Virgin

804 78 8
                                    

_The secret issues_
  *💖JUYAYI💖*

*18-19*


  *_Wattpad_*
  nimcyluv


         Before we ask
    God for anything we must first thank him for everything 🙌🏻🙇🏻‍♀️

     *Dedicated to MaimunaAbdullahi* still waiting for ur hurt coffee I luv u my jerry🥰🌹

Not edited.
        
                .....Cikin tsoro da firgici haɗi da ƙaraji Fannerh ta shiga girgiza Afnerh tare za kiran sunanta "Afnerh pls wake up pls Hadnerh,ganin Afnerh ko mutsi ba tayi ne ya sashi taɓe baki tare da juya zai shige cikin bedroom ɗinsa sai kuma yaga rashin da cewar hakan ko babu komai baƙin Fauwaz ne kuma Fauwaz ya zama jininsa bazai taɓa iya wulaƙanta jinin abokin nasa ba.
Bak damu da yadda surar jikinsa da take a buɗe ba a hankali ya taka tare da ƙara sawa wajansu cikin muryarsa wacce bata fita sosai sabida tsaɓar rashin son maganarsa,lumshe gajiyayyun idanunsa yay tare cije lips ɗinsa ya ƙara mutsa bakinsa tare da ware laɓɓansa yace.
"ke Aljanu gareta halan?" baƙin ciki ne ya kama Fannerh har bata san lokacin data wurga masa wata uwar harara ba tare da faɗin"what Aljanu fa?Allah yay mata tsari dasu"ƙara taɓe fuska yay irin ko'a jikinsa ɗinan "ok farfaɗiya take kenan?"ya ƙara jefa mata wata tambayar cikin sauri Fannerh ta ɗago kanta tare da zuba masa baki ta saki ganin gama ɗaya ya maida hankalinsa kan T.V tamkar bashi yay maganar ba.
Ganin ta ɗauke daga garesa ne yasa ta juya tare zuwa wajan freezer  tare da saka hannu ya ɗauko gorar ruwa mai sanyin gaske cikin gajiyawa da kukan da Fannerh take ya lumshe idanunsa haɗi da saka hannu ya shafi ƙwantaccen gashin da yay luff a ƙirjinsa a haka ya ƙarasa wajan da suke,tsaki yaka cikin lion sound voice yace "oyya gefe"yana faɗin hakan ya sunkuya tare da riƙe gefen rigar Afnerh ya jawota haɗi da jinginata da jikin sofar dake parlon,murfin gorar ruwan dake hannunsa ya ɓalle kai tsaye ya sheƙa mata ruwan a jikinta.
Wata wawiyar ajjiyar zuciya ta sauke tare da ƙanƙame jikinta jin wani a zababban sanyi daya ratsa jikinta lokaci guda a galabaici ta shiga faɗin.
"shine wallahi shine tabbashi shine my heart dream shine mafarkin zuciyata a kullum dashi nake ƙwana nake dashi bana da burin daya huce na kanga a gaske,a kansa na guji dukkan waƴanda suka ce suna sona wallahi kaine eyes ball ɗinka sune suka ƙara tabbatarmin da haka,fatana da kuma muradina haɗi da cikar farin cikin zuciyata shine Allah ya bayyana min kai ubangiji kada ya ɗauki raina sai naga wanda zuciyata dake mafarki a kansa sai gashi na ganka when all is gone a lokacin da komai ya ƙare yanzu kaine duniyata kaine jindaɗi na,kaine muradina,kai farin cikina,kaine mahaɗin rayuwata,kaine bangwan da zan jingina naji daɗi a raina,dan Allah ka taimaki zuciyar data mace a kanka tun kafin tasan waye kai"ta ƙare zancen lokacin da take fashewa da wani irin razanannan kuka mai taɓa zuciya.
Lallai "SO" masifa ne a duk halin da mutum yake ciki baya hana zuciyarsa bayyana abinda yake so da kuma muradin kasan cewa dashi koda ace bazai samu wannan abunda ƙaddara ta haɗa Afnerh da Fahad duk a cikin mafarki wanda a kullum tana tunanin mafarkinta gaskiya ne dalilin hakan ta sauya sunanta daga Afnerh zuwa "Hadnerh" suna mafi soyuwa a gareta.
Lallai marfin Afnerh ya zamantu gaskiya domin gashi ubangiji ya haɗata da mafarkin zuciyarta ko hakan na nufi wani sabon shafin ƙaddarar wani daga cikinsu?.
Ganin ta fita a hankalinta kuma ya gama tabbatar da abinda take faɗa gaskiya wanda tasa ƙwaƙwalwarsa ta tafi wani dugun tunani dasun tunasar dashi wani alƙawari da yay a baya wannan wanne alƙwari ne?wa yaywa shi?wannan sune tambayoyin da suke ƙasan zuciyarsa amma babu amsa.
Cikin sanyin jiki tare da kasala ha saka tattausan hannunsa tare da ɗurawa saman fuskarta a sanyaye ya shiga goge mata hawayen dake zuba cikin idanunta.
Haɓarta ya ɗago tare da zubawa oval face ɗinta idanu kafin ya taɓe baki tare da saurin saki fuskarta,kamar bazai magana ba sai kuma yace.
"فاذكروني اذكر كم واشكرولي ولآ تكفرون.    (آلبقرة ١٥٢)".
"ku ammabace ni zan ambace ku,ku gode mini kada ku butulce min (baƙara aya ta 152).

 JUYAYIWhere stories live. Discover now