The weeding

619 98 32
                                    

*💖JYY💖*

*36-37*

*_NIMCYLUV_*


'''Wattpad@Nimcyluv'''

*_@Telegram_* https://t.me/joinchat/U6Qw0BuhKkqh5GZ8RadieQ


والذاكرين آلله كثيرا والذاكرات أ عدالله الله لهم مغفرة واجرا غظيما. 


             .....Wani yawun takaici ta haɗiya tare da runtsa idanunta ta shiga kukawa da numfashinta daya ɗauke,yay mata abinda ba tayi zatu ba,yayinda wani shashi na zuciyarta ya cika da kunyar abinda yay mata a gaban mutane,lumshe idanunsa yay sosai ƙamshin dake fita a jikinta ta yafi dashi,ƙara ƙasa yay da kansa zuwa wuyanta tare da tura hancinsa wata ajjiyar zuciya ya sauke wacce take nuni da zallan abinda yake ransa da kuma yanayin dake gangar jikinsa,sosai feelings ɗinta ke neman zautar dashi ya tare da dagula masa lissafi,ware idanunsa yay tare da mannasu akan fuskarsa,a sanyaye yaɗan murza waist ɗinta haɗi da juyata suka shiga  fuskantar junansu,yadda ya sanya hancinsa a wuyanta hakan ya ƙara ɓata mata rai zuciyarta ta shiga ta fasa idanunsa ya ƙanƙance kaɗan hakan ya tabbatar ɓacin ranta yaje ƙarshe dan abune mai wahalar gaske kaga idanunta sun sauya,wani huci ta fita mai zafi tare da fincikar numfashinta wanda ya ɗauke sanadiyar murza waist ɗinta da yayi,kasa ɗago kai tayi saima wasu siraran hawaye da suka shiga zuba daga cikin idanunta,yadda hawayen ke fita ta cikin idanunta ya sashi sasauta riƙon da yay mata,hannunsa yasa ya tallafu haɓarta tare da zuba oval face ɗinta idanunsa,bakinsa ya masu daf da kunanta yace"meye na kuka bayan mun kusa cima burinmu?"still bata buɗe idanunta ba haka kuma ta gagara cewa komai sabida wani abu daya tsaya mata a maƙoshi,kalamansa jinsa take tamkar ruwan dalma a zuciyarta.
       "Meye?"
Shine abinda ya ƙara tambayarta a karu na biyu,bakinta ta shiga taunewa haɗi dasa hannu ta toshe bakinta ganin kuka nason ƙwace mata,kai ta shiga girgizawa tare dayin baya,ganin yadda ta ruɗe ta fita hayyacinta yasa yaja baya zuciyarsa a cunkushe ya juya yabar wajansa,wata ƙatuwar ajjiyar zuciya ta sauke tare da dafe ƙirjinta dake ɗagawa,a hankali taja jikinta zuwa wani ɗan luku da babu kuwa durƙushewa tayi a wajan tare fasa kuka mai ciwo,kuka take sosai kukan dake nuna zallar damuwar dake ƙwance a ranta,kuka take mai nuna abinda zuciyarta ke muradi d kuma son kasan cewa dashi,kuka take wanda yake nuna tana cikin kewa da buƙatuwa,ƙara ƙanƙame jikinta tayi tare da cusa kanta tsakanin cinyoyinta ta shiga rera kukanta mai cin rai.

   A can wajan amarya Fannerh sosai abin yay armashi sunsha rawa tare da cashewa,kana aka yanka cake saida komai ya lafa za'a yanka cake ɗin Lili aka shafa a kaga bata wajan,dariya suka saka Yusrah ta buɗe baki tace"ai kawai mucinye shi daman bai isheni ba tana can tabi mijinta daɗi soyayya Allah dai ya bamu masu sunmu"dry Fannerh tayi tare da faɗin Ameen dai ƴar uwa ga wannan sakalyar ta tsaya son masu wani"da sauri Yusrah tace "kai haba kice ƙaddarar soyayya ta faɗa mata,wama take sone?"taɓe baki Fannerh tayi kana taja tsaki tace "Yaya Fahad wai fa,inda yake dajin kai gashi nan ko kallo bai isheta ba,bama ƙya gabansa,aikin banza ayi mutun ko zuciya babu na fahimci wannan farar fatar da sajen ke ruɗarki"wani tari ne ya suɓucewa Yusrah tayi saurin ɗaukan ruwa tasha,numfashi taja tare da faɗin "Don't tell me guy ɗin da nagani a gidanan?"Afnerh wacce tun ɗazu ba tai magana ba sbd ɓacin rai da kuma baƙin cikin maganganun Fannerh,sosai ta zubawa Yusrah idanu tana son gane mood ɗinta amma ta kasa saima cewa da tayi "to Allah ya ƙyauta" tana faɗin hakan taja bakinta tayi shuru tare da lulawa duniyar tunani,murmushi Afnerh tayi tare da faɗin "he's mine tabbas Fahad nawa ne kuma zan tabbatar maku da hakan idanma wata na tunanin sonsa wlh tayi ƙarya" Babu wanda ya kulata bare tayi tunanin zasu tankata,Khalisat dake gefe wacce tun ɗazu take sauraransu tace "abun babu sauƙi mutuniyata gske zansu naga wannan guy ɗin"gira ta ɗaga mata tare da faɗin "zaki ganshi soon,amma zaki zaucewa sbd ƙyansa am telling u"gaba ɗaya suka rankaya zuwa cikin gida.

 JUYAYIWhere stories live. Discover now