DAN ISKAN NAMIJI

By feedynbash

47.8K 1.5K 174

Labarine me taba zuciya yadda maza suke zaluntar matansu da yadda iyaye ke lalata rayuwar yaransu sboda abun... More

page 1-2 & 2-3
5-6&7-8
page 9-10&11-12
page 13-14&15-16
page17-18&19-20
21-22&23-24
25-26
25-26&27-28&29-39
31-40
41-50
50-70
Book 2 part 1
part 2
Part 3
part 4
part 5
part 6
page 7
part 9
part 10
part 11
part 12
part 13
part 14
part 15
part 16
part 17
part 18
part 19
part 20
TALLAH! TALLAH! TALLAH!

part 8

1.3K 44 8
By feedynbash

_*👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*_

               _*NA*_

_*FAREEDA ABDULLAHI*_
     
       _*(Feedyn Bash)*_

_*BOOK  2*_

_*Faceebook Fareeda Abdullahi Ibrahim*_

_*Whattpad @FeedynBash*_

_*Instragtam Feedyn Bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash6660*_

_*E-mail  faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



_*Dedicated to: whattpad fans gaskiya ba abun da zan ce muku sai godiya, yadda kuke mun magana ta WhatsApp da alkhairan ku a gareni, nagode sosai Allah ya bar kauna kuci gaba da suburbudo mun vote*_

                     *35-40*

Kuka ya ke kamar karamin yaro yana jijjiga ta gaba daya, basirar sa ta toshe ganin wankin hula ze kai shi ga dare ya sa ya dakko ruwa a fridge me sanyi ya dinga fesa mata.

Wata ajiyar zuciya ta saka tana sheshshekar kuka da hanzari yai kan ta, yana rungumota yai jikinsa yana ta hawaye yana tausaya mata dan ya saba da maza ba karamar illa yai mata ba.

Yadda kasan an tsagata biyu haka take ji wani azababben radadi ne yake ratsata ta ko ina wani kuka take kamar ranta ze fita.

Ganin haka duk ya rikice ya gigice hankalinsa ya tashi ya rasa inda ze sata ya tarairayota, nan ya din ga jin tashin bugun kofa wanda ake barazanar balla kofar gaba daya ya rikice.

Bai sani ba ya zari rigar baccin ta ya maka ya dauka best ce ya fice, yana bude kofar wazai gani Baby Chakwai ne jina jina da shi ya shigo yana tangadi dan daga gani yana jin jiki.

Wani mugun kallo yake bin Alhaji da shi ya zauna ragwaf Alhaji ma ya zauna wani kallo ya ke bin sa da shi, wanda gaba daya Alhaji ya gama tsarguwa a hankali ya din ga bin jikinsa da kallo.

Wata zabura yai ganin rigar Nauwara a jikinsa ya zubawa Baby Chakwai ido, "kalleni da kyau" yana magana yana cije baki dan ga dukkan alamu ko yaci duka ne ko kuma anyi barin mota da shi.

"Uban me ya hadaka da rigar mace? wa ka kawo gidan nan mace! mace a gidan nan gidan nan!" jikinsa ya kama bari "wallahi um um...." Be barshi yai magana ba ya wanka masa wani gigitaccen mari.

A hankali ya dago ya kalleshi "ni ka mara? ni ka mara? me nai ma haka? baka tsaya kaji uzirina ba" "to meye uzirin naka? munafiki!" ganin haka yai maza ya ce.

"Baby Nauwara ce ba lafiya shi ne dalilin daya sa kaga ganni a rikice" wani mikewa yai cike da bala'i "Nauwara! da ma tana gidan nan? ai a sukwane yai dakin nata.

Ya tarar da ita a kwance tsirara face face da jini be san sanda yai kukan kura ba duk ciwon da ya ke ji ya dena, dan yasan angama komai yai kan ta hankalin sa a matukar tashe, ya wanka mata mari ya fara duk ta kamar Allah ya aiko shi, sannan ya hau kata yana jibga hakan be masa ba ya damko gashin ta ya fara ja.

Tana ihu kamar ranta ze fita ganin haka ta fara kokarin ceton ran ta, ya damko gashin kan ta ya fara jan ta zuwa parlour, abun da yai masifar daga hankalin Alhaji Ghali kenan.

Yayo kan Baby Chakwai ya hankade shi gefe ya fadi ya saki wata kara saboda beyi tsammani ba, "baka da hankali ne? kashe ta za kai ko me matata ce auren ta nai auren sunna, amma saboda bana san bacin ranka nake musguna mata.

Cin amanata ka gama yi da Fesal yanzu haka nasan komai fa" zaro ido Baby Chakwai yai cike da fargaba a tunanin sa an bashi labarin irin jibgar da yaron Fesal yai masa, saboda yazo ya kamasu tare ya nada masa na jaki, shi ne ya huce akan nauwara shi yai masa jina jina shi ma ya huce bakin ciki akan ta, dan karfi ne da Fesal kamar doki.

"Amma ban nuna ma ba na dauke kai saboda haka ka fita daga hanyar matata nagaya ma, zamanka daban zamanta daban, abun naka yayi yawa kai kana gefe kana cin amanata ni ka hanani sakewa.

Kafi kowa sanin cewa ban da abun da zan nema a wajen wata mace kai nake so Baby, meyasa ka dami Nauwara haka ne? nima ina da kishi sosai fiye da tunaninka amma nasan kana cin amanata nake daurewa."

Da hanzari ya je ya sako kayansa ya taho ya sawa Nauwara doguwar riga wadda sam bama ta cikin hayyacinta, a lokacin ya dauke ta Baby Chakwai na gefe yana mamakin wannan abu daya faru kenan asirin da yakewa Alhaji Ghali ya ta shi a banza kenan.

Wani kukan kura kawai yayi yai kan Alhaji Ghali ba inda zaka da ita gwara na ga gawarta da naganta a jikin ka, ganin ze bata masa lokaci ya ture shi ya fice ya bar shi a wajen a kwance yana kururuwa.

Ya nufi asibiti da ita yana zuwa aka karbe su akai Emergency da ita ta daku karshen dakuwa, sannan ta karye a hannu sannan sai an mata dinki saboda ba karamin farkawa yai mata ba.

Hankalin sa ya tashi ganin shiru sai bayan awa biyu likitan ya fito yace ya bishi office, suna shi ga ya ce ya gaya masa gaskiya me ya same ta?" cikin rawar murya yace "fada sukai da kishiyarta."

Doctor ya ce to $sai an hada da yan sanda alhaji, saboda case din babbane wannan dukan ranta ta ke nema muraran, so take kawai ta ke ta kashe ta dan wannan dukan bana hankali bane."

Abun ya daga hankalinsa sosai da kyar ya shawo kan likitan ya amince aka bar maganar, ya zube masa makudan kudi ya koma gida dan gaba daya hankalinsa yayi kan Baby Chakwai, sam bashi da nutsuwa a tattare da shi bai san me Baby zai masa ba shi ma dole tasa yai abun da yai.


*******************

Lawan ya doku ya saki wata kara saboda yadda gadon bayansa ya amsa, da kyar ya ce "lafiya? me nai muku kuma?" "zakaci ubanka yau kanwar mu kake bi kanwarmu kake nema haka."

Da sauri Lawan ya ce "baki da mutunci Baby dama yayyen ki kika kawon bansani ba" yana kokarin motsawa "wallahi bansan....." bata karasa ba dayan ya fara wanka mata mari suka dinga dukan Lawan tun yana ihu sai da yai shiru.

Ita ko data yunkura za tai magana sai mari sai da suka tara musu gajiya fuskar Baby tai sundum jini ya kwanta musamman idon ta, shi ko da kyar ya ke motsi jikinsa duk sun masa jina jina sun farfasa masa kai, suka gama suka tattare kudin jikin sa da nata suka kara gaba.

Lawan ya mike yana tangadi ya zura kayansa Baby ta ce "my Love" ya juya ya kara wanka mata mari ya din ga dukan ta, "muguwa azzaluma kin sa an kusa kashe ni zaki mun magana dadin abun kema kin ci ubanki ai jaka ki jira hukuncina kuma."

Ya saka kaya yai gaba ya barta kuma "kar ki sake na dawo na sameki anan wallahi" ya fice yana dingisa kafarsa yaja motarsa yama rasa ina ze nufa, sai sannan yaji bakin cikin rabuwa da Laila dan yasan ita kadai ce zata iya juriya akan wannan lamarin, ita ce karkatacciyar kuka me dadin hawa suna san juna shi da Laila dole ya dawo da ita.

Ganin ba wata mafita yasan halin Ummi sarai bare ya daketa ya baro gidan bazata saurare shi ba, gidan Saudat yaja motarsa ga nufa da kyar yake tukin saboda yadda aka tara masa gajiya.

Gidan Saudat ya nufa tana parlour a zaune ta sheka kwalliya shigowar ta kenan sun gaya mata sun gama aiki, ta sallamesu ta ce zata kara nemasu in dai be gyara halinsa ba.

A hankali yai parking ya shi ga gidan da kyar yake takawa ya shi ga tana parlour tana waya tana kyalkyala dariya, ya shi go ya fadi a kan carpet yaraf "dubani Saudat! dubani ban da lafiya, yimun treatment please."

Da hanzari ta tashi tana kallon yadda sukai masa da fuska duk sun kumbura, shi kansa yai wani gingimeme musamman goshin sa da keyarsa, wata dariya ta subuce mata ta din ga yi har da tsugunawa tana rike ciki.

Yanzu kai Lawan meya sameka haka? Barin mota kai ko Yan fashi ne suka tareka koko duka aka nadama? Ta kuma shekewa da dariya gaba daya ya gama kuluwa ji yake kamar ya shaketa.

Ita ko dariya ta ke tana kallonsa ganin da gaske take yai mata banza yaci gaba murkususu, dan kanta ta gaji da dariyar ta ce masa "yanzu Lawan me kake so nai ma? na tambaye ka kaki ka gayan kasan Doctor ce ni?

A yanayin jikin nan naka be kamata na taba ka ba sai da police, amma kaga kai mijinane dole nasan treatment din da zan baka dole kai min bayani." wata harara ya buga mata yaja tsaki "mtswww!

Sabani muka samu da wasu amma fa na ragargajesu, dan ko gane kamannin su ba'ai." Habawa ta kara fashewa da wata hadaddiyar dariya "Allah mutumina? kuri Master kai dai kace mun kwanjin ka a wajen mata ya kare kawai ba karfi wajen maza."

"Ya isheki Saudat idan bazaki mun ba na mike nai gaba" "a'a meyai zafi angona dole na duba ka ai" da sauri ta dakko first aid box ta fara treatment din sa da mugun, ta din ga tsilala masa hydrogen dasu spirit ihu yake kamar ransa ze fita, duk sai da ta dirje saboda azaba lawan har da fitsari.

Nan ya kwanta yana mai da numfashi ya gama hada gumi yai sharkaf hankalinsa ya tashi, ya tabbatar Saudat ba ta da imani ya kawo kansa mahallaka, be gama tunani ba ya ganta da tafasashshen ruwan zafi a roba ta dumfaro shi.

"Ke! ke! ke! dakata, mezaki da ruwa?" ta dalla masa harara "zan yiwa in da ya kumbura gashi ne, ga kafar ka ta kumbura da wannan goshin."

Ta ajiye ta danne shi ta hau kansa ta zauna, magana yake mata tai masa banza duk yadda yaso ture ta ya kasa ta danne shi sosai, ta dakko towel ta tsoma da ruwan yana yarari ta danna masa a kafar, wata karar azaba ya saki ragowar fitsarin da ya gagara fitowa ya zubo gaba daya.

Lawan wani hawayen azaba ya ke ashe dama haka take azzaluma ce, besan san da ya saki kara ba saboda yadda ta nana masa akan ciwon sa na kansa, ji yai kwakwalwar sa na neman dena aiki.

Sai da ta gama yi masa azaba ta tafi ta bar shi dan tasan jikin sa yai likwiy baze  iya komai ba, sai da ya huta ya mike ya sanja kaya ya fita daga gidan ya nufi gidan Ummi dan shi ka dai yasan hukuncin da zewa Saudat.

Wata dariya ta sheke da ita "muzuba mugani Dan iskan namiji, ka hadu da fitinanniyar mace, idan jumurin ka isakanci da wulakanta mata wallahi sai na baka lesson a rayuwar mu, kuma auren mu igiya dubu ba tsinkewa ba yaji bare saki, zama daram Saudat da Lawan hhhhhhhhhhh!."

To fa fans maji magani wannan zama na Lawan da Doctor Saudat ko ze dore? kuyi hakuri kuci gaba da bibiyata dan jin yadda zata kaya, ni ce taku a kullum a koda yaushe.

             *Feedyn Bash Cele*


*Pls*
*Share*
*Comment*
*Vote*

Continue Reading

You'll Also Like

21.5K 448 42
What If Chloe lukasiak has a twin sister who is the favorite?
62.8K 1.8K 178
"In a world of pirates and adventure, meet Ryo, a half mink-half human with a tragic past. After losing his parents, Ryo was taken in and trained by...
509K 15.1K 38
MALE WEDNESDAY X READER "I love you...Wednesday Addams" The girl cried while hugging him as tight as she could. "I love you too....Amore mio. Please...
550K 18.7K 80
Child of the Eldest Gods from the East, Heiress of Earth and Legacy of Stars and Magic, Has the Affinity to Balance the Peace of Nature, Fated Love i...