruwa suke yi, soyayyar mahaifiyarta data kanwarta kawa aminiya tana dawo mata, tana tunanin dukkan ninsu ko suna cikin wanne hali ne?.

"Ki gafarce ni Inna ! Ki gafarce ni !! Na riga na gama yanke kauna daga Kara ci gaba da rayuwa a wannan alkarya ! Idan da rabo zamu gana ko ba yanzu ba, ko kema nasan ba ki da zabin da zaki bani wanda ya wuce wannan Inna zan yi kewarku sosai Inna idan da tsawon rai zamu gana..!".

Kuka ne ya ci karfinta sosai har sai da ta durkushe kasa akan gwiyoyinta tare da dafe kasa da hannuwanta tana rera kukan ban tausayi da kunar zuci, ganin alfijir na niyar ketowa ya sanyata mikewa ta ci gaba da gudu ba ji ba gani tun idanuwanta na zub da hawaye har ya zamana sun kafe kaf sai kukan zuci kukan da yafi dukkan kuka ciwo da daci.
Ta yi gudun sa'o'i goma sha biyu ko fiye da haka, domin sai da rana ta take sosai ishi da yunwa sun galabaitar da ita sosai amma duk da haka gani take duk wanda ya biyota yanzu zai iya cimmata haka ta kara kaimi da juriya ta cigaba da cin uban gudu cikin dokar jejin da babu gida gaba babu gidan baya, illa kukan tsuntsaye kala-kala, ta shafe tsayin sa'a tana gudun ta ganta a wani fili fetal banda rairayi na Sahara babu komai, baka kuma hangen komai, bata yi kasa a gwiwa ba wajen cigaba da gudu duk kuwa da zafin saharar dake cin karfarta bata yanke kaunaba, tun tana jin zafin ya zamana tafin kafafuwanta sun jure, ya dauketa tsayin sa'a uku kafin ta fita daga wannan Sahara ta fada wani jejin Mai duhu nan ta yi zaman wasu dakiku tana haki na wahala da galabaita, rugugi ta fara ji wanda ya kara kidimata ta sake mikewa ta yanka jejin tana sassarfa bata tsaya ba sai da ta isa daf da wasu itatuwan bishiyun maina dake jere reras kamar jerasu aka yi bata damu ba ta kusa ta cikinsu ta fice, tana fita ta fara hangar alamun wata alkarya can gaba gareta take ta kara kaimi da azama domin isa ga wannan alkarya, tana da yinin samun ko da ruwa ne domin jika moshinta, cikin dakika guda ta gifta wannan icen Maina a daidai lokacin da wata irin tsawa da rugugi suka sauka a cikin garin na Maina wanda ya girgiza duk wanda yake rayuwa a kauyen, ba mutane ba hatta dabbobinsu sun girgiza, tuni Mahaifin Manya ya fada cikin dakin tsafinsa domin ganin gaskiyar abin da ke shirin faruwa, hankalinsa ne ya duguzunma ya tashi yayin da yaga wutar tsafinsa na canja launinka kala-kala kafin daga bisani ta yi baki wuluk allon da sunan Shatu ke ajiye gefe tuni sunan ya goge allon ya tarwatse har sai da aka yi wulli da Dan Zabuwa can gefe, a kidime ya rarrafa ya fice daga dakin ya nufi dakin Manya dake kwance ya shanya baki yana wani irin nannauyan bacci duk wannan abin tashin hankalin dake faruwa baisan ana yi ba.

BAHAGUWAR RAYUWAWhere stories live. Discover now